Gwamna Ya Sare Gwiwoyin 'Yan Adawa, Ya Haska Dalilan da Za Su Sa APC Lashe Zabe a 2027

Gwamna Ya Sare Gwiwoyin 'Yan Adawa, Ya Haska Dalilan da Za Su Sa APC Lashe Zabe a 2027

  • Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya yi tsokaci kan makomar jam'iyyar APC a babban zaben shekarar 2027
  • Abdullahi Sule ya nuna cewa 'yan adawa ba za su kai labari ba a zaben domin kuwa sun kasa daidaita matsalolin da suka yi musu katutu
  • Hakazalika, ya kuma yi watsi da zarge-zargen da jam'iyyun adawa ke yi, inda ya nuna cewa hakan ba sabon abu ba ne a fagen siyasar Najeriya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Nasarawa - Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya yi magana kan zaben shekarar 2027 da ake tunkara.

Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa jam’iyyar APC za ta ci gaba da rike mulki a zaben gama-gari na 2027.

Gwamna Abdullahi Sule ya ce APC za ta yi nasara a 2027
Gwamna Abdullahi Sule a wajen taron APC a Jos Hoto: Abdullahi A Sule Mandate
Source: Facebook

Gwamna Sule ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa a shirin 'Politics Today, na tashar Channels tv a ranar Alhamis, 29 ga watan Janairun 2026.

Kara karanta wannan

Bayan shigar Abba Kabir, APC ta shirya karbar gwamna zuwa cikinta

Meyasa APC za ta yi nasara a 2027?

Sule ya danganta wannan tabbaci da ingantuwar alamomin tattalin arziki, daidaiton manufofi, da kuma kwanciyar hankali a cikin jam’iyyar mai mulki, inda ya ce wadannan abubuwa na ba APC fifiko a kan sauran jam’iyyu.

A cewarsa, APC na tsaye kan tubalin akida tare da karfin tsari, kuma tana da ikon duba alkiblarta lokaci zuwa lokaci ta hanyar tattaunawa mai fadi da ta hada masu ruwa da tsaki da dama.

Gwamna Sule ya yi watsi da zargin 'yan adawa

Da yake mayar da martani kan suka da zarge-zargen da jam’iyyun adawa ke yawan yi, gwamnan ya ce irin wadannan abubuwa ba sababbi ba ne, illa dai suna nuna dabi’ar siyasar adawa a Najeriya.

Gwamna Sule ya yi watsi da zargin 'yan adawa
Gwamna Abdullahi Sule na jawabi a wajen taron APC a Jos Hoto: Abdullahi A Sule Mandate
Source: Facebook
“Kun taba ganin irin wannan a baya. Mun gani tun kafin matsalolin Kaduna, kafin batun Osun. Mun sha ganin hakan. Haka ake tsammanin ‘yan adawa su rika yi; suna yin abin da ya dace da matsayinsu na ‘yan adawa."

Kara karanta wannan

Bayan Abba ya shiga APC, an zakulo gwamnoni 7 da suka rage a jam'iyyun adawa

“Jam’iyyar LP da kuke magana a kanta ta gama fama da rikice-rikicenta ne kwanan nan. PDP ma har yanzu ba ta kammala warware nata matsalolin ba. Don haka sai ka ga watakila jam’iyyu daya ko biyu ne kawai suka rage."

- Gwamna Abdullahi Sule

Jam'iyyar APC ba ta da wata shakka

Ya jaddada cewa APC ba ta da wani dalilin firgita da ayyukan kananan kwamitoci ko kungiyoyin siyasa, yana mai cewa jam’iyyar mai mulki na da karfin kafa manyan kwamitoci masu fadi da za su hada daruruwan muhimman masu ruwa da tsaki daga sassan kasar nan.

Gwamnan ya kuma nuna cewa an samu ci gaba a fannin tsaro a wurare da dama a kasar, duk da cewa ya amince har yanzu akwai kalubale a wasu jihohi kadan.

Sule wanda zai bar ofis a badi ya ce kokarin da gwamnatin tarayya ke yi na ci gaba da magance matsalolin tsaro na tafiya yadda ya kamata, kuma an fara ganin sakamako.

Sanata ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa sanatan jam'iyyar ADP daga jihar Plateau, Pam Mwadkwon Dachungyang, ya sauya sheka zuwa APC mai mulki.

Kara karanta wannan

Bayan shigar Gwamna Abba APC, sakataren ADC ya ja kunnen jam'iyyar kan zaben 2027

Sanata Dachungyang ya bayyana cewa ya zaɓi komawa jam’iyyar APC ne domin samun kyakkyawan dandamali na hidimtawa al'ummar mazabarsa yadda ya kamata.

Hakazalika, ya bayyana cewa akwai rarrabuwar kai da tashe-tashen hankula a cikin gidan jam'iyyar ADP waɗanda suka kasa ƙarewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng