Ana Wata ga Wata: 'Yan Bangar Siyasa Sun Farmaki Sakatariyar Jam'iyyar ADC

Ana Wata ga Wata: 'Yan Bangar Siyasa Sun Farmaki Sakatariyar Jam'iyyar ADC

  • 'Yan bangar siyasa sun farmaki ofisoshin jam’iyyar ADC a Benin inda suka fasa tagogi tare da kokarin kona ginin da man fetur a yau Alhamis
  • Shugaban jam’iyyar Kennedy Odion ya zargi abokan hamayya da kokarin tsoratar da su domin su fice daga takarar zaben shekarar 2027
  • Rundunar yan sanda ta tura karin jami’an tsaro zuwa titin Ogbelaka bayan rahoton barnar da aka yi wa tutocin jam’iyyar da wasu kayayyaki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Edo - Wasu fusatattun matasa da ake zargin ƴan bangar siyasa ne sun kai hari sakatariyar jam’iyyar ADC dake kan titin Ogbelaka a birnin Benin, jihar Edo.

Maharan sun fasa tagogin ginin tare da lalata wasu kayayyaki, inda suka yi ƙoƙarin ƙona ofishin kurmus kafin mazauna yankin su kawo ɗauki su fatattake su.

Kara karanta wannan

Yadda Sheikh Pantami ya ki amsa wa Tinubu da aka yi masa tayin mukaman gwamnati

'Yan bangar siyasa sun farmaki sakatariyar ADC a jihar Edo.
Sakatariyar jam'iyyar ADC a jihar Edo da 'yan bangar siyasa suka farmaka. Hoto: @EdoPoliceNG
Source: Twitter

An yi yunkurin kona sakatariyar ADC

Wani faifan bidiyo dake yawo a yanar gizo ya nuna yadda aka farmaki ginin, da kokarin kona shi, da kuma jawabin wani da abin ya faru a kan idonsa, a cewar rahoton Daily Trust.

Shugaban jam'iyyar ADC na Jihar Edo, Kennedy Odion, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa maharan sun zo ne da nufin ruguza ofishin baki ɗaya.

A cewarsa, ƴan bangar siyasar sun farmaki ofishin dauke da jarkokin man fetur, amma jajircewar magoya bayan jam'iyyar dake yankin ne ya hana su cin nasarar ƙona ginin.

Odion ya zargi wasu ƴan siyasa da hannu a harin, yana mai cewa:

“Wasu ƴan siyasa suna son ADC ta bar jihar domin kada wata jam’iyyar hamayya ta fafata da su a zaɓen 2027.”

'Yan sanda sun yi martani kan harin

Kakakin rundunar ƴan sandan Jihar Edo, Eno Ikoedem, ta tabbatar da cewa an sanar da su harin da misalin ƙarfe 8:00 na dare a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

'Mutane sun yi ta kansu,' Halin da ake ciki a garin da aka kashe sojan Najeriya

Ta bayyana cewa binciken farko ya nuna an fasa tagogi biyu tare da lalata tutocin jam’iyyar, sannan an tura jami’an tsaro yankin domin tabbatar da zaman lafiya.

Hukumar ƴan sandan ta sha alwashin kamo duk wanda ke da hannu a wannan ta'addanci domin ya fuskanci shari'a, tana mai cewa ba za ta amince da barazanar siyasa ba.

ADC ta yi kira ga jami'an tsaro da su tabbatar da tsaro a ofisoshin jam'iyyun siyasa a Edo.
Taswirar jihar Edo, inda 'yan bangar siyasa suka farmaki sakatariyar jam'iyyar ADC. Hoto: Legit.ng
Source: Original

ADC ta yi kira ga jami'an tsaro

Shugaban ADC, Odion ya jaddada cewa tsarin dimuƙaraɗiyya ya ba kowa damar shiga jam'iyyar da yake so, don haka babu wanda zai tilasta musu barin tsarin siyasarsu.

Wannan hari ya janyo fargaba a tsakanin sauran kananan jam'iyyu a jihar, waɗanda ke ganin wannan a matsayin farkon matsin lamba na siyasa, in ji rahoton Tribune.

Mazauna birnin Benin da ADC sun yi kira ga gwamnati da ta tabbatar da tsaro a ofisoshin jam'iyyun siyasa domin guje wa rikicin da zai iya janyo asarar rayuka.

An kona sakatariyar jam'iyyar ADC

A wani labari, mun ruwaito cewa, wasu miyagu sun cinnawa sakatariyar jam'iyyar adawa ta ADC a Najeriya wuta wanda ya jawo asarar dukiyoyi.

Kara karanta wannan

APC ta ce Sheikh Pantami zai taka rawa yayin sabunta katin jam'iyya a Gombe

Ofishin jam’iyyar ADC da ke jihar Ekiti ya kone kurmus tun kafin a rantsar da sababbin shugabannin jam’iyyar da aka zaba a matakin jiha.

Kadarorin da suka lalace sun hada da rumfuna 1000 da ke dauke da kujeru, da wasu sassan ginin da suka kama da wuta, cewar majiyoyi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com