Kusa a APC Ya Sha Alwashin Cin Amanarta idan Aka ba Abba Kabir Tikitin Takara

Kusa a APC Ya Sha Alwashin Cin Amanarta idan Aka ba Abba Kabir Tikitin Takara

  • Jigon APC a Kano, Abdulmajeed Almustapha Kwamanda, ya soki jam’iyyarsa kan yadda take watsi da ’ya’yanta
  • Kwamanda ya ce za su iya cin amanar APC idan aka hana Barau Jibrin taka rawa a 2027, yana mai cewa hakan zai jawo faduwarta
  • Ya kuma caccaki gwamnatin Abba Kabir Yusuf, yana zarginta da almundahana, tare da yabon Barau Jibrin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Jigon APC a Kano, Abdulmajeed Almustapha Kwamanda ya yi tsokaci game da dambarwar siyasar jihar da ake ciki.

Dan Bilki Kwamanda ya soki jam'iyyarsa ta APC game da yadda take rike 'ya'yanta duk da gudunmawa da suka bata.

Dan Bilki Kwamanda ya soki Abba Kabir
Jigon APC, Abdul-majeed Dan Bilki Kwamanda da Abba Kabir Yusuf. Hoto: Abdul-majeed Dan Bilki, Abba Kabir Yusuf.
Source: Facebook

Kwamanda ya magantu kan ba Abba takara

Dan Bilki ya bayyana haka ne a cikin wani bidiyo yayin wata hira da aka da shi wanda Abdul-Aziz Na'ibi Abubakar ya wallafa a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Sauya shekar Abba: NNPP ta ce lokaci bai ƙure ba, tana fatan Gwamna zai hakura

Ya bayyana za su iya cin amanar APC ta ko ta ina idan har aka ce za a hana Barau Jibrin taka rawarsa a zaben 2027 da ke tafe.

Kwamanda ya kuma caccaki gwamnatin Abba Kabir Yusuf inda ya ce kwasar kudin al'umma kawai suka sani kuma mabarnata ne.

Ya ce:

"Ai babu yadda za a yi a siyasa yadda muka santa wallahi gwara mu yi zubar gado, yau aka wayi gari a ce a rufe siyasar Barau a Arewa gwara APC ta fadi.
"Gwara mu ci amanarsu mu fadawa talakawa ka da su zabi mabarnata, gwamnatin Abba ai akwai barna cikinta sosai.
"Gwamnati ce fa ake yi da 'ya'ya da mata, gwamnati ce mabarnata ba iyaka suka hadu, da uba da yaran gida da yaran uban gida suke diban kudin mutane ba dalili."
Dan Bilki Kwamanda ya yabawa Sanata Barau Jibrin
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin. Hoto: Barau I Jibrin.
Source: Facebook

Kwamanda ya yabawa kokarin Barau Jibrin

Da aka tambate shi bayan cewa za su yi zubar gado, hakan bai nuna rashin kishin jam'iyya? Sai Kwamanda ya ce ai ita ma APC ba ta kishin 'ya'yanta.

Ya bayyana halayen kirki na Barau Jibrin da yadda yake taimakawa 'ya'yan talakawa wurin tallafin karatu da kuma ba su ayyuka.

Kara karanta wannan

'Annoba ne ga jam'iyyu': Tsohon dan takarar gwamnan Kano ya fadi matsalar Kwankwaso

"Ai jam'iyyar ma ba ta kishin mutane, da tana kishinmu ai babu wanda za a tsayar babu hamayya kamar Barau Jibrin saboda shi jama'a suke so.
"Shi ne mutumin kirki, shi ne mai juriya, duk Arewa babu mai taimakon mutane kamar Barau Jibrin yana taimakon na birni da na kauye.
"Ya ba 'ya'yan talakawa tallafin karatu sun fi mutum 2,000 yanzu kuma a ofishinsa akwai mutane sama da 3,000 da ya ba su aiki."

- Dan Bilki Kwamanda

Aikin hajji: Kwamanda ya soki Abba Kabir

Kun ji cewa AbdulMajid Dan Bilki Kwamanda ya zargi gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, da soke sunansa daga jerin masu tafiya aikin hajji.

Kwamanda ya bayyana cewa Mataimakin Shugaban kasa, Kashim Shettima, ne ya ba shi damar tafiya wanda gwamnan Kano ya hana.

Kwamanda ya nuna takaicinsa kan yadda gwamnan ya cire sunansa daga cikin wadanda za su yi hajjin a shekarar 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.