ADC Ta Samo Hanyar Ceto Najeriya daga Hannun Shugaba Tinubu

ADC Ta Samo Hanyar Ceto Najeriya daga Hannun Shugaba Tinubu

  • Jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya ta koka kan salon mulkin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, inda ta yi magana kan kubutar da kasar nan
  • Mai magana da yawun ADC, Bolaji Abdullahi, ya bayyana cewa akwai hanyar da za a bi domin ganin an ceto Najwriya daga halin da ta tsinci kanta a ciki
  • Bolaji ya kuma zargi gwamnati da yin jabun dokoki bayan da majalisar tarayya ta amince da su, kuma ya ce hakan bai taba faruwa ba a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Mai magana da yawun ADC, Bolaji Abdullahi, ya ce babban manufar jam’iyyar adawar ita ce kifar da Shugaba Bola Tinubu daga mulki.

Bolaji Abdullahi ya bayyana hakan a matsayin wajibi domin ceto Najeriya daga abin da ya bayyana gazawa a fannin mulki da ba a taɓa ganin irinsa ba.

Kara karanta wannan

Waiwaye: Yadda ɗan Obasanjo ya goyi bayan Buhari shekaru kafin Abba Atiku ya koma APC

ADC ta ragargaji shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da kakakin APC na kasa, Bolaji Abdullahi Hoto: Sanusi Bature D-Tofa, Bolaji Abdullahi
Source: Facebook

Mai magana da yawun jam'iyyar ADC ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da tashar Channels tv a shirinsu na 'Politics Today' ranar Juma'a, 16 ga watan Janairun 2026.

Mece ce manufar jam'iyyar ADC?

Kakakin ADC mai hamayya ya bayyana cewa abin da jam'iyyar ta tasa a gana shi ne raba Shugaba Tinubu da mulki don ceto Najeriya.

“Manufarmu kawai ita ce cire Tinubu daga mulki. Wannan shi ne ajandar, ba wai don wata fa’idar Najeriya ba."
"Tabbas muna son cire Tinubu daga mulki, domin sai an cire shi ne kawai za mu iya ceto kasarmu."
"Babu wani yanayi da zai ba da damar ya ci gaba da zama a kan mulki mu kuma mu iya ceto kasar. Yanzu abubuwa na nuna kamar an yi garkuwa da ita ne.”

- Bolaji Abdullahi

An soki jami'an gwamnatin Tinubu

Bolaji Abdullahi ya kuma soki halayen wasu mutane a cikin gwamnati, yana zarginsu da tafiyar da kasa da da yaren ’yan fashi.

Kara karanta wannan

Kusa a APC ya sha alwashin cin amanarta idan aka ba Abba tikitin takara a Kano

“Idan ka dubi halayen wasu mutanen da ke cikin gwamnati, idan ka ji suna cewa ‘za ka iya kwace iko da ƙarfi ka gudu da shi,’ wannan harshen ’yan fashi ne."

- Bolaji Abdullahi

ADC ta yi zargi kan gwamnatin Tinubu

Ya kuma zargi gwamnati da yin jabun dokoki da majalisar dokoki ta kasa ta amince da su, yana mai cewa irin wannan abu bai taɓa faruwa ba a tarihin Najeriya.

ADC ta yi zargi kan gwamnatin Tinubu
Mai magana da yawun jam'iyyar ADC na kasa, Bolaji Abdullahi Hoto: @BolajiADC
Source: Twitter
“Gwamnatin da za ta iya yin jabun doka da aka riga aka amince da ita a hukumance, me za ka kira hakan? Akwai abubuwan da suka faru a baya-bayan nan da ba a taɓa ganin irinsu ba a tarihin Najeriya."
“Wannan shi ne karon farko da majalisar tarayya za ta kafa doka, sai wasu mutane a cikin gwamnati su zauna su sauya ta."

- Bolaji Abdullahi

Jigo a ADC ya zargi Tinubu da sakaci

A wani labarin kuma, kun ji cewa jigo a jam'iyyar adawa ta ADC, Ladan Salihu, ya zargi gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da yin sakaci wajen fuskantar kalubalen matsin tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Sauya shekar Abba: NNPP ta ce lokaci bai ƙure ba, tana fatan Gwamna zai hakura

Ladan Salihu Salihu ya bayyana cewa cire tallafin mai ba tare da isassun matakan rage radadi ba ya kara tsananta wahalhalun tattalin arziki.

Ya bayyana cewa cire tallafin mai da Shugaba Tinubu ya yi, ya jawo 'yan Najeriya na kashe kudade masu yawa a fannin sufuri.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng