Magana Ta Fito: Abin da Buhari Ya Gayawa Gwamnonin Arewa kan Dan Takararsa a Zaben 2023
- An yi ta maganganu kan batun ko akwai dan takarar da marigayi Muhammadu Buhari ya so ya gaje shi.a zaben shekarar 2023
- Tsohon shugaban ma'aikatar fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari ya yi tsokaci kan batun yayin wata tattaunawa da aka yi da shi
- Farfesa Gambari ya bayyana cewa tabbas marigayi Buhari ya gayawa gwamnonin Arewa matsayarsa kan batun dan takarar da ya ke goyom baya
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa a zamanin marigayi Shugaba Muhammadu Buhari, Farfesa Ibrahim Agboola Gambari, ya yi magana kan zaben 2023.
Ibrahim Gambari ya ce Buhari bai yi amanna da ya zabi wanda zai gaje shi ba gabanin zaben shugaban kasa na 2023.

Source: Facebook
Gambari ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, 2 ga watan Fabrairun 2026 yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na tashar Channels tv.
Ya mayar da martani kan ikirarin da ke cewa Buhari ya ruɗi tsohon mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, da tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, su shiga takarar shugaban kasa ba tare da ya fayyace wanda ya fi so ba.
"Buhari bai ji cewa ya kamata ya zabi wani dan takara ya mara masa baya ba.”
- Farfesa Ibrahim Gambari
Gwamnonin Arewa sun gana da Buhari
Ya bayyana cewa tsohon shugaban kasar ya fito karara da matsayarsa ne a lokacin da gwamnonin jihohin Arewa 19 suka kai masa ziyara bayan sun amince cewa ya kamata mulki ya koma Kudancin Najeriya.
“Gwamnonin jihohin Arewa 19 sun zo wajen Buhari bayan sun fitar da sanarwa cewa shugaban kasar Najeriya na gaba ya fito daga Kudu, kuma sun sanya hannu a kan hakan.”
- Farfesa Ibrahim Gambari
A cewar Gambari, gwamnonin sun nemi ganawa da Buhari ne domin su tabbatar ko tuni ya riga ya zabi wanda zai gaje shi.
"Suka ce suna son ganawa da shugaban kasa. Lokacin da na gaya masa, ya tambaye ni me ya sa? Sai na ce suna son sanin ko ka riga ka zabi dan takara, tunda kai ne shugabansu.”

Kara karanta wannan
Yadda aka gyara Tudun Biri bayan sojojin Najeriya sun yi kuskuren jefa bam a taron Maulidi
- Farfesa Ibrahim Gambari
An so jin matsayar Buhari kam dan takararsa a 2027
Farfesa Ibrahim Gambari ya ce ya halarci taron don haka abin da yake fada shi ne kawai abin da ya gani da idonsa.
“Na kasance a taron, kuma zan yi magana ne bisa abin da na sani, kuma dukkansu shaidu ne.”
“Sun zo. Sai na shiga na fada masa cewa baki sun zo. Suna son su sani ko kana da dan takarar da ka zaba domin shugaban kasa da kuma takarar jam’iyya. Na kuma ce, ni ma a matsayina na shugaban na’aikatanka, ina son sanin hakan.”
- Farfesa Ibrahim Gambari

Source: UGC
Buhari ya ce bai da dan takara
Gambari ya bayyana cewa martanin Buhari ya kasance kai tsaye ne ba tare da wata kwana-kwana ba.
"Sai ya ce, ba ni da dan takarar da na zaba domin ya gaje ni a matsayin shugaban kasa. Sai na ce masa, to ya kamata ka gaya musu. Kuma ya gaya musu haka nan take.”

Kara karanta wannan
'Masu tunanin 'yan Arewa ba za su zabi Tinubu a 2027 ba sun tafka babban kuskure'
- Farfesa Ibrahim Gambari
Dalilin Buhari na ba Lai mukamin Minista
A wani labarin kuma, kun ji cewa Lai Mohammed ya yi magana kan mukamin Minista da ya samu a gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari.
Lai Mohammed ya bayyana cewa Buhari ya ba shi mukami ne saboda amana, biyayya, da kuma doguwar hidima da ya yi masa.
Tsohon ministan ya bayyana cewa alaƙarsa da Buhari ta samo asali ne tun a shekarar 2012 lokacin da ya roƙi Buhari ya rubuta gabatarwa ga littafinsa na farko.
Asali: Legit.ng
