An Biyo kan Masu Shara: Gwamna Ya Yi Barazanar Korarsu kan Rijistar Zama Yan APC

An Biyo kan Masu Shara: Gwamna Ya Yi Barazanar Korarsu kan Rijistar Zama Yan APC

  • Gwamnatin Taraba ta yi barazana ga wasu ma'aikata yayin da ake ci gaba da yin rijistar mambobin jam'iyyar APC a jihar
  • Shugaban hukumar tsaftar muhalli ya ce duk wanda bai mallaki katin zama 'dan APC ba zai fuskanci hukunci har da kora daga aiki
  • Masu shara sun zargi gwamnati da tilasta musu shiga APC, inda jami’in gwamnati ya tabbatar da hakan a fili ba tare da tsoron komai ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Jalingo, Taraba - Gwamnatin Jihar Taraba ta bayyana aniyarta ta sallamar dukkan ma’aikatan sharan tituna da ke karkashin shirin 'Operation Keep Taraba Clean'.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa an yi masu barazanar kora daga aiki idan ba su yi rajistar jam’iyyar APC mai mulki ba a jihar.

Gwamnati ta yi barazanar korar ma'aikata kan rijistar katin APC
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima yayin karbar Gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba. Hoto: Agbu Kefas.
Source: Facebook

Shugaban hukumar kula da muhalli da tsaftar gari ta jihar, Hon. Illiya Kefas, ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a birnin Jalingo, babban birnin jihar, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Gwamnati ta bada umarnin rufe makarantu a fadin jihar Kogi

Kashim Shettima ya karbi Gwamna a APC

Wannan lamari na zuwa ne kwanaki kadan bayan Gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba ya shiga jam'iyyar APC mai mulki a hukumance.

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ne ya karbe shi a wani gagarumin taro da aka yi a Jalingo.

Taron ya samu halartar manyan yan siyasa a Najeriya ciki har da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin.

Gwamnatin Taraba ta yi barazana ga ma'aikata kan shiga APC
Gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba. Hoto: Agbu Kefas.
Source: Twitter

Rijistar APC: Barazanar da aka yi wa ma'aikata

Illiya Kefas ya ce babu wani ma’aikaci a hukumar da za a bari idan ya ki shiga rajistar APC ta intanet ake gudanarwa a halin yanzu.

A cewarsa, duk wanda ya ki yin rajistar APC ba kawai fuskantar dakatar da albashi zai yi ba, har ma da sallamar aiki gaba daya.

Rahotanni sun nuna cewa masu shara tituna sun zargi gwamnatin jihar da tilasta musu shiga rajistar APC, tare da yi musu barazanar hukunci idan suka ki.

Sai dai da aka tuntubi Hon. Illiya Kefas domin karin bayani, ya tabbatar da lamarin ba tare da ja da baya ba.

Kara karanta wannan

Ministan tsaro zai rikide zuwa siyasa bayan gwamnatin APC ta ba shi mukami

Ya ce:

“Eh, duk wanda ya ki yin rajistar APC ba zai samu albashi ba, kuma zan sallame shi. Zan kori duk wanda ba shi da katin mambobin APC.”

Maganar ta janyo ce-ce-ku-ce a jihar, musamman ganin yadda ake zargin amfani da matsin lamba wajen tilasta wa ma’aikatan gwamnati shiga jam’iyyar siyasa mai mulki.

Lamarin ya zo ne a daidai lokacin da ake ta ce-ce-ku-ce a kasa kan zargin tilasta wa wasu yan Najeriya har da ma’aikatan gwamnati shiga rajistar APC ta intanet.

APC ta tilasta wa ma'aikata rijista a jam'iyya

A wani labarin jam'iyyar APC ta yi karin haske bayan zargin da ake yi mata cewa tana tilasta ma'aikatan gwamnati shiga cikinta.

Sakataren yada labarai ya ce zargin ƙarya ne tsantsa, tana zargin ADC da yaɗa bayanan bogi saboda nasarar rajistar jam'iyyar.

APC ta tsawaita wa’adin rajista daga 31 ga Janairu zuwa 8 ga Fabrairu 2026 saboda dimbin ‘yan Najeriya da suka shiga rajistar da kansu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.