Hadimin Gwamna Ya Ajiye Siyasar Jam'iyya bayan Abba Ya Bar NNPP
- Hadimin Gwamnan Kano, Muktar Abdullahi Asad ya sanar da janyewa daga harkokin jam’iyya bayan ficewar Gwamna Abba Kabir Yusuf daga NNPP
- Muktar Abdullahi Asad ya jaddada cikakken goyon bayansa ga Gwamnan Kano a duk jam’iyyar da zai shiga a yayin da siyasar Kano ta dauki zafi
- Hadimin Gwamnan ya bayyana irin siyasar da zai ci gaba da yi daga yanzu bayan ya ajiye maganar siyasar kowace jam'iyya a yanzu
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Babban mai dauko rahoto a Hukumar Lantarki ta Karkara (REB), Muktar Abdullahi Asad, ya sanar da janyewarsa daga harkokin siyasar jam’iyya.
Ya bayyana cewa wannan mataki ya biyo bayan ficewar Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, daga jam’iyyar NNPP yayin da ake jiran sabuwar tafiyar siyasa da zai shiga.

Source: Twitter
Muktar Asad ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya bayyana salon siyasar da zai shiga a yanzu.
Hadimin Gwamna ya bi sawun Abba
A cewar sanarwar, daga yanzu zai karkata hankalinsa ne kan siyasar mutunci, nagartar hali da gaskiya 'dan siyasa, maimakon tsunduma cikin fafutukar jam’iyya.
A cewarsa, yanayin siyasar da ake ciki ya sa ya ga dacewar daukar wannan mataki domin ya samu damar bada gudunmawa ta hanyoyin da za su fi amfani ga al’umma.
Ya jaddada cewa janyewarsa daga siyasar jam’iyya ba yana nufin ya rabu da jagoranci ko hangen nesan Gwamna Abba Kabir Yusuf ba.
A maimakon haka, ya ce har yanzu yana nan daram wajen mara wa Gwamnan Kano baya, tare da goyon bayansa a duk jam’iyyar siyasa da ya zaba ya shiga a nan gaba.
Hadimin Abba ya fadi matsayarsa a siyasa
A cikin sanarwar, Muktar Abdullahi Asad ya bayyana sabon matsayinsa kan siyasa, inda ya ce daga yanzu shi da masu ra’ayinsa za su rika goyon bayan duk wani dan takara da suka ga ya cancanta.

Source: Facebook
Ya kara da cewa za su mayar da hankali a kan dan siyasa mai kwarewa da amana, ba tare da la’akari da jam’iyyar da yake ciki ba.
Ya ce abin da ya fi muhimmanci a wajensu shi ne ingantaccen shugabanci da zai amfanar da al’umma, ba tambarin jam’iyya ko sunan kungiya ba.
A kalamansa:
“Abin da muke nema shi ne shugabanci nagari, mai hangen nesa da tsoron Allah. Idan dan takara yana da wadannan siffofi, to jam’iyyar da yake ciki ba za ta zama shinge ba a gare mu."
Ya kara da cewa Najeriya na bukatar shugabanni masu mutunci da kishin kasa, wadanda za su fifita muradun jama’a a kan na kansu.
A cewarsa, sauyin da yake faruwa a siyasar Kano da kasa baki daya na bukatar mutane su sake duba matsayinsu, su kuma zabi abin da ya fi amfani ga cigaban al’umma.
Matasan Kwankwasiyya na shirin bin Abba
A baya, mun wallafa cewa kungiyoyin matasan Kwankwasiyya a Kano sun bayyana matsayarsu kan wannan sabon yanayin siyasa bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bar NNPP.
Da yake jawabi a wani taron tattaunawa da matasa, wakilan kungiyoyin sun jaddada cewa ba su da wata matsala ta kai tsaye da Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Aminu Abdullahi, wanda aka fi sani da Alhaji Warkal, ya ce matasan Kwankwasiyya a shirye suke su yi tafiya da gwamnan, muddin gwamnatinsa za ta biya bukatunsu.
Asali: Legit.ng


