Abin da Kwankwaso Ya Fadawa Magoya Baya bayan Ficewar Abba daga NNPP
- Jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya karɓi baƙuncin magoya baya daga al’ummar Nasarawa a Kano
- Ziyarar na zuwa ne a lokacin da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya sauya sheka daga jam'iyyar NNPP kuma ake sa ran zai koma APC
- Sanata Kwankwaso ya jaddada aniyarsa ta ci gaba da kare akidar Kwankwasiyya domin cigaban jama’a a Kano da Arewacin Najeriya
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Jagoran Kwankwasiyya kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana godiyarsa ga al’ummar Karamar Hukumar Nasarawa bisa ziyarar goyon bayan da suka kai masa.
Ɗaruruwan magoya baya ne suka kai masa ziyara gidansa da ke Kano, yana mai bayyana hakan a matsayin alamar jajircewa, biyayya da kishin al’umma.

Source: Facebook
A sakon da ya wallafa a shafin Facebook, Kwankwaso ya tabbatar da cewa ya karɓi baƙuncin ne da yammacin wannan rana, 25 ga watan Janairu, 2026.
Magoya baya sun ziyarci Kwankwaso
Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bayyana cewa ziyarar ta zo a wani lokaci mai muhimmanci da ake fuskantar ƙalubale da jarabawa a harkokin siyasa.
Ya jaddada cewa tsayin dakan da mutanen Nasarawa suka nuna ya ƙara masa ƙwarin gwiwa wajen ci gaba da fafutukar kare muradun talakawa da inganta rayuwar al’umma baki ɗaya.
A yayin ganawar, Kwankwaso ya ce yana matuƙar jin daɗin yadda al’ummar Nasarawa suka nuna jarumta da ƙuduri duk da wasu matsaloli da suka taso kwanan nan.
Kwankwaso ya ce:
“Na sake jaddada matuƙar godiyata bisa jajircewa da ƙudurinku. Duk da jarabawar da ta gwada imaninku da juriyarku, kun zaɓi tsayawa tare da mu domin amfanin jama’a."
Ya ƙara da cewa irin wannan goyon baya na nuna cewa akidar Kwankwasiyya ta samo tushe mai ƙarfi a zukatan jama’a.
Kwankwaso ya yaba wa magoya baya
Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya kuma bayyana cewa irin wannan haɗin kai da biyayya na daga cikin ginshiƙan da suka sa darikar Kwankwasiyya ke ci gaba da samun karɓuwa a faɗin Kano da ma Arewa gaba ɗaya.
Kwankwaso ya jaddada cewa shi da magoya bayansa za su ci gaba da tsayawa tsayin daka wajen kare da bunƙasa akidar Kwankwasiyya, wadda ta ta’allaka ne kan adalci, ilimi, walwala da cigaban talakawa.

Source: Facebook
Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce akidar ba ta ginu kan son zuciya ko amfanin kai ba, illa burin ganin al’umma sun samu ingantacciyar rayuwa.
Ya gode wa al’ummar Nasarawa bisa nuna amana da haɗin kai, yana mai cewa tafiyar tana ci gaba kuma nasara za ta tabbata da yardar Allah da kuma goyon bayan jama’a.
Ya yi kira ga magoya baya da su ci gaba da kasancewa masu haƙuri, haɗin kai da zaman lumana, yana mai jaddada cewa makomar Kano da Arewa za ta fi kyau muddin aka ci gaba da tsayawa kan gaskiya da muradun jama’a.
Abba ya rike tsarin Kwankwasiyya
A baya, mun ruwaito cewa gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa ficewar Gwamna Abba Kabir Yusuf daga jam’iyyar NNPP ba ya nufin an yi watsi da tsarin Kwankwasiyya.
Wannan karin haske ya zo ne awanni kaɗan bayan sanarwar ficewar gwamnan daga NNPP, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce a fagen siyasar jihar Kano da kasa baki daya.
A wata sanarwa da Daraktan Janar na Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a a Gidan Gwamnatin Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, ya ce har yanzu ana tare da NNPP.
Asali: Legit.ng


