Fayose Ya Fallasa Yadda Zaman Atiku da Makinde Ya Kaya a Gidan Janar IBB
- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi wani zama tare da gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, a gidan Janar Ibrahim Badamasi Babangida (mai ritaya)
- Atiku Abubakar ya bayyana zuwan da ya gidan tsohon shugaban kasar a matsayin neman shawara ta yau da kullum
- Sai dai, tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya fito ya bayyana abubuwan da aka tattauna a yayin zaman
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Ekiti - Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya yi magana kan taron da aka gudanar tsakanin Atiku Abubakar, Gwamna Seyi Makinde da Janar Ibrahim Badamasi Babangida.
Ayodele Fayose ya bayyana cewa an yi taron ne don kulla yarjejeniyar siyasa tsakanin Atiku Abubakar da Gwamna Seyi Makinde kan zaben shekarar 2027.

Source: Twitter
Tsohon gwamnan na jihar Ekiti ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X a ranar Laraba, 11 ga watan Fabrairun 2026.
Atiku, Makinde sun gana a gidan IBB
Atiku da Makinde dai sun gudanar da taro ranar Talata a gidan tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, da ke Minna.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya fara ganawa da Janar Babangida (mai ritaya), sannan daga baya Gwamna Makinde ya shiga taron.
Sai dai, tsohon mataimakin shugaban kasar ya shaida wa manema labarai daga baya cewa ziyarar neman shawara ce ta yau da kullum ya kai wa tsohon shugaban kasar.
Me Fayode ya ce kan ganawar?
Amma, a martanin da ya yi, Ayodele Fayose ya zayyana abin da ya kira sakamakon taron sirrin, ko da yake bai bayyana inda ya samu bayanansa ba.
Fayose ya yi ikirarin cewa an riga an cire tsohon gwamnan jihar Anambra kuma jigo a jam’iyyar ADC, Peter Obi, daga cikin lissafin tikitin shugaban kasa na jam’iyyar, shi ya sa aka zabi Makinde ya marawa Atiku baya.
“Ba sabon labari ba ne cewa Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya tafi Minna, jihar Neja, jiya domin tattaunawa da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar.”
"An zabi wurin taron da mutanen da suka halarta ne cikin tsanaki domin tabbatar da amincewa da sirrin taron."
"An yi la’akari da cewa Peter Obi ba zai yarda ya zama mataimakin Atiku ba, sannan Arewa ba za ta amince da shi a matsayin wanda zai gaji Atiku ba."
"Sannan, Atiku yana da tabbacin kaso 70 na samun tikitin ADC, bayan ya tabbatar da cewa ba a ware shiyyar da za ta fito da dan takarar shugaban kasa ba a jam’iyyar."
"Makinde ya amince zai koma ADC ne a kan sharadin za a ba shi tikitin mataimakin shugaban kasa a matsayin abokin takarar Atiku. Ana sa ran za a gabatar da wannan ga makarraban Atiku na kusa domin tattaunawa da tabbatarwa."
"Makinde ya yi alkawarin samar da kudi har naira biliyan 10 (wadanda za a bayar gida biyu), a matsayin gudunmawarsa ta farko ga abin da ya kira ‘kaddamar da ADC yadda ya kamata,’ sannan zai samar da karin kudade idan yakin neman zabe ya kankama."
"Gwamnan ya kuma ba da tabbacin cewa a zaben fidda gwani na ADC, zai tabbatar da dukkan wakilai daga Kudu-maso-Yamma, sannan zai yi amfani da tasirin matarsa, wacce ’yar jihar Rivers ce, wajen samun kuri’un wakilai a shiyyar Kudu-maso-Kudu."
"Ya bayyana cewa idan aka yi amfani da shi wajen raba kuri’un Kudu-maso-Yamma a babban zabe, hakan zai ba ADC damar da take bukata na yin nasara.”
- Ayodele Fayose

Source: Facebook
Fayose ya kara da cewa an sanya ranar gudanar da wani taron na gaba a Dubai, kasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), nan da makonni biyu masu zuwa.
Dan majalisa ya ba Atiku shawara
A wani labarin kuma, kun ji cewa dan majalisar wakilai daga jihar Adamawa, Hon. Mohammed Basil, ya ba Atiku Abubakar shawara kan siyasa.
Hon. Muhammad Basil ya yi kira ga Atiku Abubakar, da ya janye daga siyasa tare da ɗaukar matsayi na dattijo mai ba da shawara a kasa.
'Dan majalisar ya ce lokaci ya yi da Atiku zai ja gefe domin bai wa matasa ’yan siyasa dama su jagoranci al’amura.
Asali: Legit.ng


