APC Ta Ce Sheikh Pantami zai Tika Rawa yayin Sabunta Katin Jam'iyya a Gombe
- Jam’iyyar APC a Gombe ta yi karin haske kan zuwan Sheikh Isa Ali Pantami ofishin jam’iyyar domin sabunta katinsa a ranar 4 ga Fabrairun 2026
- Sakataren tsare-tsare na APC ya yi bayani kan zargin da aka yi wa Pantami da kuma abin da jam’iyyar ke bukata daga duk wani sabon ko tsohon mamba
- Pantami ya mayar da martani, yana bayyana tarihinsa a siyasa da rawar da ya taka tun kafin kafuwar APC, tare da gode wa shugabannin jam’iyyar
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Gombe – Jam’iyyar APC a jihar Gombe ta yi martani kan sabunta katin jam’iyya da Sheikh Isa Ali Pantami ya yi, bayan wasu kalamai da suka dauki hankulan jama’a game da rawar da ake sa ran zai taka a siyasar jam’iyyar.
Batun ya janyo muhawara ne bayan sakataren tsare-tsare na APC na jihar, Ibrahim Musa Bakas, ya yi tsokaci kan zuwan Pantami ofishin jam’iyyar.

Source: Facebook
A wani bidiyo da Hamza Abubakar ya wallafa a shafinsa na Facebook, Bakas ya yi maganganu game da rashin zuwan Pantami ofishin jam'iyyar a baya.
Jawabin APC kan zuwan Isa Pantami
Ibrahim Musa Bakas ya ce Sheikh Isa Ali Pantami ya zo ofishin APC domin yankan karin jam’iyya da sabunta katinsa, amma ya nuna cewa akwai abubuwan da jam’iyyar ke so a fayyace.
Bakas ya ce an yi kuskure wajen yadda wasu mutane suka rika yabon Sheikh Pantami, yana mai cewa abin da suka fada ba gaskiya ba ne.
A cewarsa, Pantami bai taba zuwa ofishin jam’iyyar ba a baya, har wasu ke dauka cewa dan jam’iyyar ADC ne kuma haka jama'a da dama ke zata.
Ya kara da cewa tun da Pantami ya shiga APC, dole ne ya ajiye wasu ayyuka ya rika zuwa ofishin jam’iyya, domin siyasa na bukatar hulda da shugabanni da mambobi.
Jam'iyyar APC ta ce Pantami zai taka rawa

Kara karanta wannan
Pantami ya sabunta rajistar zama dan APC, ya tuna shawarar da Buhari ya ba shi kan siyasar Gombe
Bakas ya ce duk da cewa an san Sheikh Pantami da ilimin addini da na zamani, siyasa na da nata dabi’u, yana mai cewa:
“Za a kada ganga Malam ya yi rawa,”
Bakas ya kara da cewa tunda gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya taka rawa, ba wanda zai ki yin hakan saboda siyasa.
Sakataren ya amince cewa Pantami ya taba yi wa jam’iyyar alheri a baya, yana mai cewa ya kawo gudunmawar da ba a taba samu ba.
Martanin Sheikh Pantami ga APC
A nasa bangaren, Sheikh Isa Ali Pantami ya ce yan APC sun kasu kashi biyu, akwai wadanda suke bayyane da kuma masu farin kaya, yana mai cewa shi yana cikin masu farin kaya.
A wani bidiyo da Abba Sani Pantami ya wallafa a Facebook, Malamin ya kara da cewa wasu na dauka cewa yanzu ne ya shiga siyasa, amma ba haka ba ne, domin tun 2001 yake harkokin siyasa.
A cewarsa, a lokacin da aka fara kiran Muhammadu Buhari ya shiga siyasa, suna daga cikin wadanda suka je har gidansa domin shawo kansa.

Source: Facebook
Gudunmawar Pantami a kafuwar APC
Pantami ya bayyana cewa yana daga cikin wadanda suka kafa APC, yana mai cewa hadakar ACN da CPC da ta haifar da jam’iyyar an tattauna ta a gidan marigayi Sarkin Borgu a Kaduna a shekarar 2010.
Ya kara da cewa tarukan APC da aka yi a 2011 ma yana cikin mahalarta, yana mai jaddada cewa siyasar yau ba ita ce farkon shigarsa ba.
A karshe, Pantami ya gode wa shugabannin APC bisa tarba da suka masa, tare da bayyana farin cikinsa na sabunta katin jam’iyyar a hukumance.
Legit ta tattauna da Babayo
A wata hira da wani malamin Izala a Gombe, Muhammad Babayo, ya bayyanawa Legit cewa shigar malamai siyasa na da fa'ida amma kuma na da hadari.
Malam Babayo ya ce:
"Dole a samu mutanen kirki su shiga kowace harka domin a gyara ta. Amma kuma harkar siyasa abin tsoro ce matuka."
"Yanayin siyasar Najeriya na bukatar dogon nazari kafin mutum ya shiga. Fatan alheri kawai zan yi wa Pantami."
APC za ta samu karin gwamnonin jihohi
A wani labarin, kun ji cewa, Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya bayyana cewa karin gwamnoni na hanyar shiga jam'iyyar APC.
Gwamna Abdullahi Suke ya ce ayyukan alheri da shugaba Bola Tinubu ke yi a Najeriya ne ke sanya 'yan siyasa komwa APC mai mulki.
Ya kara da cewa babu abin tayar da hankali domin 'yan siyasa na taruwa a jam'iyyar APC, ya ce hakan ba barazana ba ne ga dimokuradiyya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


