Abu Ya Girma: Tinubu Ya Sake Shiga tsakani kan Rikicin Rivers, Ya Ba Fubara da Wike Umarni
- Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarni na musamman domin dakatar da rikicin siyasa da ke gudana tsakanin Gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara da Nyesom Wike
- Matakin shugaban kasar ya biyo bayan watanni na rikicin siyasa da ya jawo barazanar tsige Gwamna Fubara daga kujerarsa
- Shugaba Bola Tinubu ya ba da umarni ga bangarorin Wike da Gwamna Fubara kan rikicin siyasar na jihar Rivers
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sake shiga tsakanin a rikicin siyasar da ya addabi jihar Rivers.
Shugaba Tinubu ya ba da umarnin a dakatar da yunkurin tsige Gwamna Siminalayi Fubara daga kan mukaminsa.

Source: Twitter
Kamar yadda tashar Arise News ta ruwaito, majiyoyi da dama sun bayyana matsayar ta Shugaba Tinubu kan rikicin siyasar na jihar Rivers.
Me Tinubu ya ce kan rikicin Rivers
Majiyoyi sun ce kafin ya tashi zuwa kasar Turkiyya a wata ziyarar aiki a ranar 26 ga Janairu, Shugaba ya gargadi Wike da ya dakatar da duk wani shiri ko yunƙurin tsige Gwamna Fubara nan take.
Shugaban kasar ya jaddada cewa ci gaba da gaba tsakanin bangarorin biyu zai lalata tafiyar da mulki da kwanciyar hankali a jihar mai arzikin man fetur.
Wata majiya ta ruwaito Tinubu na cewa:
“Dole ne a bar Fubara ya yi mulki, amma dattawa da shugabannin siyasa irin su Wike sun cancanci girmamawa. Ba za a yi watsi da girma a siyasa ba saboda sabanin kai da kai.”
Fubara da Wike: Sharuddan yarjejeniyar sulhu
Wannan sabon yunkuri na Tinubu ya zo da tsauraran sharudda, inda aka ce Fubara zai amince da Wike a hukumance a matsayin jagoran siyasa na jihar Rivers, wanda ke da ikon karshe kan harkokin jam’iyya.
A daya bangaren kuma, an umurci Wike da magoya bayansa da su dakatar da duk wani abu da ya shafi tsige gwamnan.
"Manufar ita ce tabbatar da kwanciyar hankali da ingantaccen tafiyar da mulki a jihar Rivers. Shugaban kasa ya bayyana karara cewa dole ne duk wata matsalar cikin jam’iyya ta bi karkashin ikon Wike.”
- Wata majiya
Umarnin ya kuma shafi zabukan cike gurbi na majalisar dokokin jihar Rivers da za a yi a mazabun Ahoada East II da Khana II, inda aka ce ’yan takarar Wike za su samu amincewar jam’iyyar APC.
Hukumar zabe ta kasa INEC ta sanya ranar 21 ga Fabrairu, 2026, domin gudanar da zabubbukan.
Tinubu ya taba shiga tsakani a baya
Kokarin sulhu da Tinubu ya taba yi a baya, ciki har da dokar ta-baci ta watanni shida da aka ayyana a watan Maris 2025, bai kai ga kawo karshen rikicin ba.
Wannan sabon umarni na shugaban kasa na nuni da yunƙurin dawo da daidaito a tafiyar da mulki da kuma hana sake tabarbarewar al’amura a jihar.

Source: Facebook
Batun tazarcen Gwamna Fubara
Duk da cewa shiga tsakanin da shugaban kasar ya yi na nufin tilasta zaman lafiya, majiyoyi sun bayyana cewa an dakatar da tattaunawa kan yiwuwar takarar Fubara a zaben 2027, Vanguard ta kawo labarin.
Sun ambato Tinubu na cewa lokacin irin wannan magana bai yi ba tukuna ganin ba a buga gangar siyasa ba.
Dalilin hana Wike filin taron siyasa a Rivers
A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamnatin jihar Rivers ta yi magana kan dalilinta na hana Nyesom Wike yin amfani da filin wasa don taron siyasa.
Kwamishinan harkokin wasanni na jihar, Chris Green ya ce babu wata takardar neman izini da gwamnatin Rivers ta karɓa ko ta ƙi amincewa da ita.
Ya ƙara da cewa baya ga rashin gabatar da buƙatar amfani da filin wasan, filin na fama manyan gyare-gyare kuma ba ya da aminci ga taron jama’a.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


