Yayin da Ake Hasashen Sauya Shettima, an Ce Tinubu na Shirin Sauya Shi da Gwamna
- Limamin addinin Kirista, Elijah Ayodele ya yi hasashen cewa Shugaba Bola Tinubu na shirin sauya Kashim Shettima kafin zaben 2027
- Malamin ya yi gargadin barazanar rikici a APC idan har shugaban ya yi yunkurin sauya Shettima daga mukaminsa
- Ayodele ya ce cire Shettima cikin rikici zai iya janyo masa aiki da muradun APC, yana mai cewa gwamna ne ake shirin dauka a madadinsa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Gabanin zaben shekarar 2027 ke kara karatowa, Fasto Elijah Ayodele ya yi hasashen sauya Kashim Shettima a matsayin mataimakin shugaban kasa.
Ayodele ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu na shirin sauya Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima kafin zaben da ke tafe.

Source: Facebook
Gargadin da Fasto ya yi ga Tinubu
Hakan na cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Lahadi, 25 ga Janairu, 2026 da muke ciki da hadiminsa ya yada ga Legit.ng.
Ayodele ya ce ya taba gargadin Tinubu kan amfani da tikitin Musulmi da Musulmi da ya ce zai zama rigima da jam'iyya mai mulkin Najeriya.
Limamin ya bayyana cewa rashin bin wannan gargadi na iya haifar da sauke Shettima daga mukaminsa cikin gaggawa kafin babban zabe.
Ayodele ya ce ana tunanin daukar wani gwamna mai ci a matsayin sabon mataimakin shugaban kasa idan aka sauke Shettima.
Ya gargadi cewa idan aka cire Shettima cikin rikici, hakan zai sa ya yi aiki da muradun da ka iya cutar da jam’iyyar APC.
Limamin ya kuma shawarci Tinubu da kada ya zabi wani daga cikin gwamnoni da suka sauya sheka zuwa APC, musamman daga Arewa.
Ya ce:
"Idan aka zaɓi ɗaya daga cikin gwamnonin da suka tsallaka (zuwa APC) daga Arewa, hakan zai haifar da tashin hankali a Arewa.”

Source: Twitter
Matsalar da sauya Shettima zai jawo
A cewarsa, daukar irin wadannan gwamnoni daga Arewa zai iya haddasa tashin hankali da fusata jama’a a yankin wanda ba za a iya dakile wa cikin ruwan sanyi ba.
Ayodele ya kara da cewa duk da ana ganin Tinubu na kokari, akwai “makiya masu cin amana” da ke aiki a boye kan gwamnatinsa wanda hakan babbar matsala ce gare shi.
Ya zargi wasu makusantan shugaban kasa da toshe hanyoyin masu son taimakawa, yana cewa kudi ba zai iya warware matsalar ba, cewar Daily Post.
Kan tsaro kuwa, Ayodele ya yi zargin cewa Amurka na da tasiri a harkar tsaron Najeriya, tana sanin inda za ta raunana gwamnati.
An gargadi Tinubu kan 'shirin' sauya Shettima
Kun ji cewa wata ƙungiyar APC ta Arewa ta Tsakiya ta gargaɗi jam’iyya da kada ta cire Kashim Shettima daga tikitin Bola Tinubu a zaɓen 2027 da ke tafe.
Ta ce cire Shettima zai zama babban kuskuren siyasa da zai iya lalata shirin sake zaɓen Shugaba Tinubu idan ya nemi ya zarce.
Masoyan na APC a Arewa ta Tsakiya sun jaddada cewa sauya tikitin Musulmi-Musulmi zai ƙarfafa adawa maimakon kawo nasara an zaben da ake tunkara.
Asali: Legit.ng

