Tafiyar Kwankwasiyya Ta Sake Samun Naƙasu, Kwamishina Ta Bar NNPP, Ta Rike Abba

Tafiyar Kwankwasiyya Ta Sake Samun Naƙasu, Kwamishina Ta Bar NNPP, Ta Rike Abba

  • Ana ci gaba da kama layi a gwamnatin jihar Kano bayan Abba Kabir Yusuf ya bar NNPP zuwa APC mai mulki
  • Kwamishiniyar harkokin mata ta Kano, Hajiya Amina Sani (Amina HOD), ta fice daga NNPP zuwa APC, lamarin da ya tayar da kura a siyasar jihar
  • Gwamnatin Kano ta ce sauya shekar Amina HOD zuwa APC ya nuna rungumar akidar “Kano First” domin ci gaba da zaman lafiya a jihar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kano - Tafiyar Kwankwasiyya ta sake samun rauni a jihar Kano bayan rasa Kwamishina da ta bi Gwama Abba Kabir Yusuf.

Kwamishiniyar harkokin mata, yara da masu bukata ta musamman ta jihar Kano, Hajiya Amina Sani, ta sanar da sauya sheƙa daga jam’iyyar NNPP zuwa APC.

Kwamishina a Kano ta yi murabus
Gwamna Abba Kabir da Rabiu Musa Kwankwaso. Hoto: Abba Kabir Yusuf.
Source: Facebook

Kwamishina a Kano ta koma APC

Kara karanta wannan

'Babu gwamnan da zai zauna a NNPP': An fadi babban dalilin Abba na shiga APC

Hakan na cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na Kano, Ibrahim Waiya, ya fitar da Punch ta samu.

Sanarwar ta ce Amina HOD ta rungumi akidar “Kano First” domin gaggauta ci gaban jihar da kasa baƙi ɗaya.

Hajiya Amina Sani, wacce aka fi sani da Amina HOD, ta kasance daya daga ginshikan tafiyar Kwankwasiyya, kuma an santa da tsayayyiyar akida da jajircewa.

Waiya ya ce matakin ya kuma zo ne domin karfafa zaman lafiya da hadin kai a tsakanin al’ummar Kano, tare da bai wa jama’a damar zabar makomarsu ta siyasa.

A cewar sanarwar, sauya shekar ta zama wani sabon tarihi a siyasar Kano, tare da farkar da hankalin jama’a kan muhimmancin makomar jihar gaba daya.

Gwamnatin ta ce jama’ar Kano yanzu suna zabar tsakanin muradun jihar baki daya da kuma bukatun wasu ‘yan tsirarun mutane masu son zuciya.

Kwamishinar Abba Kabir ta bar NNPP zuwa APC
Gwamna Abba Kabir na jihar Kano. Hoto: Abba Kabir Yusuf.
Source: Facebook

'Amafanin shiga APC da gwamnati ta yi'

Sanarwar ta kara da cewa tafiyar siyasar da ake ciki ba wai magana ba ce kawai, illa tafiya ce mai ma’ana wacce za ta sake daga darajar Kano.

Kara karanta wannan

Sanusi II ko Aminu Ado: Gwamna Abba ya bayyana wanda zai ci gaba da zama Sarkin Kano

Ta ce wannan tafiya za ta mayar da Kano matsayi mai kyau ta fuskar siyasa, tattalin arziki da zamantakewa a cikin jerin jihohin Najeriya.

Gwamnatin ta bayyana cewa kwamishinoni masu rike da manyan ma’aikatu sun tabbatar da biyayya ga Gwamna Abba Yusuf duk da sauye-sauyen siyasa.

Sanarwar ta jaddada cewa iko ba ya gushewa muddin manyan hukumomi suna aiki tukuru wajen kawo sauyi da ci gaba ga al’umma.

Ta ce duk wani yunkurin rikici daga wasu mutane masu tayar da kura ba zai canza gaskiyar da ke faruwa a jihar Kano ba.

Gwamnatin Kano ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da aiki bisa doka da tsarin dimokuradiyya, tare da karfafa hadin kai tsakanin bangarorin gwamnati.

Dan Kwankwaso ya yi murabus

Kun ji cewa dan jagoran Kwankwasiyya, Mustapha Rabiu Kwankwaso ya ajiye muƙaminsa na Kwamishinan Matasa da Wasanni na Kano.

Mustapha Rabi'u Musa Kwankwaso ya ajiye mukaminsa ne a ranar da Gwamna Abba Kabir Yusuf ke koma wa APC a hukumace.

Ya yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf, yana fatan matasa da wasanni za su ci gaba da samun kulawa a gwamnatinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com