Lamura na Ƙara Dagulewa Abba Kabir, Kwamishina a Gwamnatinsa Ya Yi Murabus

Lamura na Ƙara Dagulewa Abba Kabir, Kwamishina a Gwamnatinsa Ya Yi Murabus

  • Kwamishinan Kimiyya da Fasaha na Kano, Yusuf Ibrahim Kofarmata, ya yi murabus nan take a gwamnatin Abba Kabir
  • Kofarmata ya ce yanayin siyasar yanzu na iya kawo shakku kan ‘yancin aikinsa da gaskiya, lamarin da bai dace da ka’idojin mukaminsa ba
  • Ya gode wa gwamnatin Kano bisa damar aiki, yana fatan murabus dinsa zai taimaka wajen kare martabar ofishin da amincewar jama’a

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Kwamishinan Kimiyya, Fasaha da Kirkire-kirkire na Jihar Kano, Yusuf Ibrahim Kofarmata, ya yi murabus daga mukaminsa.

Wannan na zuwa ne sakamakon rikicin siyasa da ya taso bayan Abba Kabir ya bar jam'iyyar NNPP wanda ake hasashen zai koma APC.

Kwamishinan Abba Kabir ya yi murabus
Gwamna Abba Kabir na jihar Kano. Hoto: Abba Kabir Yusuf.
Source: Facebook

Dalilin murabus din Kwamishina a Kano

Kofarmata ya sanar da murabus dinsa ne ta wata takarda da ya aikawa hukumomin da suka dace, yana nuna damuwa kan halin siyasar jihar, cewar Daily Nigerian.

Kara karanta wannan

Hadimin Gwamna ya ajiye siyasar jam'iyya bayan Abba ya bar NNPP

Ya ce yanayin siyasar da ake ciki na iya lalata ‘yanci da adalcin da ake bukata daga mukamin Kwamishinan Jiha.

A cewarsa, karuwar matsin lamba, biyayya da nuna bangaranci na iya haifar da shakku ko gaskiyar rashin adalci a hukuncinsa.

Ya bayyana cewa hakan ya sabawa ka’idojin ɗabi’a da mutuncin da ya kamata Kwamishinan Jiha ya kasance da su a kowane lokaci.

Kofarmata ya jaddada cewa mutuncin mukamin kwamishina na dogara ne kan ikon aiki ba tare da tsoma baki ko matsin lambar jam’iyya ba.

Ya ce ci gaba da kasancewarsa a ofis a irin wannan yanayi na iya rage amincewar jama’a ga hukumomin gwamnati.

Saboda haka, ya yanke shawarar janyewa domin kare sahihancin ofishin da kuma nuna jajircewarsa ga gaskiya a hidimar jama’a.

Abba Kabir ya sake rasa kwamishina a Kano
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano. Hoto: Abba Kabir Yusuf.
Source: Facebook

Kalaman da kwamishinan ya yi ga Abba

Tsohon kwamishinan ya gode wa Gwamnatin Jihar Kano bisa damar da aka ba shi ya yi aiki a ma’aikatu daban-daban.

Ya ce a lokacin aikinsa ya samu damar bayar da gudunmawa ga sauye-sauyen manufofi da ci gaban jihar Kano.

Kara karanta wannan

Rarara ya saki sabuwar waka ga Abba ana shirin dafe shi a APC bayan barin NNPP

A cikin takardar, ya ce yana godiya ga amincewar da aka nuna masa tare da fatan murabus dinsa zai taimaka wa ofishin ya yi aiki cikin ‘yanci.

Ya bukaci a karɓi murabus dinsa a matsayin sanarwa a hukumance ta ficewarsa daga Majalisar Zartarwa ta Jihar Kano.

Murabus din Kofarmata na zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar sauye-sauyen siyasa da rikice-rikice a jihar Kano.

Wadannan rikice-rikice sun jawo muhawara daga jama’a kan harkokin mulki, adalci da ‘yancin hukumomin gwamnati a jihar, cewar Daily Post.

Kwamishina a Kano ya bi layin Kwankwaso

Kun ji cewa kwamishinan gwamnatin Kano, Adamu Aliyu Kibiya ya kama layinsa a siyasar jihar bayan ficewar Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Kibiya ya ce har yanzu yana tsaye kan akidu da manufofin jam'iyyar NNPP mai adawa a kasa da Kwankwaso ya assasa domin ci gaba.

Ficewar gwamnan ta haifar da sabon tsari a siyasar Kano, inda ‘yan jam’iyya da dama ke bayyana inda suka dosa a halin yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.