Sunan Malami Ya Fito: An Shawarci Kwankwaso kan ’Yan Takarar da Za Su Kifar da Abba
- Kusa a APC, Abdulmajid Dan Bilki Kwamanda ya ce ficewar Abba Kabir zuwa APC babban butulci ne ga Rabiu Kwankwaso
- Kwamanda ya yi hasashen cewa Kwankwaso zai iya kifar da Abba Kabir idan ya tsayar da ‘yan takara ingantattu a zaben shekarar 2027
- Ya ce tasirinsu da mu'amala da jama’a na iya jawo nasara, yana mai cewa akwai manyan kalubalen siyasa a Kano nan gaba
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Kusa a jam'iyyar APC, Abdulmajid Dan Bilki Kwamanda ya yi hasashe kan siyasar Kano bayan Abba Kabir ya koma jam'iyyar.
Kwamanda ya bayyana cewa abin takaici ne yadda Abba Kabir ya butulce wa Rabiu Kwankwaso wanda shi ne ya yi sanadin daukakarsa.

Source: Twitter
Yan takarar da aka shawarci Kwankwaso ya tsayar
Kwamanda ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da DCL Hausa ta zanta da shi kuma ta wallafa a shafin Facebook.
A cikin bidiyon, Kwamanda ya ce idan Kwankwaso ya tsayar da wasu ingantattun yan takara da za su kifar da gwamnatin Abba Kabir.
Ya bayyana Ahmad Garban Bichi da Malam Ibrahim Khalil a matsayin wadanda za su iya kayar da Abba saboda tasirin da suke da shi.
Ya ce:
"Idan Kwankwaso ya tsayar da mutum ingantacce, ina mai tabbatar maka a cikin APC ma sai an ci amanarta, yana da kalubale wannan gwamnan.
"Idan aka tsayar da Ahmad Garban Bichi saboda shi dan manyan mutane ne ina fada maka Kwankwaso zai yi nasara.
"Sai ya dauko Malam Ibrahim Khalil wanda ya yi takarar gwamna a ADC ya mayar da shi mataimakin Ahmad Garban Bichi."

Source: Facebook
Kwamanda ya fadi tasirin Malam Ibrahim Khalil
Kwamanda ya bayyana tasirin da Malam Ibrahim Khalil yake da shi wanda yake ganin zai yi tasiri wurin kayar da Abba Kabir.
Ya nuna damuwa game da butulcin da Abba ya yi wa Kwankwaso bayan shafe shekaru 40 suna tare a siyasance.
"Saboda Ibrahim Khalil dan bakin kasuwa ne, dan dangi ne, malami ne yana da mutane maza da mata, ina ganin Abba yana ganin wannan gwamnati za a kayar da shi.
"Idan ni ne a ra'ayi na, gwara na bar kujerar gwamnan da in bar Kwankwaso, babu wanda ya san Gwamna Abba sai ta dalilin Kwankwaso.
"Shekara 40 ba wasa ba, ina ganin dole butulcin ya yi wa Kwankwaso ya yi masa ciwo, dole ya yi wa masoyan Kwankwaso ma ciwo amma akwai rigimar siyasa zuwa gaba."
- Cewar Kwamanda
An shawarci Kwankwaso ya hada kai da Barau
A wani labarin 'dan jam’iyyar APC, Abdulmajid Dan Bilki Kwamanda, ya ce fitar Abba Kabir Yusuf daga NNPP ya zama babban cin amana ga Rabiu Musa Kwankwaso.
Ya bayyana cewa sun riga sun dauki Sanata Barau Jibrin a matsayin dan takara a Kano, yana mai cewa hadin kan Barau da Kwankwaso zai iya kifar da Abba.
Dan Bilki ya ce tasirin Sanata Rabiu Kwankwaso a Kano bai gushe ba, yana mai jaddada cewa masu bin Abba suna bin bukatar kansu ne ba akida ba.
Asali: Legit.ng

