2027: APC Ta Tabo Batun Ba Gwamna Abba Tikitin Takara Kai Tsaye bayan Barin NNPP
- Shugaban APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas, ya yi tsokaci kan shirin Gwamna Abba Kabir Yusuf na shigowa jam'iyyarsu
- Abdullahi Abbas ya bayyana cewa za su yi maraba da Gwamna Abba Kabir Yusuf idan har ya yanke shawarar shigowa jam'iyyar APC
- Hakazalika ya warware zare da abawa kan batun ba Gwamna Abba tikitin takara kai tsaye a zaben 2027 idan ya shigo APC
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Shugaban jam'iyyar APC na jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas, ya yi magana kan ficewar Gwamna Abba Kabir Yusuf daga NNPP.
Abdullahi Abbas wanda ake yi wa lakabi da 'Dan Sarki ya bayyana cewa idan gwamnan ya shigo jam'iyyar APC a Kano, za su yi maraba da shi.

Source: Facebook
Shugaban na APC a Kano ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da ya yi da jaridar Daily Trust.
Gwamna Abba ya fice daga jam'iyyar NNPP
Idan ba a manta ba Legit Hausa ta ruwaito cewa a ranar Juma'a, 23 ga watan Janairun 2026, Gwamna Abba Kabir ya yi murabus daga jam'iyyar NNPP.
Gwamnan ya danganta matakin da ya dauka na ficewa daga NNPP, kan rikice-rikicen da suka addabi jam'iyyar.
A halin yanzu akwai sabanin cikin gida a jam'iyyar hamayya ta NNPP wanda ta bangare zuwa tsagin masu kayan marmari da mai alambar littafi
Me shugaban APC ya ce kan Gwamna Abba?
A yayin hirar, Abdullahi Abbas ya bayyana cewa a shirye suke su yi maraba da gwamnan idan ya shigo jam'iyyar APC.
“Muna maraba da shi hannu bibbiyu a jam’iyyarmu, domin a siyasa babu wani ɗan siyasa mai tunani nagari da zai ki karin karfi. Kamar yadda kuka sani, siyasa batu ne na adadi.”
“Saboda haka, sauya sheƙa zuwa jam’iyyarku na nufin kara yawan ku, kuma hakan kai tsaye na kara mana damar samun nasara a zaɓe.”
“Mun sha bayyana matsayarmu a lokuta da dama cewa za mu karɓi duk wanda ya ga kyawun jam’iyyarmu kuma yake son shigowa cikinta.”
- Abdullahi Abbas
Batun ba da tikitin takara kai tsaye a APC
Dangane da batun tikitin takara kai tsaye kuwa, shugaban na APC ya bayyana cewa wannan ba wata matsala ba ce a yanzu.
“Wannan ba matsala ba ce a yanzu. Batu ne da za a tattauna bayan an kammala dukkan matakan sauya sheka, kuma duk wanda ke shigowa ya kammala tsarinsa yadda ya dace.”
“Dangane da Gwamna Abba Kabir Yusuf, kamar yadda ku ka sani ba shi kaɗai ke shigowa ba. Akwai zababbun shugabannin kananan hukumomi, kansiloli da sauran masu rike da mukaman siyasa da za su shigo jam’iyyarmu tare da shi.”
“Saboda haka, sai an kammala komai sannan mu zauna mu tsara dabarar da kowa zai amfana da ita. Batun ya wuce kawai yin takara; maganar ita ce yadda jam’iyyar APC za ta yi nasara a zaɓen gama gari na 2027.”
“A takaice, batun zama ne mu tattauna mu cimma matsaya, kuma babu abin da ya gagara a nan.”
“Muna jiran zuwansa, kuma ku yarda da ni, za mu fitar da tsari da zai tabbatar da nasarar jam’iyyar gaba ɗaya, cikin fahimtar juna, ba tare da wani rikici tsakanin tsofaffin mambobi da sabbin mambobi ba.”
“Haka kuma, a ra’ayina na kaina, a siyasar Najeriya abu ne mai wahala matuka gwamna mai ci ya faɗi a zaɓen fidda gwani. Irin wannan abu ba kasafai yake faruwa ba.”
“Duk da haka, idan yanayi ya sa dole a gudanar da zaɓen fidda gwani, to haka za a yi. Amma batun tikitin kai tsaye ga gwamnan ba shi ne babban abin damuwarmu a yanzu ba, za mu daidaita komai idan ya iso.”
- Abdullahi Abbas

Source: Facebook
Tsokacin Kwankwaso kan ficewar Abba daga NNPP
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon dan takarar shugaban kasa, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi magana ficewar Gwamna Abba Kabir Yusuf daga jam'iyyar NNPP.
Babban jigon na jam’iyyar NNPP kuma jagoran tafiyar Kwankwasiyya, ya bayyana cewa ba zai sayar da kansa a siyasa ba.
Kwankwaso ya ce tsawon shekarunsa a siyasa ya nuna cewa burinsa shi ne ‘yantar da talakawan Najeriya daga danniya da zalunci.
Asali: Legit.ng


