Rikicin APC: Majalisa Ta Fara Yunkurin Tsige Mataimakin Gwamna? Aiyedatiwa Ya Yi Bayani

Rikicin APC: Majalisa Ta Fara Yunkurin Tsige Mataimakin Gwamna? Aiyedatiwa Ya Yi Bayani

  • Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya musanta rade-radin da ake yadawa cewa ya fara yunkurin tsige mataimakinsa, Olayide Adelami
  • Hakan na zuwa ne bayan hasashen da wani malamin coci ya yi cewa ya gano cewa mataimakin gwamnan zai bar mukaminsa
  • Aiyedatiwa ya bayyana cewa wannan hasashe karya ce mara tushe, ana yada shi ne domin tayar da hankali da bata amincin tsakaninsu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ondo, Nigeria - Gwamnan Jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ya yi watsi da jita-jitar da ke cewa ana shirin tsige mataimakinsa, Olayide Adelami, yana mai bayyana labarin a matsayin ƙarya marar tushe.

A ’yan kwanakin nan, ana ta raɗe-raɗin cewa akwai sabani tsakanin gwamnan da mataimakinsa, tare da zargin cewa ana shirin tsige shi a Majalisar Dokokin Jihar.

Gwamnan Ondo.
Gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa a wurin taro Hoto: Hon. Lucky Aiyedatiwa
Source: Facebook

Rikicin siyasa da ke faruwa a Ondo

Kara karanta wannan

Ramadan: Gwamna ya amince da ciyar da talakawa, ya yi wa malaman addini tagomashi

The Nation ta ce wasu rahotanni sun danganta wannan zargi da rikicin ya barke a cikin ƙungiyoyin siyasa a garin Owo, inda mataimakin gwamnan ya fito.

Haka nan kuma ana zargin mataimakin gwamnan Ondo na takun saka da Kwamishinar Kuɗi ta jihar, Misis Isaacs Omowunmi, wadda ake cewa tana da kusanci da Gwamna Aiyedatiwa.

Sai dai da yake jawabi a wajen kaddamar da sabon titin Ayegunle–Iwaro Oka a karamar hukumar Akoko Kudu maso yamma, Aiyedatiwa ya ce babu wata matsala tsakaninsa da mataimakinsa.

Ana shirin tsige Mataimakin gwamnan Ondo?

Ya kuma bayyana cewa rade-radin tsige mataimakin gwamnan da ake yadawa na cikin tunanin masu son tada hankali, wadanda ke neman riguza amincin da ke tsakaninsu.

Gwamna Aiyedatiwa ya bayyana cewa ya ga bidiyon da wani malami, Olumuyiwa Akogun, ya fitar inda ya ce an yi masa “wahayi” cewa za a tsige mataimakin gwamnan nan ba da jimawa ba.

Malamin, wanda shi ne jagoran cocin God Central Ministry a Jihar Ekiti, ya yi ikirarin cewa ya ga labarin da ke nuna an tsige mataimakin gwamnan.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fusata kan kashe kashe a taron APC, ya dauki kwakkwaran mataki

Gwamna Aiyedatiwa ya karyata wahayin malami

Aiyedatiwa ya ce bidiyon wani ƙoƙari ne na kawar da hankalin gwamnatinsa daga aikinta. Ya jaddada cewa Adelami mataimaki ne mai aminci kuma babu wani shiri ko niyyar cire shi daga mukaminsa.

“Wasu na yaɗa bidiyon ƙarya suna cewa za a tsige mataimakin gwamna. Daga ina? Ina za su tsige shi? Kada ku kula da su; suna neman suna ne kawai. Wannan ba zai faru ba,” in ji gwamnan.
Jam'iyyar APC
Tutar jam'iyyar APC mai mulki a jihar Ondo Hoto: @OfficialAPCNig
Source: Twitter

A cikin bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta, malamin ya ce ya ga gwamna da mataimakinsa tsaye tare da tutar ƙasa kafin wata “guguwa” ta taso ta raba su, yana mai cewa hakan na nuni da rikici mai tsanani da ka iya ɓarkewa.

Sai dai gwamnan ya jaddada cewa shi da mataimakinsa suna aiki tare cikin haɗin kai domin ci gaban al’ummar jihar, kuma babu wata barazana, kamar yadda Punch ta kawo.

Gwamna Aiyedatiwa ya yi maganar rikicin APC

Kara karanta wannan

Tinubu ya ba Aminu Ado Bayero jagorancin ciyar da talakawa a Ramadan

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Lucky Aiyedatiwa, ya umarci jami’an tsaro su binciki rikicin da ya faru a taron jam'iyyar APC na mazabu da aka yi a jihar Ondo.

Aiyedatiwa ya bukaci hukumomin tsaro su gano tare da gurfanar da wadanda ke da alhakin rikicin da ya tarwatsa taron mazabu na jam’iyyar APC.

Ana zargin wasu matasa ‘yan daba masu alaka da ‘yan kungiyar NDLEA a jihar Ondo ne suka kawo cikas ga taron wanda ya jawo asarar rayuka da dama.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262