Shettima Ya Je Kaduna, Ya Bayyana Abin da Gwamna Uba Sani Ke Mayar da Jihar

Shettima Ya Je Kaduna, Ya Bayyana Abin da Gwamna Uba Sani Ke Mayar da Jihar

  • Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya je jihar Kaduna domin kaddamar da shirin sake tsugunar da mutanen kauyen Tudun Biri
  • Kashim Shettima ya kwararo yabo ga Gwamna Uba Sani kan salon jagorancin da yake yi a mulkin jihar Kaduna
  • Mataimakin shugaban kasar ya nuna cewa jam'iyyar APC, ta ci gajiyar abubuwa da gwamnan yake yi a Kaduna tun bayan hawansa mulki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kaduna - Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya yi magana kan salon mulkin Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna.

Kashim Shettima ya ce salon shugabancin Gwamna Uba Sani na kara mayar da jihar Kaduna zuwa jiha mai jam’iyya daya, sakamakon yawaitar sauya sheka da ’yan adawa ke yi zuwa jam’iyyar APC.

Shettima ya kwararo yabo ga Gwamna Uba Sani
Kashim Shettima na magana tare da Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna Hoto: Uba Sani
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce Shettima ya bayyana hakan ne a karshen mako yayin kaddamar da shirin sake tsugunar da mutanen kauyen Tudun Biri a jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

APC ta kara karfi, Shettima ya karbi gwamnan da ya shiga jam'iyyar a hukumance

Me Shettima ya ce kan Gwamna Uba Sani?

Kashim Shettima ya yabawa gwamnan kan abin da ya kira kokarin hada kowa da kowa wajen fadada karfin APC a fadin jihar.

"Gwamna Uba Sani, muna matukar godiya. A hankali kana mayar da Kaduna jiha mai jam’iyya daya, inda ’yan majalisar wakilai daga Soba, Makarfi da Kudan ke kan hanyarsu ta shigowa APC."

- Kashim Shettima

Shettima ya tuna baya kan zaben 2023

Da yake waiwayen sakamakon zabubbukan gama-gari na 2023, Shettima ya ce APC ta sha babban kaye a Kaduna kafin wadannan sauya shekar da ake ta yi.

"A 2023, mun rasa dukkan kujerun Sanata uku ga PDP. Daga cikin ’yan majalisar tarayya 16, APC na da guda hudu kacal, PDP na da 10, yayin da jam’iyyar LP ke da biyu.”

- Kashim Shettima

A cewarsa, yanayin ya sauya tun daga lokacin, sakamakon abin da ya kira kokarin Gwamna Sani da shugabannin jam’iyyar, inda ya kara da cewa fitattun ’yan adawa da dama sun shiga APC.

Kara karanta wannan

Yadda aka gyara Tudun Biri bayan sojojin Najeriya sun yi kuskuren jefa bam a taron Maulidi

"Muna tare da tsohon Gwamna Mukhtar Ramalan Yero. Haka kuma muna da Sanata Sunday Marshal.”

- Kashim Shettima

Uba Sani ya samu yabo

Shettima ya bayyana abubuwan da ke faruwa a Kudancin Kaduna a matsayin abin da bai taba faruwa ba, yana mai cewa yankin ya saba zabar sanatoci ne karkashin jam’iyyar PDP tun shekarar 1999.

"Wannan ne karo na farko a tarihi da APC ke da Sanata a Kudancin Kaduna, sakamakon kokarin Gwamna Uba Sani.”

- Kashim Shettima

APC na kara karfi a Kaduna

Ya kuma sanar da sauya shekar wani dan majalisar wakilai mai ci daga mazabar Igabi, wadda ya ce na daga cikin mafi girma a kasar nan, mai rumfunan zabe kusan 600 da kuma masu rijista kusan 400,000, jaridar Vanguard ta kawo labarin.

Kashim Shettima ya yabawa Gwamna Uba Sani
Kashim Shettima na jawabi a wajen kaddamar da ayyuka a Tudun Biri Hoto: Uba Sani
Source: Facebook

Mataimakin shugaban kasar ya alakanta wadannan sauya shekan da salon shugabancin gwamnan, wanda ya ce ya gina amana tsakanin bangarorin siyasa da yankuna daban-daban.

"Wannan shi ne shugabanci. Ba tare da salonka na hada kai ba, bana ganin Sunday Marshal da sauran shugabannin Kudancin Kaduna za su shiga APC."

Kara karanta wannan

Sanusi II ko Aminu Ado: Gwamna Abba ya bayyana wanda zai ci gaba da zama Sarkin Kano

- Kashim Shettima

APC ta musanta batun sauya Shettima

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar ApC ta yi karin haske kan jita-jihar sauya Kashim Shettima a zaben shekarar 2027.

APC ta yi watsi da rahotannin da ke cewa ana shirin sauya Kashim Shettima daga matsayin mataimakin shugaban kasa a matsayin abokin takarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu gabanin zaben 2027.

Jam’iyyar ta ce ta maida hankali ne kan goyon bayan Shugaba Bola Tinubu da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima domin aiwatar da ajandar “Renewed Hope” ta gwamnatin tarayya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng