Bayan Ziyartar El Rufai, Atiku Ya Tona Shirin da APC Ke Yi kan Jam'iyyar ADC
- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya kai ziyara ga Nasir El-Rufai bayan an yi yunkurin cafke shi a filin jirgin sama
- Atiku Abubakar ya bayyana cewa akwai wani shiri da jam'iyyar APC ke yi na ganin ta raunana ADC kamar yadda ta ruguza PDP
- Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi kira da babbar murya ga 'yan adawa kan su tashi tsaye don ka da su bari hakar APC ta cimma ruwa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon Mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya yi zarge-zarge kan jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.
Atiku Abubakar ya yi zargin cewa jam’iyya mai mulki ta APC tana kulla shirin yin amfani da bangaren shari’a domin raunana jam’iyyar ADC.

Source: Facebook
Atiku ya bayyana hakan ne cikin wani bidiyo da ya sanya a shafinsa na X a ranar Juma'a, 12 ga watan Fabrairun 2026 yayin wata ziyara da ya kai gidan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.
Atiku ya samu bayanin kulli kan APC
A cikin jawabin nasa, Atiku ya ce ya samu “ingantaccen bayani” game da kullalliyar da jam’iyyar APC ke yi.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bukaci kusoshin jam’iyyun adawa da su kasance cikin shiri domin dakile wannan shiri.
“Kamar yadda suka raunana kuma suka dakile jam’iyyar PDP, akwai kuma kokari da tsare-tsare na raunana ADC ta hanyar sake amfani da bangaren shari’a."
“Dole ne mu kasance cikin shiri, kuma mu tashi tsaye wajen adawa da wannan shiri na raunana ’yan hamayya."
“Wannan bayani ne mai matukar inganci. Don haka ya kamata dukkanmu mu kasance cikin shiri tare da tabbatar da cewa ba a yi amfani da bangaren shari’a wajen raunana ADC ba."
“Kamar yadda aka yi amfani da shi wajen raunana da kuma ruguza PDP. Dole ne dukkanmu mu hada kai mu tashi tsaye wajen yaki da wadannan dakarun da ke adawa da dimokuradiyya. Ina gode muku kwarai da gaske.”
- Atiku Abubakar
El-Rufai: Atiku ya yi tir da mahukuntan Najeriya
Haka kuma, Atiku ya yi Allah-wadai da abin da ya bayyana a matsayin kokarin kunyata El-Rufai.
“Ta hanyar kunyata ka, suna cin zarafin daukacin ’yan siyasa ne. Muna yin Allah-wadai da shi baki daya kuma za mu tsaya tare da kai."
- Atiku Abubakar

Source: Twitter
El-Rufai ya yi godiya ga Atiku
A nasa martanin, El-Rufai ya gode wa tsohon Mataimakin shugaban kasar kan ziyarar da ya kai masa da kuma goyon bayan da ya ba shi.
“Kullum kana nuna damuwa kan walwala ta da ta abokanmu da sauran mutanen da muke tare."
“Wannan ziyara ta kara karfafa damuwar da ka dade kana nunawa, wadda zan ci gaba da gode maka har abada.”
- Nasir El-Rufai
Atiku ya soki yunkurin cafke El-Rufai
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon Mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya soki yunkurin jami'an tsaro na cafke Nasir El-Rufai.
Atiku ya nuna rashin jin daɗinsa kan yunƙurin da jami’an EFCC suka yi na kama El-Rufai ba tare da mutunta ƙa’idojin doka ba.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ba a kafa EFCC domin ta zama makamin siyasa na shugaban ƙasa ko jam’iyya mai mulki ba.
Asali: Legit.ng


