‘Dalilin da Ya Sa APC Ke da Kwarin Guiwar Samun Nasara a Zaben 2027’

‘Dalilin da Ya Sa APC Ke da Kwarin Guiwar Samun Nasara a Zaben 2027’

  • Jam’iyyar APC ta bayyana kwarin gwiwar lashe zaɓen shekarar 2027 bisa tsari mai ƙarfi, nasarorin gwamnati da ƙaruwa mambobinta a Najeriya
  • Shugaban APC, Nentawe Yilwatda, ya ce rikice-rikicen jam’iyyun adawa ba laifin jam'iyyar ba ne ko kadan
  • APC ta ce tana ci gaba da samun karɓuwa daga ’yan Najeriya, inda ake samun sababbin mambobi kullum

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Jam’iyyar APC ta yi magana game da kwarin guiwarta wurin samun nasara a zaben shekarar 2027 da ke tafe a a Najeriya a ranar Asabar 10 ga watan Janairun 2026.

APC ta bayyana cewa hakan na da alaka da tsari mai ƙarfi, nasarorin da ta samu a mulki da kuma ƙaruwa mambobinta a faɗin ƙasar nan.

APC ta bugi kirji kan zaben 2027
Shugaban APC, Nentawe Yilwatda. Hoto: All Progressives Congress.
Source: Twitter

APC ta sha alwashi game da zaben 2027

Kara karanta wannan

ADC na shirin hadaka da PDP da NNPP domin kifar da Tinubu a 2027

Da yake magana kan damar jam’iyyar, shugabanta, Nentawe Yilwatda, ya ce haɗin kan cikin gida da ayyukan da APC ta aiwatar sun sa jam’iyyar ta zama abar jan hankalin ’yan Najeriya, cewar Tribune.

Nentawe ya ce babu hannun APC ko kadan a sabanin rikice-rikicen da ke addabar jam’iyyun adawa.

A cewarsa, bai dace a dora laifin matsalolin jam’iyyun adawa kan APC ba, yana mai jaddada cewa ƙarfin APC yana cikin tsarinta da tarihin shugabancinta.

Yilwatda ya ce:

“Yaya za a ce ba a kula da dimokuraɗiyya ba, alhali mutane na ganin jam’iyyar da ke aiki yadda ya kamata, tana gudanar da mulki yadda ya dace kuma tana da tsari mai kyau? Sauran jam’iyyun ba su da tsari. Ba laifinmu ba ne. Ya kamata a yaba mana saboda tsari da kuma yadda jam’iyyar ta zama abin sha’awa ga masu shigowa cikinta.”

Ya ƙara da cewa APC na da cikakken tabbacin samun nasara a zaɓen 2027 da za a yi, kamar yadda ta kasance da wannan tabbacin a zaɓukan da suka gabata.

Shugaban APC ya sha alwashin nasara a zaben 2027
Shugaban APC a Najeriya, Nentawe Yilatda. Hoto: Prof. Nentawe Yilatda.
Source: Twitter

Jan hankali da APC ke yi wa yan kasa

Shugaban jam’iyyar ya ce ci gaba da samun goyon baya daga sassa daban-daban na ƙasa na tabbatar wa shugabannin APC cewa ’yan Najeriya suna tare da jam’iyyar da hangen nesanta na shugabanci.

Kara karanta wannan

NNPP ta yi watsi da hukuncin kotu game da shugabancin jam'iyyar a Kano

Ya bayyana cewa APC ita ce jam’iyyar siyasa mafi girma a Afirka, kuma tana ci gaba da jan hankalin ’yan siyasa da al’umma, inda ake ci gaba da yin rajistar sababbin mambobi kullum.

A cewarsa:

“A matsayinta na jam’iyya mafi girma a Afirka, mutane na marmarin shiga APC. Kowace rana muna rajistar mambobi da yawa. Mu ne jam’iyyar da ta fi tsari, karɓuwa da nagartar shugabanci a Najeriya."

APC ta yi wa Gwamna Caleb alkawari

Kun ji cewa Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya ce jam’iyyar za ta daina sukar Gwamna Caleb Mutfwang.

Farfesa Yilwatda ya yi ikirarin cewa APC za ta bai wa Shugaba Bola Tinubu sama da kuri’u miliyan daya a Plateau.

Ya ce APC ta kara karfi a Plateau bayan shigowar manyan ‘yan siyasa, tare da alkawarin cewa babu wanda zai kwace jam’iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.