Dalilin da Ya Sa Gwamna Fubara bai Damu da Shirin Majalisar Dokoki na Tsige Shi ba

Dalilin da Ya Sa Gwamna Fubara bai Damu da Shirin Majalisar Dokoki na Tsige Shi ba

  • Majalisar dokokin jihar Rivers ba ta aika wa Gwamna Siminalayi Fubara takardar sanar da shi shirin tsige shi a hukumance ba
  • Hadimin gwamnan Rivers, Darlington Orji ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da aka yi da shi ranar Juma'a, 16 ga watan Janairu, 2026
  • Mista Orji ya musanta ikirarin da Majalisar ta yi cewa ta aika wa Gwamna Fubara da takarda, inda ya bukaci ta kawo hujja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Rivers, Nigeria - Mai ba Gwamnan Rivers shawara kan harkokin siyasa, Darlington Orji, ya yi karin haske kan shirin da Majalisar dokoki take na tsige Gwamna Siminalayi Fubara.

Mista Orji ya bayyana dalilin da ya sa Gwamna Fubara bai yi magana ko maida martani kan zargin rashin ladabi da rashin da'a da Majalisar dokokin ta masa ba.

Kara karanta wannan

Rikici ya dauki zafi, babbar kotu ta tsoma baki kan yunkurin tsige Gwamna Fubara

Gwamna Siminalayi Fubara.
Gwamna Siminalayi Fubara lokacin da ya rantsar da wasu hadimai a fadar gwamnatin Rivers Hoto: Sir. Siminalayi Fubara
Source: Facebook

Punch ta ce a wata hira da aka yi da shi a Abuja, hadimin gwamnan ya ce Fubara bai maida martani ba ne saboda har yanzu Majalisa ba ta tura masa takarda a hukumance ba.

Tun da farko, Premium Times ta ruwaito cewa Majalisar Dokokin Rivers ta fara shirin tsige Gwamna Fubara da mataimakiyarsa, Farfesa Ngozi Nma Odu, a ranar 8 ga Janairu bisa zargin aikata manyan laifuffuka.

Wannan dai shi ne karo na uku da ‘yan majalisar ke yunkurin tsige Gwamnan tun bayan hawansa mulki a shekarar 2023.

Shin Majalisa ta sanar da Fubara shirinta?

Da yake jawabi, Darlington Orji ya ce duk da cewa Gwamna Fubara ya ji labarin shirin tsige shi ta kafafen watsa labarai da na sada zumunta, har zuwa safiyar Juma’a ba a miƙa masa wata takardar sanarwa a hukumance ba.

“Majalisar Dokokin Jihar Rivers ta yi zama a ranar 8 ga Janairu, 2026, amma har zuwa safiyar yau Juma’a, Gwamna Siminalayi Fubara bai karɓi wata sanarwa ta tsige shi ko zargin aikata laifi ba,” in ji Orji.

Kara karanta wannan

Rikici ya dawo 'danye, 'Yan Majalisa 4 sun canza tunani kan yunkurin tsige Gwamna Fubara

Fubara ta zargi Majalisa da karya doka

Ya kara da cewa majalisar ba ta bi ka’idojin doka da kundin tsarin mulki suka tanada ba wajen fara shirin tsige gwamnan.

A cewarsa, kotunan Najeriya da dama, ciki har da Kotun Koli, sun yanke hukunci cewa dole ne a miƙa wa gwamna sanarwar tsige shi kai tsaye.

“Ba a aiko masa da wata akardar ba. Da an yi hakan, da ya mayar da martani, domin ba shi da abin da zai ɓoye,” in ji Orji.
Kakakin Majalisar Rivers.
Kakakin Majalisar dokokin jihar Rivers, Rt. Hon. Martins Amaewhule Hoto: Rivers State House of Assembly
Source: Facebook

Ya kalubalanci Kakakin Majalisar, Rt. Hon. Martin Amaewhule, da ya fito da hujja idan har suna ikirarin cewa sun miƙa wa gwamnan takardar sanarwa a hukumance.

Kotu ta dakatar da shirin tsige Fubara

A baya, kun ji cewa babbar kotun jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa, Farfesa Ngozi Nma Odu.

Kotun ta hana babban alkali, Mai shari’a Simeon Chibuzor Amadi, karɓa ko yin aiki da kowace wasika daga Majalisa da ta shafi yunkurin tsige Fubara.

Kotun ta hana babban alkalin kafa kwamitin bincike kan zargin rashin da’a da ake yi wa gwamna da mataimakiyarsa, na tsawon kwanaki bakwai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262