Kurunkus: Gwamna Abba Ya Shirya Tsaf, Ya Bayyana Ranar Komawa Jam'iyyar APC
- Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya shirya tsaf domin komawa jam'iyyar APC a hukumance ranar Litinin, 26 ga watan Janairu, 2026
- Mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya ce Abba zai karbi katin zama cikakken dan APC a mazabarsa
- Wannan na zuwa ne kwanaki biyu bayan Abba Gida-Gida ya bar NNPP tare da yan Majalisar dokokin Kano da na tarayya
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Bayan tsawon lokaci ana rade-radi, gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yuauf ya kammala duk wasu shirye-shirye kuma ya tabbatar da zai koma jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.
Wannan na zuwa ne bayan Gwamna Abba ya fice daga jam'iyyar NNPP a ranar Juma'a da ta gabata, 23 ga watan Janairu, 2026, lamarin da ya kara zafafa dambarwar siyasar Kano.

Kara karanta wannan
Zance ya kare: 'Yan Majalisar Kano 22 sun bayyana matsayarsu kan tafiyar Gwamna Abba

Source: Facebook
Yaushe Gwamna Abba zai shiga APC?
Mai magana da yawun gwamnan jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya sanar a shafinsa na Facebook cewa Gwamna Abba Kabir zai koma jam'iyyar APC ranar Litinin mai zuwa.
Sanusi Bature ya ce Gwamna Abba ya shirya tsaf domin komawa jam’iyyar APC a ranar Litinin, 26 ga Janairu, 2026, biyo bayan ficewa daga NNPP a ranar Juma’ar da ta gabata.
Tarihin zaman Abba a jam'iyyar APC
Sanarwar ta tunatar da jama'a cewa Abba ya fara shiga APC ne a 2014, inda ya lashe zaben fidda gwani na takarar sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya, matsayin da daga baya ya janye wa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
An bayyana cewa bayan shekaru na gwagwarmayar siyasa a fage daban-daban, ciki har da zamansa na baya-bayan nan a NNPP, a yanzu Gwamna Abba zai sake komawa APC.
Kalakin gwmanan ya ce yanayin tafiyar da mulki na yanzu, bukatar hadin kan kasa, da ci gaba sun sanya ya zama dole Abba Gida-Gida ya koma APC, wadda ya bayyana a matsayin gida kuma dandali mai nagarta.
Dalilan Gwamna Abba na sauya sheka
Gwamna Abba ya bayyana cewa komawa APC za ta kara karfafa hadin gwiwa tsakanin Kano da Gwamnatin Tarayya, sannan ta hanzarta ci gaban ayyukan ababen more rayuwa, inganta tsaro, da kyautata rayuwar al’umma a fadin jihar Kano.
Ya kara da cewa wannan shawara za ta karfafa kwanciyar hankali ta siyasa da kuma hadin kai a jihar Kano, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Source: Facebook
A ranar Litinin, 26 ga Janairu, 2026, gwamnan zai yi rajista a hukumance a matsayin dan APC a Kano, tare da mambobin majalisar dokokin jihar 22, da yan majalisar wakilai ta tarayya guda takwas.
Haka zalika, ana sa ran shugabannin kananan hukumomi guda 44 za su marawa gwamnan baya zuwa APC.
Haka kuma ana sa ran zai kaddamar da shirin rajistar mambobin jam’iyyar APC ta yanar gizo a hukumance.
Gwamnatin Kano ta yi gargadi kan Kwankwaso
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta ce ba za ta lamunci taba mutuncin jagoran NNPP, Rabiu Kwankwaso ba.
Mai magana da yawun gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya gargadi mai cin zarafi ko zagin Kwankwaso, yana mai cewa za a dauki tsattsauran mataki a kansu.
Ya bayyana Kwankwaso a matsayin jagoran siyasa wanda dole ne a mutunta matsayinsa a siyasar Kano, ba tare da la’akari da sauye-sauyen siyasar da ake ciki ba.
Asali: Legit.ng

