Shugaban Kwamitin Yakin Zaben Uba Sani Ya Rabu da Gwamna Ya bi El Rufai zuwa ADC
- Jam'iyyar APC a jihar Kaduna da Gwamna Uba Sani sun yi rashin jigo wanda ya yi watsi da su zuwa bangaren adawa
- Tsohon Kwamishina a jihar, Muhammad Sani Bello (Mainan Zazzau), ya fice daga APC zuwa ADC, inda ya bayyana dalilansa
- Ya ce ya janye alakarsa na APC nan take, yana gode wa jam’iyyar bisa hadin kai da suka yi a lokacin da yake cikinta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Darakta-Janar na kwamitin yakin neman zaben Sanata Uba Sani a 2023, Muhammad Sani Bello, ya bar APC ya koma jam’iyyar ADC.
Sani Bello, wanda aka fi sani da Mainan Zazzau, ya taba rike mukamin Kwamishina na Ilmi da na Yada Labarai na Jihar Kaduna kafin ya bar gwamnati.

Source: Facebook
Tsohon Kwamishinan Kaduna ya bar APC zuwa ADC
Ya sanar da ficewarsa daga APC ne ta wata wasika mai dauke da kwanan wata 7 ga Janairu, 2026, wacce ya aikawa shugaban APC na mazabar Dogarawa, cewar Punch.
A cikin wasikar, Mainan Zazzau ya ce ya yanke shawarar janye membobinsa na APC nan take ba tare da wani jinkiri ba.
Ya kuma gode wa jam’iyyar APC bisa dangantakar siyasa da suka yi a lokacin da yake cikinta, yana mai bayyana jin dadinsa da hadin kan da aka samu.
Ya ce:
“Ina sanar da ku ne kan matsayina na janye kasancewata mamba a jam’iyyar APC nan take ba tare da ɓata lokaci ba.
“Ina so na bayyana godiyata kan kyakkyawar hulɗar da muka yi wadda ta amfani ɓangarorin biyu a lokacin da nake mamba a jam’iyyar.”
Alakar Sani Bello da Nasir El-Rufai
Bello na daga cikin amintattun tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, kuma ya taka rawa wajen yakin neman zaben Uba Sani a zaben 2023.
Bayan ya gama adawa da gwamnatin El-Rufai, Mainan Zazzau ya shigo APC kuma aka dama shi, a karshe ya zama Kwamishinan ilmi a 2023.
Rahotanni sun nuna cewa Bello ya bar mukamin Kwamishinan Yada Labarai ne kwanan nan kafin ya sauya sheka zuwa jam’iyyar ADC.
Bayan shigarsa ADC, jam’iyyar adawa ta nada shi mamba a kwamitin bitar kundin tsarin mulki domin shirin zaben 2027.

Source: Facebook
Jam'iyyun da tsohon kwamishinan ya shiga a baya
Tsohon Kwamishinan ya taba shiga APC a shekarar 2018 bayan ya bar jam’iyyar PDP da ya fara siyasa a cikinta.
A lokacin, Bello ya bayyana cewa ya tuntubi jam’iyyu da dama kafin ya yanke shawarar shiga APC a hukumance wanda ya rike mukamai da yawa a cikinta.
Ya ce rashin amincewa tsakaninsa da shugabancin PDP da dan takarar gwamna Isa Ashiru ne ya tilasta masa ficewa daga jam’iyyar, cewar Daily Post.
Sanata Kingibe ta bar LP zuwa ADC
Kun ji cewa jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya za ta samu sanata mai-ci wadda za ta yi rajista domin zama daya daga cikin mambobinta.
Sanata mai wakiltar babban birnin tarayya Abuja a majalisar dattawa, Ireti Kingibe, ta sanya lokacin da za ta yi rajista da jam'iyyar ADC a hukumance.
Ireti Kingibe za ta yi hakan ne bayan ta sauya sheka daga jam'iyyar LP wadda ta lashe kujerar Sanata a zaben shekarar 2023 da ya gabata.
Asali: Legit.ng

