Takarar 2027: Yadda ake Son Tada Rikici a ADC da Matakin da Atiku Ya Dauka

Takarar 2027: Yadda ake Son Tada Rikici a ADC da Matakin da Atiku Ya Dauka

  • Atiku Abubakar ya yi kira da a dakatar da cin zarafin juna tsakanin magoya bayansa da Obidients domin karfafa haɗin kai a jam'iyyar ADC
  • Rikicin ya ƙara ƙamari ne bayan Peter Obi ya shiga ADC daga LP, lamarin da ya tayar da muhawara kan wanda ya dace ya rike tutar jam’iyyar
  • Jagororin ADC a Najeriya sun gargaɗi mambobi da su guji rikice-rikice da ka iya raunana jam’iyyar gabanin 2027 da ake ganin zai kai ga nasararsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya shiga tsakani domin kwantar da hankula bayan barkewar rikici tsakanin magoya bayansa da masu goyon bayan tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi.

Rahotanni sun nuna cewa an fara samun sabanin ne kan tikitin takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar adawa ta ADC a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Atiku ko Obi? An fadi wanda zai tarwatsa ADC idan aka ba shi a 2027

Atiku Abubakar da Peter Obi
Masu neman takarar shugaban kasa a ADC, Atiku Abubakar da Peter Obi. Hoto: Mr Peter Obi
Source: Facebook

Martanin Atiku a X ya biyo bayan makonni na muhawara mai zafi, musamman a kafafen sada zumunta, tun bayan da Peter Obi ya fice daga jam’iyyar LP zuwa ADC a watan Disamban 2025.

Rikicin magoya baya ya fara ɗaukar sabon salo ne bayan da Obidients suka fara matsa lamba ga Atiku da ya goyi bayan Obi a matsayin wanda zai ɗauki tutar ADC, lamarin da ya jawo martani daga ɓangaren magoya bayan Atiku.

Kiran Atiku Abubakar ga 'yan ADC

Atiku ya fito fili ya yi kira ga magoya bayansa da na Peter Obi da su rage zafafa kalamai, yana mai gargadin cewa cin zarafin juna na raunana haɗin kan jam’iyyar adawa.

A wani saƙo da ya wallafa, Atiku ya bayyana rikicin a matsayin “yaƙin cikin gida” da zai cutar da muradun ADC da Najeriya gaba ɗaya.

Daily Trust ta wallafa cewa ya ce duk wanda ke zagin Obi ko Atiku ba ya yi wa jam’iyyar ko ƙasar fatan alheri, yana mai jaddada cewa APC ce kawai ke amfana da irin wannan sabani.

Kara karanta wannan

Yadda yaron shago ya hallaka mai gidansa makonni 3 bayan aurensa a Gombe

Atiku ya bayyana cewa haɗin kai ne kaɗai zai ba 'yan adawa damar fuskantar jam’iyya mai mulki, yana mai kira da a mayar da hankali kan abin da ya haɗa kowa wuri guda.

Yadda rikicin takara ya taso a ADC

Maganganun Atiku sun biyo bayan saƙon wani mai amfani da X da ake kira Everest, wanda ya zargi magoya bayan Atiku da raina Peter Obi.

Daga baya, wannan mutumi ya amince da kiran Atiku, yana mai cewa idan aka dakatar da irin waɗannan kalamai, ADC za ta zama jam'iyya mai ƙarfi da za ta iya kalubalantar APC yadda ya kamata.

Manyan 'yan ADC yayin wani taro
Shugabannin jam'iyyar ADC a Najeriya yayin taro a Abuja. Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Siyasar 2027: Obasanjo ya ziyarci IBB

A wani labarin, mun kawo muku cewa tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya ziyarci Janar Ibrahim Badamasi Babangida a Neja.

Ganawar shugabannin ta jawo rade-radi game da makomar siyasar 2027, musamman batun 'yan takarar jam'iyyun adawa a Najeriya.

Wasu rahotanni sun nuna cewa a kwanakin baya Obasanjo ya fara maganar hada Peter Obi da Rabiu Kwankwaso su yi takara tare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng