Shugaban Hukumar Alhazai Ya Hakura da Gwamnatin Abba, Ya Yi Murabus
- Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Laminu Rabiu, ya ajiye aikinsa nan take bayan sauya shekar Gwamna
- Alhaji Laminu Rabi'u ya danganta matakin da sauye-sauyen yanayin siyasa da kuma jajircewarsa ga tafiyar Kwankwasiyya
- Ya gode wa Gwamna Abba Kabir Yusuf da ma’aikatan hukumar bisa hadin kai da damar da aka ba shi a lokacin da ya ke shugabanci
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Laminu Rabiu, ya sanar da murabus daga kujerarsa.
Wasikar, wacce aka mika wa Gwamna Abba Kabir Yusuf, ta nuna cewa Laminu Rabiu ya dauki wannan mataki ne bayan zurfin tunani da nazari kan halin da siyasa ke ciki a halin yanzu.

Source: Facebook
Sanarwar murabus din na kunshe a cikin wata wasika da Alhaji Laminu Bichi ya fitar, wacce Isa Suleiman Ibrahim ya wallafa a shafin Facebook.
Shugaban hukumar alhazan Kano ya yi murabus
A cewarsa sanarwar, sauye-sauyen da ke faruwa a cikin jam’iyya da yanayin tafiyar siyasa sun tilasta masa sake daidaita abubuwan da yake mayar da hankali a kai.
Ya ce murabus din nasa ba ya nufin ja da baya daga hidimar jama’a, illa dai wata dabara ce ta bai wa kansa damar bada cikakken goyon baya ga akidar da ya yi imani da ita.
Alhaji Laminu Rabiu ya bayyana jajircewarsa ga tafiyar Kwankwasiyya da jagoranta, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Source: Facebook
Ya bayyana cewa:
“A matsayina na cikakken dan tafiyar Kwankwasiyya, ina nan daram kan biyayya ga jagoranmu tare da jajircewa ga manufofi da muradun da ke tafiyar da wannan tsari na siyasa.”
Laminu Rabiu ya gode wa gwamnatin Kano
Tsohon Shugaban ya kara da cewa ajiye mukamin zai taimaka wajen tabbatar da hadin kai a cikin jam’iyya tare da ba shi damar tallafa wa ci gaban Kwankwasiyya.
Alhaji Laminu ya gode wa Gwamna Abba Kabir Yusuf, inda ya bayyana amincewar da aka ba shi a matsayin babbar kima da daraja.
Ya ce:
"Na dauki lokacin da na yi a matsayin shugaba a matsayin abin alfahari da gata."
Ya kara da cewa yana jin dadin irin ci gaban da aka samu wajen inganta walwalar alhazai da kuma karfafa yadda hukumar ke gudanar da ayyukanta.
Matasan Kwankwasiyya na iya bin Gwamna Abba
A baya, mun wallafa cewa wasu kungiyoyin matasan Kwankwasiyya a Jihar Kano sun bayyana cewa a shirye suke su bi Gwamna Abba Kabir Yusuf bayan ficewarsa daga jam’iyyar NNPP.
Matasan da suka ce suna da ra'ayin kansu, sun nanata cewa hakan zai ta’allaka ne da cika wasu muhimman sharudda, musamman na tafiya da matasa a cikin harkar.
Matasan sun ce matsayinsu ya samo asali ne daga abin da suka bayyana a matsayin wariya da kuma rashin saka wa matasan da suka dade suna aiki da sadaukarwa a tafiyar Kwankwasiyya.
Asali: Legit.ng


