Bayan Shigar Gwamna Abba APC, Sakataren ADC Ya Ja Kunnen Jam'iyyar kan Zaben 2027
- Sakataren jam'iyyar ADC na kasa, Rauf Aregbesola ya aika da sakon gargadi ga APC mai mulkin Najeriya kan zaben shekarar 2027
- Tsohon gwamnan na jihar Osun ya ja kunnen APC da cewa yawan sauya shekar gwamnoni ba shi ke nuna jam'iyyar za ta yi nasara ba
- Rauf Aregbesola ya ba da misali da yadda wasu zabubbuka suka kaya a kasar nan domin tabbatar da abin da yake fada
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola, ya aika da sakon gargadi ga jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.
Rauf Aregbesola ya gargadi APC mai mulki da cewa yawan gwamnonin da ke shigowa jam’iyyar ba zai zama tabbacin samun nasararta a zaben 2027 ba.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce ya bayyana hakan ne yayin a yake magana a wajen kaddamar da wani littafi mai suna 'The Loyalist'da sakataren yaɗa labarai na kasa na jam’iyyar ADC ya rubuta.
Wane gargadi sakataren ADC ya yi wa APC?
Aregbesola ya ce idan aka duba abin da ya faru a zabubbukan baya, ikirarin da ake yi cewa ta riga ta tabbata cewa APC za ta yi nasara a 2027 ba gaskiya ba ne.
Tsohon gwamnan Osun ya ce mutane ne ke lashe zaɓe, ba gwamnonin da ke sauya sheƙa ba. Ya kara da cewa tara gwamnonin adawa zuwa APC ba zai tabbatar wa jam’iyyar nasara a zaben shugaban kasa na 2027 ba.
Sakataren na jam'iyyar ADC na kasa ya jaddada cewa biyayya ga wata manufa ta fi biyayya ga mutum ɗaya, rahoton jaridar Independent ya tabbatar da hakan.
Aregbesola ya ba misalai
Aregbesola ya tuna da abin da ya faru a shiyyoyin Kudu maso Gabas da Kudu maso Yamma a zaben da ya gabata, inda ya ce hakan hujja ce da ke nuna cewa gwamnonin jihohi ba sa tabbatar da nasarar zaɓe.
“Akwai wani zance da ke yawo wanda ke tayar da hankali, domin mu da muke masu ra’ayin dimokiraɗiyya, ana cewa tunda gwamnonin jihohi 30 suna goyon bayan wata jam’iyya, to lallai wannan jam’iyyar za ta ci zaɓe."
“Kididdigar zabukan baya-bayan nan a Najeriya ba ta goyi bayan wannan ra’ayi ba. Ina so mambobi su sani cewa sakamakon zaben da ya gabata a wannan kasa bai goyi bayan wannan tunani ba.”
“Zan yi amfani da sakamakon zabe daga shiyyoyi biyu, Kudu maso Yamma da Kudu maso Gabas domin karyata hujjar cewa gwamnonin jihohi ne ke tabbatar wa jam’iyyun siyasa nasarar zaɓe."
- Rauf Aregbesola

Source: Facebook
Ya ce duk da yawan gwamnonin APC a shiyyar Kudu maso Yamma a 2023, jam’iyyar ta samu kashi 55 cikin 100 kacal na kuri’un da aka kaɗa.
Gwamma Abba ya koma APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.
Gwamna Abba Kabir ya sanar da shigarsa APC ne a wani gagarumin taro da aka shirya a babban dakin taron da ke gidan gwamnatin jihar Kano.
Abba ya jaddada cewa dalilin komawarsa APC shi ne domin samar da kyakkyawar dangantaka da hadin kai tsakanin Kano da gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Asali: Legit.ng

