Gwamna Fubara Ya Fada Hannun da bai Dace ba Lokacin da Ya Koma Jam'iyyar APC
- Tsohon dan takarar gwamnan jihar Ribas, Tonye Cole ya ce Gwamna Siminalayi Fubara ya fada bangaren da bai dace ba a APC
- Cole ya bayyana cewa tsagin APC da ya karbi Gwamna Fubara ba shi ne halastacce ba, saboda kotu ta riga ta yanke hukunci
- Wannan kalamai na Tonye Cole na zuwa ne yayin da rikicin siyasar Rivers ke kara kamari tsakanin Fubara da yan Majalisar dokoki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Rivers, Nigeria - Tsohon ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a Jihar Rivers, Tonye Cole, ya ce Gwamna Siminalayi Fubara ya yi kuskure wajen sauya sheka zuwa jam'iyya mai mulki.
Mista Cole ya yi ikirarin cewa Gwamna Fubara ya shiga tsagin APC da ba halastacce ba ba bisa tanadin doka.

Source: UGC
Tsohon 'dan takarar gwamnan ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi a wata hira da gidan talabijin na Channels tv.
Cole ya bayyana cewa ɓangaren APC na Jihar Rivers da Emeka Beke ke jagoranta shi ne sahihi kuma halastacce a idanun doka.
Yadda Gwamna Fubara ya koma APC
A watan Disambar 2025 ne Gwamna Fubara ya fice daga jam’iyyar PDP ya koma APC mai mulki, cewar rahoton The Cable.
Haka kuma uwar jam'iyya ta kasa ta karbi gwamnan zuwa APC a hukumance lokacin da ya kai ziyara hedkwatarta da ke birnin tarayya Abuja.
Shugaban tsagin APC na jihar Rivers, Tony Okocha ne ya jagoranci yi wa Gwamna Fubara rijista tare da ba shi katin zama ɗan APC.
Da yake tsokaci kan sauya shekar, Tonye Cole ya ce Fubara ya bi hanya mara kyau ta shiga ɓangaren Okocha,
Wane bangaren APC Fubara ya shiga?
Tsohon ɗan takarar gwamnan ya ce ba za a iya amincewa da Fubara a matsayin cikakken ɗan APC ba a bisa doka, sai dai idan ya shiga ɓangaren da Emeka Beke ke jagoranta.
Ya ƙara da cewa sauya shekar Fubara dabara ce ta siyasa mai kaifin basira, kuma yawancin ’yan APC, ciki har da shi kansa, sun karɓe ta hannu bibbiyu.
“Ina nan a matsayin jagoran APC a Jihar Rivers. Dalilin kuwa a bayyane yake. Akwai shari’a da tsagin APC da na yi takara a karkashinsa ya shigar a gaban kotu.
“Wannan ita ce shari’ar ɓangaren Emeka Beke. Mun yi nasara a kotu, kuma an amince da wannan ɓangare a matsayin sahihin shugabancin APC, wannan shi ne doka.
“Wa ya karbe shi (Fubara) a APC? Wane ne ya ba shi katin zama ɗan jam’iyya? A wane wuri aka yi masa rijista? Tony Okocha ba shugaba ba ne da doka ta amince da shi, kuma a nan ne matsalar take."
- Tonye Cole.

Source: Facebook
Fayose ya fadi abin da zai ceci Fubara
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya tsoma baki kan dambarwar da ke faruwa tsakanin 'yan majalisar dokokin Rivers da Gwamna Fubara.
Fayose, wanda ake ganin yana da kyakkyawar alaka da Ministan Harkokin Abuja, Nyesom Wike, ya ce azumi da yawaita rokon Allah ne kadai za su iya ceton gwamnan.
Ya dora laifin rikicin kan gwamnan Ribas, yana mai cewa Fubara bai kiyaye yarjejeniyoyin da aka cimma a Abuja ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

