Manyan Bukatun da Kwankwaso Ya Gabatar a Shirin Hadewa da APC

Manyan Bukatun da Kwankwaso Ya Gabatar a Shirin Hadewa da APC

  • Rahotanni sun bayyana yadda tattaunawar sirri tsakanin shugabancin APC da Rabiu Musa Kwankwaso ta lalace bayan rashin cimma matsaya
  • Majiyoyi sun ce APC ta ɗauki Rabiu Kwankwaso a matsayin jigo a Kano da Arewa maso Yamma, amma abubuwa suka sauya a tsakiyar tattaunawar
  • Wasu manyan jiga-jigan APC sun nuna cewa tsarin bukatun sun tayar da hankula yayin da ake tunkarar siyasar 2027 da ma wasu batutuwan 2031

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Sababbin bayanai sun fito kan tattaunawar da aka ce an yi tsakanin jam'iyyar APC da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Rahotanni sun ce tattaunawar ta wargaje ne bayan ta ɗauki tsawon watanni ba tare da cimma matsaya ba game da wasu bautuwa ba.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso
Rabiu Kwankwaso yayin wani taron siyasa. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Rahoton This Day ya nuna cewa Rabiu Kwankwaso, wanda ake kallon tasirinsa a Kano ya shiga tattaunawar ne da manyan bukatun da suka girgiza APC.

Kara karanta wannan

Kwamishinoni 5 da suka yi murabus a gwamnatin Abba suka bi Kwankwaso

Jam'iyyar APC ta yi zawarcin Kwankwaso

A farkon tattaunawar, an ce fadar shugaban ƙasa ta ɗauki Kwankwaso a matsayin wata hanya ta shiga Kano da wasu sassan Arewa maso Yamma.

Rahoton tashar Arise News ya nuna cewa hakan ya samo asali ne daga sakamakon zaben 2023, inda jam’iyyar NNPP ta nuna ƙarfi a Kano.

Majiyoyi sun ce an yi la’akari da Kwankwaso a matsayin jigo da zai iya sauya alkiblar siyasa, musamman ganin yadda yake da magoya baya masu yawa da tsarin tafiya da aka gina tun shekarun baya.

Sai dai, yayin da tattaunawa ke tafiya, wasu manyan shugabannin APC sun fara nuna damuwa kan nauyin buƙatun da aka gabatar.

Me Kwankwaso ya nema a APC?

A cewar majiyoyi, Kwankwaso ya gabatar da buƙatar samun iko kan kusan kashi 20 cikin 100 na tsarin jam’iyyar APC a matakin ƙasa, tare da neman kujerar mataimakin shugaban ƙasa da kuma tabbacin siyasa har zuwa zangon 2031.

Kara karanta wannan

APC ta fusata da Kwankwaso ya ce Abba zai fadi zabe a 2027, ta yi martani

Biyo bayan bayanin, rahotanni sun bayyana cewa manyan jiga-jigan APC sun ce bukataun sun zama abin tayar da hankalin jam'iyyar nan take.

Sun ce buƙatar kashi 20 cikin 100 na tsarin jam’iyya abu ne da ba a taɓa tattaunawa kansa ba, kuma kujerar mataimakin shugaban ƙasa ba ta cikin abin tattaunawa.

Wani babban jami’in APC ya ce, ko shugaban ƙasa da kansa bai taɓa neman irin wannan kaso na ikon jam’iyya ba, lamarin da ya sa aka ɗauki buƙatun a matsayin masu wuce gona da iri.

Matsayar APC kan bukatun Kwankwaso

Majiyoyin sun bayyana cewa abin da ya fi ba APC mamaki shi ne yadda Kwankwaso ya fi karkata hankali kan makomar 2031, fiye da batutuwan da suka shafi 2027.

An ce hakan ya sa APC ta ɗauki tattaunawar a matsayin neman matsayi irin na mai gina jam’iyya, ba na wanda ke shirin shigowa daga waje ba.

Rabiu Kwankwaso da shugaba Bola Tinubu
Yadda Rabiu Kwankwaso ya gana da Bola Tinubu a fadar shugaban kasa. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

A sakamakon rashin cimma matsaya, an ce shugaban ƙasa ya sake duba dabarunsa, inda aka karkata hankali daga zawarcin Kwankwaso zuwa ƙarfafa dangantaka da gwamnan Kano.

Kara karanta wannan

APC, Ganduje sun yi taho mu gama da Kwankwaso kan makomar Abba a 2027

Gwamnoni za su kara shiga APC

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya bayyana cewa jam'iyyar APC za ta cigaba da karbar gwamnoni.

Ya bayyana haka ne bayan APC ta karbi gwamnonin Kano da Filato a makon nan bayan da dama sun sauya sheka a shekarar 2025.

Gwamna Sule ya ce abin mamaki ne yadda wasu ke kallon sauya sheka a matsayin butulci ko kuma yadda 'yan adawa ke damuwa da hakan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng