Bayan Abba, Kashim Shettima Zai Taso daga Abuja domin Karbar Gwamna zuwa APC
- Sanata Kashim Shettima zai kai ziyara jihar Filato domin karbar Gwamna Caleb Mutfwang zuwa jam'iyyar APC a hukumance
- An shirya bikin karbar gwamnan a yau Talata, 27 ga watan Janairu, 2026, makonni bayan ya sanar da ficewarsa daga PDP zuwa APC
- Kwamitin shirya bikin sauya shekar ya bayyana cewa ana sa ran manyan baki daga sassa daban-daban na kasar nan za su halarta
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Plateau, Nigeria - Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya, Sanata Kashim Shettima, zai karbi Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang, zuwa cikin jam’iyyar APC a hukumance yau Talata.
Idan za a iya tunawa, gwamnan, wanda aka zaba a karkashin inuwar PDP a 2023, ya sauya sheka ne zuwa APC a farkon wannan shekarar tare da dukkan mambobin majalisar zartarwarsa na Filato.

Kara karanta wannan
Bayan gama tarbar Abba a APC, Barau ya tabo batun burinsa na takarar gwamna a 2027

Source: Twitter
Tribune Nigeria ta tattaro cewa shugaban kwamitin shirya taron sauya shekar gwamnan Filato, Hon. Idris Maje ne ya bayyana haka da yake hira da manema labarai a Jos.
Manyan bakin da za su dura jihar Filato
Idris Maje, tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai, ya ce taron zai samu halartar manyan jiga-jigan APC kamar Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da Shugaban Majalisar Wakilai, Rt. Hon Tajudeen Abbas.
Sauran manyan bakin sun hada da gwamnonin APC, shugabannin jam'iyya na matakin kasa, 'yan Majalisar tarayya, ministoci, sarakuna da sauran manyan baki daga sassa daban-daban.
A cewar Hon. Maje, wannan sauya sheka na nuna wani gagarumin sauyi na tarihi a fagen siyasar jihar Filato, wanda zai iya kara fito da hadin kai da kuma shugabanci na bai-daya.
Amfanin komawar Gwamna Mutfwang APC
Ya kara da cewa wannan dabarar da gwamnan ya dauka za ta samar da wani babban dandamali na siyasa wanda zai dauki bukatun jama'a sama da na jam'iyya tare da dinke barakar fuskar siyasa da kabilanci.
"Hakan zai sa jihar Filato ta samu damar jawo manyan ayyukan ci gaba kamar inganta hanyoyi, samar da ayyukan yi, karfafa tsaro, da kyautata rayuwar jama’a daga gwamnatin tarayya," In ji Maje.

Source: Facebook
Idris Maje ya kammala da cewa, a cikin shekaru biyu da rabi na mulkin Gwamna Mutfwang, jihar Filato ta samu shugabanci mai cike da gaskiya, kaskantar da kai, da kuma jajircewa wajen yi wa al'umma hidima.
Ya ce wannan sauya sheka da gwamnan ya yi zuwa APC, zai kara jawo karin ayyukan ci gaba domin amfanin al'ummar jihar Filato, kamar yadda This Day ta ruwaito.
Gwamna Abba ya koma APC a hukumance
A wani rahoton, kun ji cewa bayan tsawon lokaci ana dambarwa a siyasar jihar Kano, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya koma jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya a hukumance.
Gwamna Abba, wanda ake yi wa lakabi da Abba Gida-gida, ya sanar da hakan ne a wani biki da aka shirya a babban dakin taron da ke gidan gwamnatin jihar Kano.
Abba ya jaddada cewa dalilin komawarsa APC shi ne domin samar da kyakkyawar dangantaka da hadin kai tsakanin Kano da gwamnatin tarayya karkashin Shugaba Tinubu.
Asali: Legit.ng
