Rarara Ya Saki Sabuwar Waka ga Abba Ana Shirin Dafe Shi a APC bayan Barin NNPP

Rarara Ya Saki Sabuwar Waka ga Abba Ana Shirin Dafe Shi a APC bayan Barin NNPP

  • Siyasar Kano na kara rikicewa bayan murabus din Gwamna Abba Kabir Yusuf daga NNPP, inda mawakin siyasa ya saki waka yana yabonsa
  • Dauda Kahutu Rarara, wanda ya saba sukar Abba Kabir da Kwankwasiyya, ya saki bangaren waka yana hasashen gwamnan zai koma APC
  • Sabuwar wakar ta jawo ce-ce-ku-ce, inda wasu ke yabawa Rarara yayin da wasu ke sukar sauyin matsayinsa a siyasa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Siyasar Kano na ci gaba da sauya salo tun bayan murabus din Gwamna Abba Kabir Yusuf daga jam'iyyar NNPP.

Mawakin siyasa a Arewacin Najeriya ya saki wata waka ga Gwamna Abba Kabir yayin da ake hasashen zai shiga APC mai mulkin Najeriya.

Rarara ya saki sabuwar waka ga Abba Kabir
Mawaki Dauda Kahutu Rarara a bidiyo yayin sakin waka ga Abba Kabir. Dauda Kahutu Rarara, Sanusi Bature D-Tofa.
Source: Facebook

Fitaccen mawakin ya tabbatar da haka a shafinsa na Facebook inda ya saki wani bangare na wakar mai tsawon mintuna kusan uku.

Kara karanta wannan

Matasan Kwankwasiyya sun shirya bin gwamna Abba, sun saka sharadi

Yadda Rarara ya rika sukar Abba a baya

Rarara dai na daga cikin masu sukar gwamnatin Abba Kabir da kuma tafiyar Kwankwasiyya saboda bambancin jam'iyya da suke da shi.

Hakan bai rasa nasaba da layin tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje da ya dauka wanda shi ne tsohon shugaban APC a Najeriya.

Mawakin yana yawan sukar jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Kwankwaso a mafi yawan wakokinsa duk da cewa sun taba tafiya tare a wa'adi na biyu na mulkin Kwankwaso lokacin yana gwamna.

An samu mabambantan ra'ayoyi kan sabuwar wakar Rarara ga Abba Kabir
Mawakin siyasa a Najeriya, Dauda Kahutu Rarara. Hoto: Dauda Kahutu Rarara.
Source: Facebook

Wakar Rarara: Baitin da ya fi daukar hankali

Ko a cikin wannan sabuwar wakar da ya sake, Rarara ya yi gugar zana yayin da yake yabon Abba Kabir da ake hasashen APC zai shiga.

Murabus din Abba Kabir ya sake rikita siyasar Kano inda aka fara kama layi inda wasu ke hadewa da gwamna wasu ko ke bin Kwankwaso.

Baitin da ya fi daukar hankali shi ne wanda yake cewa 'Kanawa na fadin hudu sau hudu ba wani fargaba, kai ne gwamna idan ma akwai wani ba mu san shi ba'.

Kara karanta wannan

'Abin da na fada wa Abba Kabir game da butulce wa Kwankwaso - Sanatan NNPP'

Martanin mutane game da wakar Rarara ga Abba

Wannan wakar ta jawo martanin dubban mutane da dama ke bayyana ra'ayoyinsu game da mawakin APC da ya yi waka ga Gwamna Abba.

Wasu daga cikin masoyan Abba na yabawa Rarara kan wakar da ya sake yayin da wasu ko ke ganin Magudu zai ji bacin rai saboda wakar da aka sake.

Sai da wasu ko bayyana wahalar da ke cikin siyasa suke yi duba da yadda ya zagi Abba a baya amma yanzu sun hade a wuri guda sabosa siyasa.

Akwai kuma wadanda ke sukar mawakin da cewa kwata-kwata ba talaka ba ne a gabansa duk inda zai cika aljihunsa shi ne mafita a gare shi.

Tijjani Gandu ya saki wakar Kwankwaso a Kano

Mun ba ku labarin cewa mawakin Kwankwasiyya, Tijjani Gandu, ya fitar da gajeriyar waka da ke nuna goyon bayansa ga Rabiu Musa Kwankwaso.

Wakar ta biyo bayan sanarwar ficewar Abba Kabir Yusuf daga jam’iyyar NNPP, lamarin da ya sake tayar da muhawara a siyasar Kano.

Dubban mutane sun mayar da martani kan wakar, inda magoya baya suka bayyana ra’ayoyi masu nuna goyon baya da addu’o’i ga mawakin tafiyar Kwankwasiyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.