Zaben Cike Gurbi: Abin da Gwamna Abba Kabir Ya Fada wa Ƴan Jam'iyyar APC

Zaben Cike Gurbi: Abin da Gwamna Abba Kabir Ya Fada wa Ƴan Jam'iyyar APC

  • Gwamnan Kano, Abba Yusuf, ya yi magana bayan gudanar da zaben cike gurbi da aka yi a wasu yankunan jihar
  • Gwamna Abba ya yaba wa hukumar zaben jihar da jami’an tsaro kan gudanar da zaben cike gurbi cikin kwanciyar hankali
  • Ya ce an gudanar da zaben cikin tsari da lumana a mazabun cikin birnin Kano da Ungogo, lamarin da ya nuna balagar siyasa da hadin kan jama’a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Gwamnan Kano, Abba Yusuf, ya bayyana farin ciki bayan kammala zaben cike gurbi a jihar da aka yi.

Abba Kabir ya yaba wa hukumar zabe mai zaman kanta a jihar da kuma hukumomin tsaro bisa yadda suka gudanar da shi cikin lumana da tsari.

Abba Kabir ya yaba wa hukumar zabe da jami'an tsaro
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano. Hoto: Abba Kabir Yusuf.
Source: Facebook

Hakan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sunusi Dawakin-Tofa, ya fitar a shafin Facebook a yau Asabar 21 ga watan Fabrairun 2026.

Kara karanta wannan

Yadda zabe ke gudana a Kano da wasu sassan Najeriya a yau Asabar

Abba Kabir ya yaba yadda aka yi zabe

Gwamnan ya bayyana zaben a matsayin wani babban mataki a tafiyar dimokuradiyyar Kano da yake ganin zai kara kawo ci gaba a jihar.

Yusuf ya ce kwanciyar hankalin da aka samu a rumfunan zabe ya nuna yadda al’umma suka kara fahimtar siyasa da kuma ingancin shirye-shiryen tsaro da aka tanada a zaben.

Ya yabawa mazauna mazabun cikin birnin Kano da Ungogo da aka gudanar da zaben, bisa nuna ladabi, hadin kai da jajircewa wajen kada kuri’a cikin lumana.

Haka kuma, gwamnan ya yabawa jam’iyyun siyasa da sauran masu ruwa da tsaki, musamman ‘yan APC kan bin dokokin zabe da kaucewa duk wani abu da zai tayar da hankali.

Ya ce:

“A karon farko cikin tarihi na baya-bayan nan, mun ga zabe ba tare da rikici, amfani da makamai ko magudi ba a Kano.”

Ya kara da cewa wannan cigaba ya dace da manufar gwamnatinsa ta “Kano ita farko”, yana mai cewa zamanin kashe-kashe da hana mutane hakkinsu na zabe ya kare.

Kara karanta wannan

Sheikh Pantami ya fadi dalilin shiga siyasa da neman gwamna a Gombe

Abba ya ji dadin yadda aka gudanar da zabe a Kano
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir yayin taro a gidan gwamnati. Hoto: Abba Kabir Yusuf.
Source: Facebook

Cike gurbi: Farin ciki da Abba ya yi

Gwamnan ya yi farin ciki inda ya ce yadda aka gudanar da zaben ya nuna Kano a shirye take da siyasar da ta dogara da tattaunawa, hakuri da mutunta ka’idojin dimokuradiyya.

Ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da aiki tare da dukkan masu ruwa da tsaki domin tabbatar da cewa zabuka masu zuwa sun kasance sahihai kuma babu tashin hankali.

A karshe, ya bai wa mazauna jihar tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da bai wa tsaron rayuka da dukiyoyi fifiko, ba tare da la’akari da bambancin siyasa ko addini ba.

Jama'a sun kauracewa zabe a Kano

A wani labarin, an samu karancin fitowar masu kada kuri'a a zaben cike gurbin 'yan majalisar dokokin Kano guda biyu a yau Asabar 21 ga Fubrairu 2026.

Kwamishinan zabe na Kano (REC), Abdu Zango ya danganta matsalar da lokacin azumin Ramadan da kuma karancin 'yan takara a zaben.

Ya kuma bayyana cewa duk da mutane ba su fito ba, amma zaben ya gudana cikin lumana da kwanciyar hankali a Ungogo da birnin Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.