"Idan Ya Isa": Buba Galadima Ya Kalubalanci Tinubu kan Zaben 2027

"Idan Ya Isa": Buba Galadima Ya Kalubalanci Tinubu kan Zaben 2027

  • Babban jigo a jam'iyyar NNPP, Buba Galadima, ya yi tsokaci kan yawan sauya shekar da 'yan adawa suke yi zuwa APC mai mulki
  • Buba Galadima ya bayyana cewa yawan sauya shekar ba za ta sanya shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi nasara a babban zaben 2027 ba
  • Fitaccen 'dan adawan ya koro bayani kan abin da ya sanya 'yan Najeriya ba za su bari APC ta cigaba da mulkin kasar nan a badi ba

​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Babban jigo a jam'iyyar NNPP, Buba Galadima, ya yi magana kan takarar Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.

Buba Galadima ya ce Shugaba Bola Tinubu ba zai samu nasara a zaben 2027 ba idan aka gudanar da zaben cikin gaskiya da adalci.

Buba Galadima ya kalubalanci Shugaba Tinubu
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da Buba Galadima Hoto: Mohammed Umaru Bago, Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Buba Galadima ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a shirin Daily Politics na tashar Trust TV, a ranar Juma'a 23 ga watan Janairun 2026.

Kara karanta wannan

2027: APC ta tabo batun b Gwamna Abba tikitin takara kai tsaye bayan barin NNPP

Buba Galadima: 'Za a doke APC a 2027'

Buba ya ce jam’iyyun adawa za su kayar da jam’iyyar APC a 2027 idan tsarin zaben ya nuna ainihin ra’ayin masu kada kuri’a.

“Dole ne a fadi gaskiya. Babu wani dan takarar shugaban kasa na APC a 2027 da zai iya samun amincewar jama’a idan aka yi zabe cikin gaskiya da adalci."

- Buba Galadima

Me Buba Galadima ya ce kan Tinubu?

Buba Galadima ya yi watsi da batun ko sauya shekar ‘yan siyasa zuwa APC zai taimaka wa Shugaba Tinubu ya ci zabe.

“Ba zai yi nasara ba. Idan zaben zai kasance cikin gaskiya da adalci, to ya gwada. Ina kalubalantar sa."

- Buba Galadima

Jigon na NNPP ya kafa hujjarsa ne kan abin da ya bayyana a matsayin rashin jin dadin jama’a, musamman a tsakanin mazauna karkara da manoma, wadanda a cewarsa su ne mafi rinjayen al’ummar Najeriya.

Buba ya jefi gwamnatin tarayya da zargi

Kara karanta wannan

Bayan ganawa da Tinubu, Gwamna Makinde ya yi magana kan icewa daga PDP zuwa APC

Dattijon ya zargi gwamnatin tarayya kan lalata harkar noma da gangan ta hanyar tsadar kayan aiki da manufofin shigo da kaya daga kasashen waje, inda ya ce farashin muhimman abubuwa kamar taki ya tashi matuka.

“Manoma su ne mafi yawan al’ummar Najeriya. Kuma babu wani manomi da zai kada kuri’a ga gwamnatin APC."
“Masu saye ba su ji dadin wannan ci gaban ba, wanda hakan ke nufin a shekara mai zuwa babu wani kwarin gwiwa ga kowa ya koma gona."
“Idan kuma ba a je gona ba, to matsala za ta taso. Wannan gwamnati ta yanke shawarar shigo da abubuwan da ‘yan Najeriya za su iya samarwa da kansu domin karya farashi."

- Buba Galadima

Buba Galadima ya yi zargi kan gwamnatin APC
Buba Galadima tare Rabiu Musa Kwankwaso da wasu 'yan NNPP Hoto: Kwankwasiyya Online Reporters
Source: Facebook

Buba Galadima ya gargadi cewa raguwar ayyukan noma na iya kara tsananta matsalar rashin tsaro, yana mai cewa yunwa da rashin aikin yi kan zama tushen aikata laifuffuka.

Gwamna Abba ya fice daga NNPP

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya raba gari da jam'iyyar NNPP mai adawa a Najeriya.

Gwamna Abba ya aika da wasikar murabus dinsa ga shugaban NNPP na mazabarsa ta Diso-Chiranchi da ke karamar hukumar Gwale.

Hakazalika, gwamnan ya danganta matakinsa na ficewa daga jam'iyyar kan abin da ya kira rikice-rikicen cikin gida da ba a warware ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng