Bayan Ganawa da Tinubu, An Ji Lokacin da Gwamna Abba Zai Zama 'Dan APC a Kano

Bayan Ganawa da Tinubu, An Ji Lokacin da Gwamna Abba Zai Zama 'Dan APC a Kano

  • Shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas ya ce Gwamna Abba Kabir Yusuf na iya karbar katin zama cikakken 'dan APC daga nan zuwa ranar Laraba
  • Abdullahi Abbas ya ce suna sa ran tsohon shugaban APC, Abdullahi Ganduje da Abba su dawo Kano domin kaddamar da aikin rijistar 'ya 'yan jam'iyya
  • 'Dan siyasar ya yi kira ga mutanen Kano da su fito su mallaki katin APC saboda yana da muhimmanci a gudanar da harkonin jam'iyya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Shugaban jam’iyyar APC na Jihar Kano, Abdullahi Abbas, ya bayyana cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na iya yin rajista tare da karbar katin zama 'dan APC a wannan makon.

Abdullahi Abbas ya ce Gwamna Abba zai iya karbar katinsa na jam'iyyar APC, wanda zai tabbatar da sauya shekarasa a hukumance tsakanin gobe Talata zuwa ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Aikin gama ya gama, Shugaba Tinubu ya shiga ganawa da gwamnan Kano a Abuja

Shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas.
Shugaban jam'iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas
Source: Facebook

Shugaban APC ya fadi hakan ne a wata hira da Freedom Radio, inda ya yi bayani kan ma’aikatan wucin-gadi kimanin 1,500 da suka dauka don gudanar da aikin rajistar mambobi ta na’ura a Kano.

Yaushe Abba zai iya zama 'dan jam'iyyar APC?

Ya bayyana cewa APC ta yanke shawarar jinkirta fara rajistar Kano ne har sai uban APC na Kano, Dr. Abdullahi Ganduje, da kuma gwamnan sun dawo daga Abuja, bayan ganawarsu da Shugaba Bola Tinubu.

Abdullahi Abbas ya ce:

“Ku kasance cikin shiri, za mu iya kiran ku gobe Talata, ya danganta da lokacin da jagoran jam’iyya, Ganduje, da gwamna suka iso Kano. Amma muna fatan ba zai wuce ranar Laraba ba.”
"Idan mai girma gwamna ya shigo a yan kwanakin nan, za a kaddamar da yin rijistar tare da shi, idan bai shigo ba za mu ci gaba da aikinmu, idan ya dawo sai ya je mazabarsa a masa.

Kara karanta wannan

Tazarce: Gwamna ya jero dalilan da za su sanya ƴan Kaduna su zabi Tinubu a 2027

Gwamna Abba zai zama jagoran APC a Kano?

Danagane da batun sauya shekar gwamnan Kano, Abbas ya ce suna fatan Abba ya gama shiri kuma ya kaddamar da shirin rijistar mambobi tare da Ganduje a Kano.

Ya kuma tabbatar da cewa idan Gwamna Abba ya shigo APC, shi ne zama jagoran jam'iyyar a jihar Kano yayin da Ganduje zai zama kamar uban jam'iyya.

Abdullahi Abbas, wanda ya ce jam'iyyar APC tana da burin doke kowace jiha, har da Legas, wajen yawan mambobi, ya bukaci ma’aikatan da aka dauka da su yi wa duk wanda ya nuna sha’awa rajista ba tare da nuna bambanci ba.

Gwamna Abba da Ganduje.
Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano da tsohon shugaban APC, Dr. Abdullahi Ganduje Hoto: Sanusi Bature, Dr. Abdullahi Ganduje
Source: Facebook

APC ta aika sako ga mutanen Kano

Haka kuma, Dan Sarki ya ce za a samar da tsarin ba da lada ga kananan hukumomi da mazabun da suka fi kowa samar da mambobi yayin gudanar da aikin, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

A karshe, Abdullahi Abbas ya yi kira ga daukacin al'ummar jihar Kano da su fito kwansu da kwarkwata su yi rijistar zama mambobin APC saboda tana da matukar muhimmanci.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya aika sako ga APC ta Kano kan shirin sauya shekar Gwamna Abba

Gwamna Abba ya gana da Shugaba Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya kai ziyara fadar shugaban kasa da ke birnin tarayya Abuja.

Rahotanni sun tabbatar da cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu yan shiga wata ganawar sirri da gwamnan Kano da yammacin ranar Litinin.

Duk da babu wata sanarwa a hukumance game da abin da fanawar ta kunsa, amma ana zaton cewa tana da nasaba da shirin sauya shekar Abba zuwa APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262