'Dalilin da Zai Sanya Peter Obi Ya Fice daga Jam'iyyar ADC kafin Zaben 2027'
- Ana ci gaba da tattaunawa da muhawara kan wanda zai iya samun tikitin takarar shugaban kasa na jam'iyyar hadaka ta ADC
- Masana harkokin siyasa dai na ganin fafatawar ta fi zafi ne tsakanin tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da Peter
- Wani mai sharhi kan al'amuran jama'a ya bayyana cewa akwai yiwuwar Peter Obi ya tattara kayansa ya fice daga ADC kafin zaben 2027
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Mai sharhi kan al'amuran jama'a, Jide Ojo, ya ce akwai yiwuwar Peter Obi ya bar jam’iyyar ADC ya koma wata jam’iyya kafin zaben 2027.
Jide Ojo ya bayyana cewa Peter Obi zai iya ficewa daga ADC ne idan bai samu nasara a zaben fitar da gwani na shugaban kasa na jam’iyyar ba.

Source: Twitter
Jide Ojo ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin 'The Morning Brief' na Channels Tv a ranar Laraba, 21 ga watan Janairun 2026.

Kara karanta wannan
APC ta ware matsayin da za ta ba Kwankwaso idan ya sauya sheka tare da Gwamna Abba
Me zai sa Peter Obi ya bar ADC?
Ya ce Atiku Abubakar na iya fin Peter Obi karfin kashe kudi, musamman idan jam’iyyar za ta gudanar da zaben fidda gwani ta hanyar amfani da deliget.
“Ana ta yada jita-jita cewa Atiku ya shahara wajen kashe kudi sosai a lokacin zaben fidda gwani na jam’iyya."
“Mu dauka cewa, a zabe na gaskiya da adalci a cikin ADC Atiku ne ya yi nasara, zan iya hango cewa Peter Obi zai iya barin ADC ya koma wata jam’iyya.”
- Jide Ojo
Atiku na iya fin karfin Peter Obi a ADC
Ya yi ikirarin cewa Atiku na son kasancewa a sahun gaba wajen tantance wanda zai zama dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC.
“Shi ya sa ake fargaba a wasu bangarori cewa zai iya fin Peter Obi kashe kudi, musamman idan za a yi zaben fidda gwani ta hanyar amfani da deliget."
- Jide Ojo
Peter Obi ya karfafa jam'iyyar ADC
Sai dai ya ce Peter Obi, tsohon dan takarar shugaban kasa na LP, ya kawo sabon karsashi da armashi cikin hadakar jam’iyyun adawa.
“Na kalli watsa shirye-shirye kai tsaye lokacin da ya bar LP ya koma ADC a ranar 31 ga Disamba, 2025."
"Kuma a wannan rana akalla sanatoci hudu daga Kudu maso Gabas, da ‘yan majalisar wakilai kusan 16 daga yankin, da kuma wasu ‘yan majalisun jihohi da ba a iya tantance yawansu ba, sun ce sun bi shi zuwa ADC."
"Lokacin da Atiku Abubakar ya bar jam’iyyarsa makonni kafin hakan, a karshen Nuwamba, ban ga wani sanata ko gwamna da ke kan mulki da ya bi shi ba.”
Jide Ojo ya tuna cewa Obi ya bayyana karara cewa lallai zai kasance dan takara a zaben 2027.
“Abin da Peter Obi ke nufi shi ne ba zai zama dan takarar mataimakin shugaban kasa ba."
- Jide Ojo

Source: Facebook
Peter Obi ya koka kan tafiye-tafiyen Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi, ya koka kan tafiye-tafiyen Mai girma Bola Tinubu.
Peter Obi ya jefo tambaya game da inda Shugaba Bola Tinubu ya shiga a daidai lokacin da ƙasar ke fuskantar matsalolin tattalin arziki da tsaro.
Hakazalika, Peter Obi ya kuma soki shugaban kasar na Najeriya kan rashin yi wa ’yan ƙasa jawabi a farkon sabuwar shekarar 2026.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

