Nentawe Ya Fadi Sirrin Nasarar Jam'iyyar APC kan Jam'iyyun Adawa
- Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda ya yi tsokaci kan yanayin yadda ake buga siyasa a Najeriya
- Farfesa Nentawe Yilwatda ya bayyana akwai bambanci tsakanin jam'iyyar APC da sauran jam'iyyun adawa a kasar nan
- Shugaban na APC ya haska kuskuren da jam'iyyun adawa ke yi, wanda hakan ya sanya ake ganin jam'iyyar na yin nasara a kansu
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bayyana abin da ya bambanta jam'iyyar da sauran jam'iyyun adawa.
Farfesa Nentawe ya ce jam’iyyun adawa a kasar nan sun fi bata lokaci ne wajen surutu a talabijin, maimakon su mayar da hankali kan wayar da kan jama’a a matakin tushe.

Source: Twitter
Yilwatda ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi, 1 ga watan Fabrairun 2026 yayin wata hira da tashar Trust TV.

Kara karanta wannan
APC ta sake taso da batun sauya shekar Kwankwaso zuwa cikinta, ta fadi tanadin da ta yi masa
Bambancin APC da jam'iyyun adawa
A yayin hirar ya amsa tambayoyi kan wayar da kan jama’a ta fuskar siyasa da kuma zargin cewa jam’iyyar mai mulki na kokarin kafa tsarin jam’iyya daya a Najeriya.
"Jam’iyyun adawa sun fi bata lokaci suna magana a talabijin. Ba aikinmu ba ne mu taimaka wa makiyanmu su bunkasa."
"Ba za mu ciyar da makiyanmu ba. Ba aikinmu ba ne. Su yi aiki, su fita titi, su yi tuntuba da jama’a.”
- Farfesa Nentawe Yilwatda
Wane aiki APC ke yi?
Ya ce karfin APC ya samo asali ne daga aikin wayar da kan jama’a a bayan fage a fadin kasar nan, ba wai yawan fitowa kafafen yada labarai ba.
"Jiya na dawo daga Taraba. Gobe kuma zan je Katsina. Ba karbar gwamna zan yi ba; aikin wayar da kan jama’a zan je yi. Ina haduwa da mutane, ina tattaunawa da su.”
“Kwana hudu da suka wuce na je wata jiha daban. A ranar Asabar kuma zan je wata jiha, ina zagayawa, ina magana da jama’a, ina wayar da kan jama’a a bayan fage.”
- Farfesa Nentawe Yilwatda
APC na ganin sakamakon jajircewarta
A cewarsa, abin da jama’a ke gani a talabijin sakamako ne kawai, ba cikakken aikin siyasa ba.
“Mu kan fi bata lokaci a bayan fage fiye da abin da kuke gani a talabijin. Abin da kuke gani a talabijin sakamako ne, amma aikin yana bayan fage."
“Me ya sa su ma ba za su bata lokaci a bayan fage ba, domin mu ga masu sauya sheka daga APC zuwa jam’iyyunsu?”
- Farfesa Nentawe Yilwatda

Source: Twitter
Da gaske APC na son tsarin jam'iyya daya?
Da yake mayar da martani kan zargin cewa APC na shirin kafa tsarin jam’iyya daya a Najeriya, da kuma kalaman da aka alakanta da tsohon shugabanta, Abdullahi Ganduje, cewa ba zai zama matsala ba idan Najeriya ta koma jam’iyya daya, Yilwatda ya musanta hakan.
“A’a. Idan duk ’yan Najeriya suka goyi bayan APC, za mu yi farin ciki matuka idan kowa ya mara wa APC baya, amma ba jam’iyya daya ba, domin muna son a rika samun wadanda za su rika kalubalantarmu.”
- Farfesa Nentawe Yilwatda
Batun komawar Kwankwaso APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta yi magana kan yiwuwar sauya shekar Rabiu Musa Kwankwaso zuwa cikinta.
Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bayyana cewa kofar jam'iyyar a bude take ga madugun na Kwankwasiyya.
Sai dai, Farfesa Nentawe ya bayyana cewa ba su tattaunawa da Kwankwaso kan batun sauya shekarsa zuwa jam'iyyar.
Asali: Legit.ng

