Sauya Sheka: An Jibge Jami'an Tsaro, Motocin Yaki a Kofar Gidan Gwamnatin Kano

Sauya Sheka: An Jibge Jami'an Tsaro, Motocin Yaki a Kofar Gidan Gwamnatin Kano

  • Rahotanni sun bayyana cewa an girke jami’an tsaro masu yawa a Fadar Gwamnatin Kano a safiyar yau Litinin 12 ga watan Janairu, 2026
  • Daga cikin karin jamian tsaron da aka jibge akwai ‘yan sanda da jami’an DSS da sauran jami’an tsaro da ke tsaron Fadar gidan gwamanti
  • An hango motocin APC guda bakwai a muhimman wurare da ke kewaye da fadar gwamnati yayin da batun sauya sheka ke kara karfi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Rahotanni sun tabbatar da cewa an samu tsauraran matakan tsaro a Fadar Gwamnatin Jihar Kano a ranar Litinin 12 ga watan Janairu, 2026.

Karin jami’an tsaron na zuwa ne bayan shirin sauya sheƙar da ake cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na shirin yi daga NNPP zuwa APC mai mulkin Najeriya.

Kara karanta wannan

Magana ta kare: Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kammala shirin shiga APC, an sa rana

An jibge jamia'an tsaro a gidan gwamnatin Kano
Wasu daga cikin jami'an tsaro da aka gani a kofar gidan gwamnatin Kano Hoto: Dala A Yau
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta lura da tarin jami’an tsaro da suka haɗa da ‘yan sanda na rundunar Najeriya da kuma jami’an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) na tsaron Fadar.

An tsauraran matakan tsaro a jihar Kano

Duk da cewa ba a fitar da wata sanarwa a hukumance da ke tabbatar da shirin sauya sheƙar ba, majiyoyi na kusa da al’amuran siyasa sun nuna cewa gwamnan na nazarin komawa APC.

A ranar Litinin, jami’an tsaro sun kafa shingaye a muhimman wurare, tare da tsayawa don tsare babbar kofar shiga fadar gwamnati shatale-talen da ke kusa da harabar fadar.

Ana zaton a jibge jami'an ne saboda shirin sauya shekar Gwamna
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf yana jawabi a gaban wani taro Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

An kuma lura da cewa akalla motocin yaki masu sulke, wato ‘Armoured Personnel Carriers’ (APCs) guda bakwai, na ‘yan sanda da DSS.

Haka kuma an girke su a wurare masu muhimmanci domin dakile duk wani tashin hankali ko taruwar jama’a da ka iya tasowa.

Gwamnatin Kano ta magantu kan sauya sheka

Kara karanta wannan

Fubara: Majalisar dokokin Ribas ta ja kunnen masu yunkurin hana ta tsige Gwamna

A jawabin da ya yi a farko, Kwamishinan yada labaran gwamnatin Kano, Ibrahim Abdullahi Waiya ya bayyana cewa babu laifi don Gwamna ya sauya sheka.

Yace Gwamna Abba Kabir Yusuf na buga lissafi a siyasar Kano domin a samu karuwar kwanciyar hankali mai dorewa da yalwa a jihar.

Ya kuma ji takaicin masu zargin Abba Gida-Gida da yi wa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso butulci, inda y ace duk wani batun sauya sheka zai amfani jama’a.

Abba ya soki Ganduje ana batun canja sheka

A baya, mun wallafa cewa duk da ana batun Gwamna Abba Kabir Yusuf zai hade da Dr. Abdullahi Umar Ganduje a APC, ya suka a kan yadda gwamantin da ya gada ta yi aikinta a Kano.

Gwamnan Kano ya bayyana haka ne a lokacin da ya raba kayayyakin tallafi ga matasa 2,260 da suka kammala shirin koyon sana’o’i guda takwas da aka yaye a sassan Kano.

Abba Kabir Yusuf ya ce an assasa cibiyoyin ne a zamanin Rabiu Musa Kwankwaso amma aka rufe su a gwamnatin Abdullahi Ganduje a lokacin da ya samu ragamar jagorancin jihar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng