Siyasar 2027: Atiku Ya Yi Ganawar Sirri da Babban Sanatan APC Abdulaziz Yari
- Tsohon mataimakin shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya yi wata ganawar sirri da Sanatan Zamfara ta Yamma, Abdulaziz Yari, a Abuja
- Ganawar ta zo ne a daidai lokacin da ake ta raɗe-raɗin sauye-sauyen siyasa da hadin-gwiwar jam’iyyu gabanin zaben Najeriya na 2027
- Duk da babu wata sanarwa a hukumance, wasu majiyoyi sun ce irin wadannan ganawa na daga cikin shirye-shiryen da ’yan siyasa ke yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya gudanar da wata ganawar sirri da tsohon Gwamnan Jihar Zamfara kuma Sanatan Zamfara ta Yamma, Abdulaziz Yari, a Abuja.
Majiyoyi sun bayyana cewa an gudanar da taron ne ta bayan fage, inda babu wani daga cikin bangarorin biyu da ya fito ya yi wa manema labarai bayani.

Source: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa zuwa lokacin hada wannan rahoto, babu wata sanarwa da aka fitar a hukumance da ke bayyana dalilin haduwar shugabannin.
Atiku Abubakar ya gana da Abdulaziz Yari
Rahoto ya nuna cewa ganawar Atiku da Abdulaziz Yari ta faru ne a wani lokaci da ake ta tattaunawa kan yiwuwar sake tsarawa da daidaita karfi a fagen siyasar Najeriya.
Rahoton Daily Post ya nuna cewa Sanata Abdulaziz Yari ya gana da Atiku ne a gidan tsohon mataimakin shugaban kasar da ke Abuja.
Zama irin wannan, musamman tsakanin manyan ’yan siyasa daga jam’iyyu daban-daban, na yawan janyo hasashe daga jama’a.
Atiku Abubakar dai shi ne dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, kuma ya sha bayyana cewa yana nan daram a siyasar kasa kuma yana da burin takara a 2027.
Karfin Abdulaziz Yari a siyasa
A daya bangaren kuma, Abdulaziz Yari sanata ne mai ci a karkashin jam’iyyar APC mai mulki. Bayan kaddamar da Majalisar Tarayya ta 10, Yari ya nemi kujerar Shugaban Majalisar Dattawa, amma bai samu nasara ba.
Yari dai na daga cikin fitattun ’yan siyasa daga Arewa maso Yamma, kuma kasancewarsa a cikin jam’iyya mai mulki na kara sanya ganawa da Atiku ta zama abin lura a idon masu bibiyar siyasa.
Idan ana maganar tsofaffin gwamnonin da har gobe ake damawa da su, dole a sako tsohon gwamnan gwamnonin Najeriyar duk da jiharsa na hannun APC a yau.
Hasashen majiyar ADC game da ganawar
Wata majiya daga cikin jam’iyyar ADC, wadda ta nemi a sakaya sunanta saboda ba ta da izinin yin magana a bainar jama’a, ta ce a ‘yan makonnin nan ana ganin karuwar ganawa da tuntubar juna tsakanin manyan ’yan siyasa.
Majiyar ta ce:
“Wannan lokaci ne na siyasa, kuma ana ganin sauye-sauye a sassa daban-daban na kasar nan. Duk da ba a bayyana cewa wannan ganawa ta siyasa ba ce, ba za a iya kawar da yiwuwar hakan ba a wannan lokaci.”
A halin yanzu dai, Atiku Abubakar da Abdulaziz Yari ba su fitar da wata sanarwa da ke tabbatar da manufar ganawarsu ba, lamarin da ya bar jama’a cikin jiran karin bayani kan abin da haduwar za ta haifar a siyasar Najeriya.

Source: Depositphotos
Maganar Atiku kan takarar 2027
A wani labarin, mun kawo muku cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi magana kan siyasar 2027 da ke kara daukar zafi a ADC.
Yayi magana ne kan yadda batun takarar 2027 a jam'iyyar adawa ke kokarin haddasa rikici tsakanin magoya bayansa da na Peter Obi a intanet.
Atiku ya martani ne ga rubutun wani dan ADC a kafar X, yana mai cewa duk mai kishin jam'iyyar ba zai so haddasa rikici ba daidai wannan lokaci.
Asali: Legit.ng


