An Fadi dalilin Hana Wike Shiga Filin Wasa a Rivers domin Taron Siyasar Tinubu

An Fadi dalilin Hana Wike Shiga Filin Wasa a Rivers domin Taron Siyasar Tinubu

  • Gwamnatin Rivers ta ce ba ta hana Nyesom Wike shiga filin wasa ba, ta bayyana cewa babu wata takardar neman izini
  • An ce ana ci gaba da gyare-gyare a filin wasan kuma ba shi da aminci ga taron jama’a, lamarin da ya sa aka hana duk wani taro
  • Gwamna Sim Fubara ya jaddada goyon bayansa ga Bola Tinubu, yana cewa gwamnatin Rivers na sahun gaba wajen tallafa wa sake zaɓensa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Port Harcourt, Rivers – Gwamnatin Rivers ta yi karin haske kan dalilin da ya sa aka hana Nyesom Wike shiga filin wasa a jihar.

An ce ministan Abuja, Wike ya zo da magoya bayansa su shiga filin wasan Yakubu Gowon domin gudanar da gangamin siyasa, inda ta ce ba ta hana su shiga ba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta ware gidajen talakawa miliyan 15 da za ta ba tallafin kudi

Fubara ya fadi dalilin hana Wike shiga filin wasa a Rivers
Gwamna Sim Fubara da Ministan Abuja, Nyesom Wike. Hoto: Nyesom Ezenwo Wike, Sir Siminalayi Fubara.
Source: Facebook

Bayanai kan hana Wike yin taro

Kwamishinan da ke kula da harkokin wasanni a jihar, Chris Green, ya bayyana hakan ne yayin rangadin duba filin wasan, cewar Premium Times.

Gangamin siyasar an yi masa lakabi da 'Renewed Hope Ambassadors' domin tallafa wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda ke neman sake tsayawa takara a zaɓen 2027.

A baya dai, Nyesom Wike ya yi barazanar amfani da ƙarfi domin shiga filin wasan a taro na gaba idan har gwamnatin Rivers ta ci gaba da hana su shiga.

Sai dai Chris Green ya ce babu wata takardar neman izini da gwamnatin Rivers ta karɓa ko ta ƙi amincewa da ita.

Kwamishinan ya ƙara da cewa baya ga rashin gabatar da buƙatar amfani da filin wasan, filin na fama manyan gyare-gyare kuma ba ya da aminci ga taron jama’a.

Ya ce:

“Idan wani na cewa an karɓi takarda kuma aka ƙi amfani da ita, to ya kawo hujja. Ni ban ga wata irin takarda ba.

Kara karanta wannan

'Na hango shi a karagar mulki': An 'fadi' gwamnan da zai gaji kujerar Tinubu

“Ana aiki a filin Yakubu Gowon a yanzu. Akwai gine-gine, manyan injuna, da muhimman kayan aiki ko’ina.”
Fubara ya magantu kan hana Wike shiga filin wasa a Rivers
Gwamna Sim Fubara yana sanya hannu a wata takarda a Rivers. Hoto: Sir Siminalayi Fubara.
Source: Facebook

Gyare-gyaren da ake yi a filin wasan

Green ya bayyana cewa gyaran da kamfanin 'Monimichelie Sports Construction' ke yi na nufin inganta filin domin ya dace da ka’idojin hukumar FIFA.

Ya ce fiye da bututu 40,000 ne aka binne a ƙarƙashin filin wasan, lamarin da ke sa saman filin ya zama mai rauni da haɗari, cewar TheCable.

Ya ƙara da cewa ba daidai ba ne wani ya nemi amfani da filin a irin wannan hali, yana mai cewa gwamnatin jihar ta tanadi wasu wurare na daban domin tarukan siyasa da na jama’a.

Gwamnatin Tinubu ta magantu kan rigimar Wike, Fubara

Kun ji cewa ana ci gaba da muhawara kan rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa dangane da siyasar jihar Rivers mai arzikin mai.

Fadar shugaban kasa ta fito ta yi tsokaci kan rikicin siyasar wanda ya sa alaka ta yi tsami tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da Nyesom Wike.

Hadimin Shugaba Tinubu ya bayyana cewa shugaban kasar yana kan matsayar da Nentawe Yilwatda ya dauka dangane da matsayin Gwamna Fubara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.