Rikici Ya Dawo 'Danye, 'Yan Majalisa 4 Sun Canza Tunani kan Yunkurin Tsige Gwamna Fubara

Rikici Ya Dawo 'Danye, 'Yan Majalisa 4 Sun Canza Tunani kan Yunkurin Tsige Gwamna Fubara

  • Majalisar dokokin jihar Rivers na ci gaba da shirinta na sauke Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa, Farfesa Ngozi Odu
  • 'Yan majalisa hudu da kwanakin baya auka nemi a yi sulhu cikin ruwan sanyi, sun dawo sun aake goyon bayan yunkurin tsige Fubara da Odu
  • A cewar yan Majalisar, Gwamna Fubara bai nuna sha'awar zaka teburin tattaunawa domin samun masalaha ba, don haka ya cancanci a tsige shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Rivers, Nigeria - Membobin Majalisar Dokokin Jihar Rivers hudu sun canza tunani kan matsayarsu ta janyewa daga shirin tsige Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa, Farfesa Ngozi Odu.

Yan Majalisar guda hudu sun yi amai sun lashe, sun sauya shawararsu inda suka bayyana cikakken goyon bayansu ga shirin tsige gwamnan da mataimakiyarsa.

Gwamna Fubara da mataimakiyarsa.
Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa, Farfesa Ngozi Odu Hoto: Sir. Siminalayi Fubara
Source: Twitter

Yan Majalisa 4 sun canza tunani a Rivers

Kara karanta wannan

Shirin tsige Gwamna Fubara a Rivers ya sake gamuwa da cikas a majalisa

Jaridar Leadership ta rahoto cewa ‘yan majalisar sun hada da Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar, Hon. Sylvanus Nwankwo da Hon. Peter Abbey, mai wakiltar mazabar Degema.

Sauran mutum biyun su ne, Hon Barile Nwakoh na mazabar Khana I; da kuma Emilia Amadi mai wakiltar mazabar Obio/Akpor II a Majalisar dokokin jihar Rivers.

Karkashin jagorancin Shugaban Marasa Rinjaye, Nwankwo, ‘yan majalisar sun bayyana cewa sun dauki wannan matakin ne sakamakon abin da suka kira sakacin gwamna wajen neman maslaha a rikicin da ke faruwa.

Sun bayyana sabuwar matsayar tasu ne a ranar Juma’a yayin da suke tattaunawa da manema labarai a kofar shiga zauren Majalisar Dokokin Jihar Rivers.

Wannan mataki na zuwa ne kwanaki biyu kacal bayan 'yan Majalisar hudu sun yi kiran a sasanta rikicin siyasar da ya girgiza jihar cikin ruwan sanyi.

Dalilan 'yan Majalisa na juyawa Fubara baya

Nwankwo ya ce:

“Za ku tuna cewa a ranar 12 ga watan Janairun 2026, ni da abokin aikina, Honarabul Peter Abbey, mun yi kira ga abokan aikinmu da su nemi mafita ta siyasa kan wannan dambarwa da ke tsakanin Majalisa da Gwamnan Jihar Rivers.

Kara karanta wannan

Sakon da Bello Turji ya aiko ya hargitsa mutane, an fara guduwa a jihar Sakkwato

“A yayin da muke jiran martanin wannan kira na mu, mun gano cewa gwamna da mataimakiyarsa sun sa yaran su a kafafen yada labarai sun ci gaba da caccakar Majalisa maimakon neman maslahar siyasa.
"A kan wannan dalili ne ni, Honarabul Sylvanus Nwankwo, da abokin aikina a nan, Honarabul Peter Abbey, muke tabbatar da cewa muna goyon bayan shirin tsigewar.
Majalisar Rivers.
Babban allon sanarwa da ke kofar shiga zauren Majaliaar dokokin jihar Rivers Hoto: Rivers State Assembly
Source: Twitter

Haka kuma, Hon. Nwakoh da Amadi sun ce sun yanke shawarar dawowa su goyi bayan shige Fubara ne bayan sun fahimci gwamnan da mataimakiyarsa ba su da sha’awar warware rikicin cikin ruwan sanyi.

Jaridar Daily Trust ta gano cewa ana zargin matakin da yan Majalisar suka dauka daga baya na da alaka da matsin lamba daga shugabannin siyasa, wadanda ke biyayya ga Ministan Abuja, Nyesom Wike.

Majalisar dokokin Rivers ta koka

A baya, kun ji cewa Majalisar Dokokin Jihar Rivers ta bayyana cewa wasu mutane na yunkurin hana shirin tsige Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa.

Ta ce mutanen na ƙoƙarin amfani da wasu kotunan Fatakwal domin karya ko raunana shirin tsige Gwamna Fubara da mataimakiyarsa duk da laififfukan da suka aikata.

Majalisar Dokokin Jihar Rivers karkashin jagorancin Rt. Hon. Martin Chike Amaewhule, ta yi kira ga kowa da kowa da ya mutunta doka da oda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262