Ana Batun Tsige Shi, Kwankwasiyya Ta Tura Sako ga Mataimakin Gwamnan Kano

Ana Batun Tsige Shi, Kwankwasiyya Ta Tura Sako ga Mataimakin Gwamnan Kano

  • Kwankwasiyya ta jinjinawa mataimakin gwamnan Kano, Aminu Gwarzo bisa yadda ya tsaya kan akidar tafiyar duk da matsin lambar da yake fuskanta
  • Ta kuma yabawa mambobinta masu amana, wadanda suka ajiye aikinsu daga gwamnatin Kano bayan Gwamna Abba ya koma APC
  • Tafiyar Kwankwasiyya ta tabbatar wa al'umma cewa babu wani matsin lamba da zai karkatar da ita daga manufofinta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Kwankwasiyya ta yaba wa Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Aminu Abdulsalam Gwarzo, bisa yadda ya nuna amana duk da matsin lambar da yake fuskanta.

Haka zalika, Kwankwasiyya ta jinjinawa sauran zababbun jami'ai da suka tsaya tsayin daga tare da jaddada mubaya'arsu ga jagoran NNPP na kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Kwankwaso da Gwarzo.
Jagoran NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso da mataimakin gwamnan Kano, Aminu Gwarzo Hoto: @KwankwasoRM
Source: Twitter

Daily Trust ta tattaro cewa hakan na zuwa ne bayan murabus ɗin da wasu masu muƙaman siyasa suka yi daga Gwamnatin Jihar Kano domin nuna goyon baya ga Kwankwaso.

Kara karanta wannan

Magoya bayan Kwankwaso sun gano abokin takarar da ya dace da shi a 2027

Sun dauki wannan mataki ke bayan Gwamna Abba Iabur Yusuf ya sauya sheka daga NNPP zuwa jam'iyyar APC mai mulki.

Sakon Kwankwasiyya ga Aminu Gwarzo

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Kwankwasiyya Dr. Habibu Sale Mohammed, ya fitar ranar Lahadi, ya bayyana cewa mataimakin gwamnan Kano ya nuna jarumta.

"Kwankwasiyya tana jinjina wa jarumta da tsayin daka na mataimakin ' gwamna, da zaɓaɓɓun wakilanmu da suka haɗa da Sanata, 'yan Majalisar Wakilai da na Jiha, da kansiloli waɗanda suka tsaya kan amanar da jama'a suka ba su,” in ji sanarwar.

Habibu Sale ya ce mataimakin gwamnan da sauran jami’ai sun ƙi karɓar “tayin abubuwa da dama da kuma matsin lamba” daga hukumomin jiha da na tarayya.

An yabi kwamishinonin da suka yi murabus

Sanarwar ta kuma jinjina wa tsofaffin kwamishinoni, masu ba da shawara na musamman (SAs), darektoci, da shugabannin hukumomin gwamnati waɗanda suka yi murabus domin nuna goyon baya ga Kwankwaso.

Kwankwasiyya ta bayyana matakin da suka dauka a matsayin sadaukarwa domin kishin akida maimakon son kai.

Kara karanta wannan

Kano ta kara daukar zafi, an kalubalanci Kwankwaso kan wasu kwangilolin gwamnatin Abba

Ƙungiyar ta bayyana cewa:

"Tun farko Sanata Kwankwaso ya roƙi waɗanda suka yi murabus ɗin da su sake tunani su zauna a muƙamansu domin cigaban mulki, amma suka ƙi.
"Wadanda suka yi murabus ɗin sun nace cewa akidarsu ba ta dace da sabon tsarin da suka bayyana a matsayin 'jagorancin Gandujiyya' a Jihar Kano ba.
Yan Kwankwasiyya.
Taron yan Kwankwasiyya karkashin jagorancin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: @SaifullahiHON
Source: Facebook

Muna nan kan akidarmu - Kwankwasiyya

A ƙarshe, tafiyar ta Kwankwasiyya ta jaddada cewa ba a gina ta a kan neman mulki ko alfarma ba, sai dai a kan sadaukarwa, hidima ga jama'a, da kuma fafutukar tabbatar da adalci.

Ta tabbatar wa magoya bayanta cewa tana nan daram, kuma babu wani matsin lamba da zai karkatar da ita daga manufofinta, kamar yadda Punch ta kawo.

Wani dan Kwankwasiyya a Kano, Sanusi Isiyaku ya bayyana wa Legit Hausa cewa za su nuna wa Gandujiyya karfin da Kwankwaso yake da shi.

Ya nuna mamaki karara kan yadda Gwamna Abba ya bar tafiyar gidan siyasar Kwankwaso, yana mai cewa ko a mafarki bai taba tunanin haka za ta faru ba.

Kara karanta wannan

Rikicin NNPP: An sake kunno wa Kwankwaso wuta bayan Gwamna Abba ya koma APC

"Duk dan Kwankwasiyya mai amana ba zai bar gidan Kwankwaso ba, duk da na yi mamakin tafiyar Abbba Gida-Gida, amma mun shirya bin zabin madugu a jihar Kano.
"Ina son Abba maganar gaskiya saboda mutumin kirki ne, amma kuma zan fifita matsayar Kwankwaso idan Allah ya kaimu zaben 2027," in ji shi.

Majalisa na shirin tsige Aminu Gwarzo?

A wani rahoton, kun ji cewa majalisar dokokin jihar Kano ta musanta rahotanni da ake yadawa cewa tana yunkurin tsige mataimakin gwamna, Aminu Abdussalam Gwarzo.

Ta kuma yi ikirarin cewa an kirkiri wadannan rahotannin na karya ne kawai domin haddasa takaddama ta siyasa da ba ta da amfani a jihar Kano.

Majalisar ta bayyana cewa babu wani kudiri ko yunkuri a gaban mambobin majalisar Kano da nufin tsige mataimakin gwamnan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262