Borno: Tsohon Ɗan Takarar Gwamna Ya Yi Watsi da PDP, Ya Rungumi ADC gabanin 2027
- Tsohon ɗan takarar gwamna, Mohammed Ali Jajari ya fice daga babbar jam'iyyar hamayya ta PDP, ya koma ADC mai adawa da gwamnatin tarayya
- Babban ɗan siyasar kuma mai son takara ya ce matakin ya biyo bayan tuntuba da nazarin halin siyasa, kuma ya gano ADC ce mafita da za ta jawo ci gaba
- A jawabinsa, Alhaji Mohammed Ali Jajari ya yi alkawarin shugabanci nagari da fifita muradun jama’ar jihar Borno a tafiyar siyasarsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Borno – Tsohon dan takarar gwamnan Jihar Borno a zaben 2023, Mohammed Ali Jajari, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar adawa ta PDP, tare da bayyana shigarsa jam’iyyar ADC.
Jajari ya dauki wannan mataki ne bayan yin tuntuba mai zurfi da manyan jiga-jigan siyasa da kuma nazari kan hakikanin halin da siyasar jihar Borno ke ciki a halin yanzu.

Source: Twitter
Wannan sanarwa ta fito ne a wata sanarwa da kungiyar ADC Vanguard ta wallafa a shafin X, inda ya ce an kammala dukkannin shirye-shirye kan batun.
Tsohon ɗan takara a Borno ya koma ADC
Mohammed Ali Jarari ya bayyana cewa burinsa shi ne cika muradin al’ummar jihar, tare da samar da wata sabuwar hanya ta siyasa da za ta amfanar da jama’a.
Jajari ya yi rajista a hukumance da jam’iyyar ADC, yana mai jaddada cewa sauyin jam’iyyar da ya yi ba don son zuciya ba ne, illa don neman hanyar da za ta ba shi damar yin hidima ga mutanen Borno.
Ya ce wannan sabon mataki yana nuna kudurinsa na ci gaba da fafutukar samar da shugabanci nagari, adalci, da hada kan al’umma ba tare da wariya ba.
Tsohon ɗan takaran ya fadi dalilin shiga ADC
A cikin sanarwar, Jajari ya bayyana cewa shiga ADC wani sabon babi ne a tafiyarsa ta siyasa, inda ya kuduri aniyar bayar da shugabanci mai ma’ana da kuma gina ingantaccen dandali da ya dace da bukatun talakawa.
Ya ce ADC na ba shi damar gabatar da sahihin muradunn siyasa da zai saurari kukan jama’a tare da aiwatar da manufofin da za su inganta rayuwar al’umma.
Jajari ya kuma nuna godiyarsa ga shugabannin PDP, magoya baya, da duk masu fatan alheri da suka mara masa baya a tsawon lokacin da ya shafe yana tafiyar siyasa.

Source: Original
'Dan siyasar ya ce ba zai taba mantawa da gudummawar da suka bayar ba, yana mai cewa goyon bayansu ya taka muhimmiyar rawa wajen gina kwarewarsa da fahimtarsa kan bukatun jama’a.
Jajari ya yi kira ga duk masu kishin ci gaba da hadin kai da su hada kai da shi a karkashin inuwar jam’iyyar ADC domin gina Jihar Borno domin kowa ya amfana.
Jam'iyyar ADC ta shiga Borno da karfinta
A baya, mun wallafa cewa jam’iyyar ADC na ƙara samun karɓuwa a jihar Borno, musamman bayan kaddamar da Sanata David Mark a matsayin sabon shugaban rikon kwarya na ƙasa.
Rahotanni daga jihar sun nuna cewa ana ci gaba da samun sauya sheƙa mai yawa daga jiga-jigan jam’iyyun adawa, tare da wasu fitattun ‘yan APC, zuwa jam’iyyar ADC da ke son karbe mulki a 2027.
An tabbatar da cewa Alhaji Idris Mamman Durkwa, tsohon mai neman takarar gwamna, ya fice daga jam’iyyarsa ya koma ADC, kuma yana daga cikin manyan jihar da suka sauya sheka.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

