APC ta sha kasa: INEC ta sanar da sakamakon zaben ciyaman da aka gudanar a Abuja

APC ta sha kasa: INEC ta sanar da sakamakon zaben ciyaman da aka gudanar a Abuja

  • Mohammed Kasim na jam'iyyar PDP ya lashe zaben ciyaman na karamar hukumar Gwagwalada da kuri'u 22,165
  • Hukumar INEC ta bayyana cewa dan takarar na PDP ya doke abokin hamayyarsa na APC wanda ya samu kuri'u 17,700
  • Wannan nasara ta PDP ta zo ne duk da yadda aka rahoto ministan Abuja, Nyesom Wike ya na yi wa APC yakin neman zabe

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Hukumar INEC ta ayyana ɗan takarar PDP, Mohammed Kasim, a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙaramar hukumar Gwagwalada da aka gudanar a ranar Asabar.

Kasim ya samu ƙuri'u 22,165, inda ya doke babban abokin hamayyarsa na jam'iyyar APC, Yahaya Shehu, wanda ya samu ƙuri'u 17,788.

INEC ta ayyana dan takarar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben Gwagwalada, Abuja.
Malaman zabe na kirga kuri'u, da Mohammed Kasim, dan takarar PDP da ya lashe zabe a Abuja. Hoto: Getty Images, Jagaban Matasan Abuja/Facebook
Source: Getty Images

PDP ta lashe zaben ciyaman a Abuja

Babban jami'in tattara sakamakon zaɓen, Philip Akpen, ya bayyana cewa an gudanar da zaɓen cikin lumana a dukkanin yankunan ƙaramar hukumar, in ji rahoton Premium Times.

Kara karanta wannan

An yi babban rashi: Mataimakin kwamishinan 'yan sanda a Najeriya ya rasu

Nasarar Kasim ta zo ne a daidai lokacin da jam'iyyar PDP ke fuskantar matsin lamba sakamakon ficewar jiga-jiganta kamar Atiku Abubakar wanda ya koma jam'iyyar ADC.

Wannan nasara ta nuna cewa har yanzu jam'iyyar tana da tasiri a matakin ƙarkara duk da rarrabuwar kai da ake samu a babban ofishinta na ƙasa.

A zaben ciyaman na Gwagwalada, jam'iyyar PDP ta samu ƙuri'u 22,165, yayin da jam'iyyar APC ta samu 17,788, sannan jam'iyyar APGA ta zo ta uku da ƙuri'u 1,687.

Gwagwalada yanki ne da ke nuna haɗakar ƙabilu da addinai daban-daban na Najeriya, wanda hakan ya sa wannan nasara ta kasance mai matuƙar mahimmanci ga PDP.

Manufofin Kasim, sabon ciyaman a Abuja

Kididdiga ta nuna cewa mutane 207,577 ne suka yi rajista a Gwagwalada, amma mutane 46,294 ne kacal aka tantance domin jefa ƙuri'a a ranar zaɓen na ranar Asabar.

Sakamakon ya nuna cewa an sami jimillar ƙuri'u 43,960 masu inganci, yayin da aka yi watsi da ƙuri'u 1,521 waɗanda ba su da amfani a zaɓen.

A lokacin yaƙin neman zaɓensa, Mohammed Kasim ya mayar da hankali ne kan inganta jin daɗin al'umma, ƙarfafa mata, samar da ingantaccen ilimi da kuma kiwon lafiya.

Kara karanta wannan

Hukumar INEC ta sanar da sakamakon zaben 'dan Majalisa da aka gudanar yau Asabar

Mazauna yankin suna sa ran cewa zai cika waɗannan alƙawura domin kawo ci gaban da ake buƙata a fadin ƙaramar hukumar ta Gwagwalada baki ɗaya.

PDP ta samu nasara a karamar hukumar Gwagwalada duk da rikicin shugabanci da take fama da shi.
Jami'an hukumar INEC suna kidaya kuri'un da aka kada a zaben Najeriya. Hoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Ana jiran sakamakon zabukan Abuja

Wannan nasara na iya zama babban kwarin gwiwa ga sauran ƴan takarar jam'iyyar PDP a zaɓuka masu zuwa yayin da suke ƙoƙarin sake dawo da martabar jam'iyyar.

Hukumar INEC ta gudanar da zaɓen ne a ƙananan hukumomi shida na birnin tarayya Abuja waɗanda suka haɗa da AMAC, Abaji, Kwali, Kuje da kuma Bwari yanzu.

Ana ci gaba da jiran sanar da sauran sakamakon zaɓukan ƙananan hukumomin birnin tarayya Abuja domin sanin jam'iyyar da za ta fi yawan shugabannin ƙananan hukumomi.

Imran Muhammad ya wallafa bidiyon lokacin da baturen zabe ka karanta sakamakon a shafinsa na X. Kalli bidiyon a kasa:

APC ta lashe zaben dan majalisa

A wani labari, mun ruwaito cewa, hukumar INEC ta kammala tattara sakamakon zaben cike gurbin da aka gudanar a mazabar Ahoada ta Gabas a jihar Ribas.

'Dan takarar APC, Ukalikpe Napoleon shi ne ya samu nasara da kuri'u 3,980, inda ya lallasa abokan hamayyarsa a zaben da aka gudanar ranar Asabar.

Jami'ar INEC, Farfesa Rosemary Ogbo, ce ta sanar da sakamakon tare da tabbatar da cewa an gudanar da zaɓen cikin tsari, adalci da gaskiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com