Jagora a APC Ya Yi Hasashen Atiku zai Yi Amfani da Kuɗi don Ruguza ADC

Jagora a APC Ya Yi Hasashen Atiku zai Yi Amfani da Kuɗi don Ruguza ADC

  • Jigo a APC, Osita Okechukwu ya yi gargadi cewa ADC na iya karya tsarin karɓa-karɓa na shugabancin ƙasa saboda tasirin Atiku Abubakar
  • Ya yi zargin cewa tsohon Mataimakin shugaban kasa, Atiku ya taka rawa wajen rikitar da jam’iyyun adawa, daga ciki har da PDP
  • Ya ce karya tsarin karɓa-karɓa na 2023 ta taimaka wajen raunana dimokuraɗiyyar Najeriya kuma da alama za a maimaita hakan a ADC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Wani daga cikin wadanda suka suka kafa jam’iyyar APC, Mista Osita Okechukwu, ya yi gargadi cewa ADC na fuskantar barazanar karya tsarin karɓa-karɓa na shugabancin ƙasa.

Ya ce wannan al'amari zai biyo bayan ƙara karfin tasirin tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar a cikin tafiyar an hadakar adawa.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna, Sanata Dickson ya koma jam'iyyar hadaka, ADC? Gaskiya ta fito

Ana zargin Atiku zai karya tsarin karba-karba a ADC
Jagora a hadakar ƴan adawa ta ADC, Atiku Abubakar Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

The Guardian ta wallafa cewa Okechukwu ya zargi Atiku da bin wani tsari na siyasa da a cewarsa ya jawo rikice-rikice da durƙushewar jam’iyyun adawa a baya.

Jigon APC ya dura a kan Atiku

Daily Post ta wallafa cewa Osita Okechukwu ya bayyana cewa tsohon Mataimakin shugaban kasar ya saba karya yarjejeniyar karɓa-karɓa tsakanin Arewa da Kudu.

Ya yi wannan bayani ne a matsayin martani ga kalaman Atiku a ranar Asabar 10 ga watan Janairun 2026 inda ya ce dimokuraɗiyyar Najeriya na fuskantar barazana saboda yadda gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke raunana jam’iyyun adawa.

A cewar Okechukwu, ya kamata Atiku ya binciki kansa domin yin adalci ga tarihin rawar da ya taka wajen kai dimokuraɗiyyar ƙasa halin da take ciki a yau, musamman bayan zaɓen 2023.

Okechukwu ya ce rashin bin tsarin karɓa-karɓa da kuma Sashe na 7 na kundin tsarin mulkin jam’iyyar PDP, wanda ake zargin Atiku ya karya, ya taimaka matuƙa wajen durƙusar da jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Harin Amurka: Shugaban ƙaramar hukuma a Binuwai ya nemi ɗauki kan karuwar ƴan ta'adda

Da Atiku aka karya PDP - Jagora a APC

bayyana Atiku a matsayin ɗaya daga cikin manyan mutanen da suka jawo abin da ya taimaka wajen rugurguza PDP.

A cewarsa:

“Idan Alhaji Atiku Abubakar ya zurfafa tunani, zai fahimci cewa karya tsarin karɓa-karɓa – wanda yarjejeniya ce ta masu ruwa da tsaki a Jamhuriya ta Hudu – ta taka muhimmiyar rawa wajen wannan mummunan yanayi.”
Okechukwu na zargin Atiku zai yi amfani da kudi don neman takara a ADC
Alamar jam'iyyar ADC (daga hagu), Atiku Abubakar (daga dama) Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Ya kuma nuna damuwa cewa Atiku na iya maimaita irin wannan kuskure a jam’iyyar ADC, musamman ganin cewa babu wani ɗan takarar shugaban ƙasa a ADC da ke da irin ƙarfin kuɗi da tasirin da Atiku ke da shi.

Okechukwu ya tuna cewa an tsara tsarin karɓa-karɓa tun 1999 ne domin tabbatar da haɗin kai, adalci, wakilci da kwanciyar hankali ta hanyar bai wa Arewa da Kudu damar musayar shugabancin ƙasa.

Ya ce idan ba don wannan tsari ba, Atiku da kansa da wuya ya zama Mataimakin Shugaban Ƙasa a 1999.

Atiku ya ƙaryata janye wa daga takara

Kara karanta wannan

ADC na shirin hadaka da PDP da NNPP domin kifar da Tinubu a 2027

A baya, mun kawo labarin cewa tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya fayyace matsayinsa kan zaɓen 2027, inda ya jaddada cewa ba shi da niyyar janye wa daga takara.

Atiku Abubakar ya bugi ƙirji kan aniyarsa ta tsayawa takara ne a cikin wata sanarwa da aka fitar da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Paul Ibe, ya sanya wa hannu.

A cikin sanarwar, tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar ya yi zargin cewa fadar shugaban ƙasa da jam’iyyar APC na tsoma baki a harkokin jam’iyyun adawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng