APC na Shirin Mamaye Najeriya, bayan Abba, Wasu Gwamnoni za Su Sauya Sheka

APC na Shirin Mamaye Najeriya, bayan Abba, Wasu Gwamnoni za Su Sauya Sheka

  • Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya ce jam’iyyar APC a buɗe take ga ƙarin gwamnonin jihohi da ke son sauya sheƙa a Najeriya
  • Abdullahi Sule ya bayyana cewa jam'iyyar APC ta karɓi gwamna na 29 mai ci a ofis, yayin da wasu ke shirin shiga jam’iyyar a nan gaba kaɗan
  • A hirar da ya yi da manema labarai, gwamnan ya ƙaryata zargin cewa yawaitar gwamnonin APC na iya jefa Najeriya cikin tsarin jam’iyya ɗaya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya ce jam’iyyar APC, ba ta hana ko ta tsoratar da kowa daga shiga cikinta, yana mai jaddada cewa ƙofofin jam’iyyar a buɗe suke ga kowane gwamna.

Jawabinsa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta muhawara a fagen siyasar Najeriya kan dalilan da ke sa jam’iyya mai mulki ke ƙara samun sababbin gwamnonin jihohi.

Kara karanta wannan

Gwamna ya sare gwiwoyin 'yan adawa, ya haska dalilan da za su sa APC lashe zabe a 2027

Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule
Gwamna Abdullahi Sule yayin taron APC a Filato. Hoto: Gov. Abdullahi A. Sule Mandate
Source: Facebook

Gwamnan ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels TV, inda ya tabo batun rade-radin sauya sheƙar gwamnonin jihohi zuwa APC.

Sauya sheka zuwa APC butulci ne?

A yayin hirar, gwamna Sule ya nuna mamakinsa kan yadda jam’iyyun adawa ke nuna fargaba duk lokacin da aka samu labarin wani gwamna ya bar su ya koma APC.

Gwamnan ya ce idan sauya sheƙar gwamna ba ta da tasiri, to bai kamata ta zama abin tayar da hankali ba ga 'yan adawa a Najeriya.

A cewarsa:

"Me ya sa jam’iyyar adawa ke shiga firgici idan wani gwamna ya tafi, alhali idan tafiyarsa ba ta nufin komai?”

Ya ƙara da cewa bai dace a ɗauki sauya sheƙar gwamna a matsayin cin amana, butulci ko barazana ga tsarin dimokiraɗiyya ba:

"Me ya sa za a ce butulci ne idan gwamna ya bar inda ya ke, me ya sa sauya sheka za ta zama matsala idan gwamnoni ba su da tasiri?"

Kara karanta wannan

APC ta fusata da Kwankwaso ya ce Abba zai fadi zabe a 2027, ta yi martani

Jam'iyyar APC ta karɓi gwamna na 29

Gwamnan Nasarawa ya bayyana cewa APC ta karɓi gwamna na 29, inda ya ce gwamnan Jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya halarci taron jam’iyyar bayan sauya sheƙarsa.

Ya kuma ce wannan na zuwa ne bayan jam’iyyar ta riga ta karɓi gwamnan Jihar Taraba, wanda ake sa ran za a yi masa tarba ta hukuma nan da wasu kwanaki.

Yadda aka yi taron APC a jihar Filato
Kashim Shettima da manyan APC yayin taron jam'iyya a Filato. Hoto: Gov. Abdullahi A. Sule Mandate
Source: Facebook

Sule ya ce wadannan gwamnoni suna taimakawa wajen tallata APC, kansu da kuma Shugaban Ƙasa, yana mai hasashen cewa wasu gwamnonin ma za su iya shiga nan gaba.

Gwamnan ya ƙi amincewa da zargin da ke cewa yawaitar gwamnonin APC na iya jefa Najeriya cikin tsarin jam’iyya ɗaya. Ya ce wannan tunani ba shi da tushe.

'APC za ta yi nasara a 2027,' Gwamna Sule

A wani labarin, mun kawo muku cewa Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya bayyana cewa jam'iyyar APC za ta yi nasara a 2027.

Kara karanta wannan

Buba Galadima ya yi tone tone kan Abba, ya fadi alherin da Buhari ya masu

Gwamnan ya fadi haka ne yayin taron APC da aka yi a jihar Filato domin karbar gwamnan jihar bayan ya sauya sheka daga PDP.

Abdullahi Sule ya kara da cewa tikitin Bola Tinubu da Kashim Shettima zai taka rawar gani a zabe mai zuwa kuma zai samu goyon bayan jama'a.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng