Bayan Kano Ta Koma Hannun APC, Tinubu Ya Fadi Wanda Zai Zama Jagoran Jam'iyya a Jihar

Bayan Kano Ta Koma Hannun APC, Tinubu Ya Fadi Wanda Zai Zama Jagoran Jam'iyya a Jihar

  • Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya warware batun wanda zai jagoranci APC a duk jihar da jam'iyyar ke mulki a fadin kasar nan
  • Tinubu ya yabawa matakin da gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas ya dauka na sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar APC
  • Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yelwatda ya bukaci Gwamna Kefas ya hada kan 'ya'yan jam'iyya domin samun nasara

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Taraba, Nigeria - Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa gwamnonin da ke karkashin inuwar jam’iyyar APC su ne jagororin jam’iyyar a jihohinsu.

Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin taron karbar Gwamna Agbu Kefas zuwa cikin jam’iyyar APC wanda aka gudanar a birnin Jalingo.

Shugaba Bola Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu lokacin da ya kai ziyarar aiki jihar Katsina Hoto: Ibrahim Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

Jaridar The Nation ta rahoto cewa Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, wanda ya wakilci Tinubu, ya sanar da cewa Gwamna Kefas ya zama jagoran APC a jihar Taraba.

Kara karanta wannan

APC ta kara karfi, Shettima ya karbi gwamnan da ya shiga jam'iyyar a hukumance

Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya sauya sheka daga NNPP zuwa APC.

Bola Tinubu ya yabi Gwamnan Taraba

Shugaba Tinubu ya bayyana aniyarsa ta ba wa gwamna Kefas da majalisar zartarwarsa cikakken goyon baya domin kawo cigaba a jihar Taraba.

Ya nuna cewa gwamnan yana kokari kwarai wajen hada kan jama’a da sasanta duk wani sabani domin samun hadin kai a jihar.

Shugaban ya bukaci al’ummar jihar Taraba da su mara wa Gwamna Agbu Kefas baya tare da ba shi goyon baya domin ya samu nasara.

Haka kuma, ya nuna jin dadinsa kan yadda aka samu gwamnan da ya sauya sheka a shiyyar Arewa maso Gabas, inda ya kira jihohin Adamawa da Bauchi da su bi sahu su dawo jam’iyyar da ke mulki a kasa.

Shugaban APC ya ja hankalin Gwamna Kefas

Tun da farko, Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Farfesa Nentawe Yelwatda, ya yaba wa Gwamna Kefas kan matakin da ya dauka na dawowa jam’iyya mai mulki.

Yelwatda ya ce Kefas bai yi kuskure ba da ya fice daga jam’iyyar PDP wadda ya bayyana a matsayin "jirgin da yake nutsewa."

Kara karanta wannan

Sanusi II ko Aminu Ado: Gwamna Abba ya bayyana wanda zai ci gaba da zama Sarkin Kano

Ya bayyana matakin gwamnan a matsayin babbar nasara da za ta bai wa jihar damar habaka tattalin arziki da kuma sanya matasa da mata su zama masu dogaro da kai.

A cewarsa, yanzu jihar Taraba ta zama wani sashe na jam’iyyar da za ta yi nasara a zaben 2027, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Shugaban APC.
Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda a hedkwatar jam'iyya da ke Abuja Hoto: @OfficialAPCNig
Source: Twitter

Ya kuma tabbatar wa daukacin mambobin APC, tsofaffi da sababbi, cewa kowa zai samu dama iri daya a harkokin jam’iyyar, sannan ya shawarci gwamnan da ya zama uba ga kowa.

Daga karshe, ya ba gwamnan shawara da ya hada kan jam'iyyar APC kuma kada ya nuna bambanci a tsakanin mambobi.

'Yan Arewa za su sake zaben Tinubu?

A wani labarin, kun ji cewa tsohon shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje ya ce babu wanda ya dace mutane su sake zaba a 2027 kamar Bola Ahmed Tinubu.

Ganduje ya bayyana cewa wadanda ke tunanin cewa 'yan Arewa ba za su sake zaben Shugaba Bola Tinubu ba a 2027 sun tafka babban kuskure.

Ganduje ya tunatar da cewa an yi yarjejeniya tun kafin zaben marigayi Shugaba Muhammadu Buhari cewa bayan shekaru takwas na mulkinsa, mulki zai koma Kudu

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262