Dogara da Kiristoci 3 da Ake Sa Ran Tinubu Zai Maye Gurbin Shettima da Su a 2027
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana nazarin wasu fitattun Kiristocin Arewa hudu domin zama abokan takararsa a zaben 2027 mai zuwa
- An rahoto cewa Tinubu na nazarin dauka tsakanin Yakubu Dogara, tsohon kakakin majalisa da Christopher Musa da wasu Kiristoci biyu
- Wannan sabon mataki na nufin gyara korafe-korafen da aka yi kan tikitin Musulmi da Musulmi wanda jam'iyyar APC ta yi amfani da shi a 2023
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Sababbin bayanai sun nuna cewa Shugaba Bola Tinubu yana nazarin wasu fitattun Kiristocin Arewa hudu a matsayin abokan takara a zaben 2027.
Idan har wadannan bayanai suka tabbata, hakan na nufin cewa Shugaba Tinubu zai ajiye mataimakinsa na yanzu, Kashim Shettima a neman tazarcensa.

Source: Twitter
Kiristoci 4 da za su iya maye gurbin Shettima
Majiyoyi daga kafafen yada labarai daban-daban sun ambaci sunayen Hon. Yakubu Dogara, Lt-Gen. Christopher Musa (mai ritaya) daga cikin wadanda Tinubu ke nazari, in ji rahoton The Guardian.
Hakazalika, daga cikin wadanda ake sa ran za su iya maye gurbin Shettima a 2027 akwai Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Filato, da kuma Bishop Matthew Hassan Kukah.
Ana kallon wadannan sunaye ne a matsayin wani bangare na dabarun siyasar Shugaba Tinubu domin samar da daidaito tsakanin addini da kuma yankunan kasar nan.
Dabarun siyasa da kuma daidaiton addini
Rahotanni sun bayyana cewa makarraban shugaban kasar suna nazarin wadannan mutane ne domin amsa korafe-korafen da suka biyo bayan tikitin Musulmi da Musulmi a 2023.
Masu sharhi kan lamuran yau da kullum sun lura cewa kundin tsarin mulki ya bai wa Shugaba Tinubu damar zabar abokin takara daga kowane bangare na kasar.
Sukar da aka rika yi wa tikitin 2023 ta fito ne daga ciki da wajen Najeriya, har ma da jami'an gwamnatin kasar Amurka wadanda suka bukaci a zabi Kirista a 2027.
Kalubalen tsaro da kuma hadin kan kasa

Kara karanta wannan
Barazanar Bello Turji ta sa 'yan Najeriya gudun hijira Nijar, suna mawuyacin hali
Kungiyoyin Kirista da na farar hula sun bayyana cewa samar da daidaito a shugabanci zai iya karfafa hadin kan kasa, musamman a yankunan da ke fama da su.
Duk da haka, kungiyoyin Musulmi na Arewa sun bayyana cewa rashin tsaro ya shafi kowa, ba tare da la'akari da addini ba, kamar yadda Boko Haram suke kai hare-hare kan kowa.
Suna cewa hare-haren yan bindiga da garkuwa da mutane sun addabi kowa, don haka kalubalen na kasa baki daya ne ba wai na wani bangaren addini ba.

Source: Facebook
Waye zai fi dacewa a matsayin mataimaki?
Tambayar da masana siyasa ke yi yanzu ita ce, waye a cikin mutane hudu nan—Dogara, Janar Musa, Mutfwang ko Kukah—zai fi dacewa da mataimakin shugaban kasa?
Dole ne shugaban Najeriya na gaba ya mayar da hankali kan samar da kwanciyar hankali, ci gaban tattalin arziki, da kuma adalci ga dukkan yankuna da kananan hukumomi.
Yayin da aka tunkari shekarar 2027, ana sa ran tattaunawa kan zabin Shugaba Tinubu zai kara zafi tare da sauya tsarin kawance a cikin jam'iyyar APC mai mulki.

Kara karanta wannan
Shugaba Tinubu ya turo sako daga kasar waje kan rasuwar malamin Musulunci a Najeriya
Amurka na matsin lamba ga Tinubu
A wani labarin makamancin wannan, mun rahoto cewa, ana kara matsin lamba kan Shugaba Bola Tinubu da ya sake duba tsarin tikitin shugaban ƙasa da mataimaki gabanin 2027.
Majiyoyi masu ƙarfi sun bayyana cewa wasu daga Amurka sun nuna ra’ayin cewa ya dace Tinubu ya tsaya da tikitin Musulmi da Kirista a 2027.
Rahotanni sun ce kafin matsin lamba daga Amurka, an fara la’akari da sauke Kashim Shettima tare da maye gurbinsa da Abdulaziz Yari, ko Nuhu Ribadu, lissafin da yanzu yake canja.
Asali: Legit.ng
