An Ga Mataimakin Gwamnan Kano a Karon Farko bayan Gwamna Abba Ya Koma APC

An Ga Mataimakin Gwamnan Kano a Karon Farko bayan Gwamna Abba Ya Koma APC

  • Mataimakin gwamnan Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo ya halarci taron sauka da haddar Alkur'ani mai girma yau Lahadi
  • Wannan ne karo na farko da aka ga Aminu Gwarzo a taron jama'a tun bayan sauya shekar Gwmana Abba Kabir Yusuf a hukumance
  • Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin Kano ta matsa wa Aminu Gwarzo ya sauka daga kujerar mataimakin gwamnan idan ba zai bi Abba Gida-Gida APC ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Yayin da ake ta ce-ce-ku-ce kan makomarsa, mataimakin gwamnan Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya fito bainar jama'a.

Aminu Gwarzo ya halarci wani taron saukar karatun Alkur'ani mai girma, wanda shi ne taro na farko da ya halarta tun bayan sauya shekar Gwamna Abba Kabir Yusuf daga NNPP zuwa APC.

Aminu Gwarzo.
Mataimakin gwamnan Kano, Aminu Gwarzo a taron saukar Alkur'ani Hoto: Comr. Aminu Abdussalam Gwarzo
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin wata gajeruwar sanarwa da mataimakin gwamnan ya wallafa a shafinsa na Facebook da yammacin yau Lahadi, 1 ga watan Fabrairu, 2026.

Kara karanta wannan

Sanusi II ko Aminu Ado: Gwamna Abba ya bayyana wanda zai ci gaba da zama Sarkin Kano

An matsawa Aminu Gwarzo ya yi murabus

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da alaka ke kara tsami tsakanin Gwamna Abba da mataimakinsa, Aminu Gwarzo, wanda ya kekashe kasa ya ki komawa jam'iyyar APC.

A makon da ya gabata ne Gwamna Abba da galibin mambobin majalisar zartarwa ta Kano suka sauya sheka daga NNPP zuwa APC.

Sai dai kwamishinoni biyar sun nuna ba za su bi gwamna zuwa APC ba, bisa haka suka yi murabus daga mukamansu tare da jaddada mubaya'arsu ga jagoran NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso.

A rahoton da Daily Trust ta kawo, majiyoyi da dama sun nuna cewa an matsa wa Aminu Gwarzo ya yi murabus daga kujerar mataimakin gwamnan Kano matukar ba zai dawo APC ba.

Gwamnatin Kano ta hannun kwamishinan yada labarai, Hon. Ibrahim Wiaya ta shawarci Gwarzo da ya yi murabus daga mukaminsa idan ba zai bi tafiyar Gwamna Abba ba.

Taron sauka.
Mataimakin gwamnan Kano, Aminu Gwarzo yana mika kyauta a taron sauka Hoto: Aminu Abdussalam Gwarzo
Source: Facebook

Mataimakin gwamna ya halarci saukar Alkur'ani

Kara karanta wannan

An zo wajen: Matsayar majalisar dokokin Kano kan tsige mataimakin Gwamna Abba

Yayin da ake dakon jin martaninsa, an ga mataimakin gwamnan ya halarci taron sauka da haddakar Alkur'ani mai girma a a makarantar Markaz Al-Mu’allim Lawan Al-Hafiz da ke cikin jihar Kano.

Aminu Gwarzo ya bukaci daliban da suka haddace Littafin Allah mai tsarki da su yi amfani da abin da suka karanta wajen tafiyar da rayuwarsu ta yau da kullum

"A safiyar yau, na halarci taron saukar Alkur’ani da haddar Alkur’ani mai girma na makarantar Markaz Al-Mu’allim Lawan Al-Hafiz, wanda dalibai 161 suka kammala.
"Ina kira ga daliban da su yi amfani da abin da suka haddace ta hanya ta gari, sannan su kasance jakadu na kwarai ga addinin Musulunci."

- Aminu Abdussalam Gwarzo.

Kwamishina da wasu jiga-jigai sun koma APC

A wani labarin, kun ji cewa dan majalisar wakilai, Alhassan Ado Doguwa, ya karbi daruruwan mambobin jam’iyyar NNPP zuwa jam’iyyar APC a jihar Kano.

Doguwa, wanda ke wakiltar mazabar Doguwa/Tudun Wada a majalisar tarayya, ya jagoranci aikin rajistar mambobin APC inda ya karbi manyan masu sauya sheka daga NNPP.

Manyan mutanen da suka sauya shekar sun hada da Kwamishinan Ruwa kuma tsohon shugaban APC na jiha, Alhaji Umar Haruna Doguwa; da Injiniya Ado Ibrahim Doguwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262