Matsala Ta Tunkaro, An Yi Hasashen Gwamnonin APC 8 Za Su Juya Wa Tinubu Baya a 2027
- Fitaccen limamin coci a Najeriya, Primate Elijah Ayodele, ya yi hasashen wahalar da Shugaba Bola Tinubu zai fuskanta a zaben 2027
- Ayodele ya yi ikirarin cewa ya hango wasu gwamnoni takwas a APC da ba za su marawa kudirin tazarcen Shugaba Tinubu baya ba
- Ya kuma bayyana cewa akwai wani babban kusa a siyasar Najeriya da zai sauya sheka zuwa jam'iyyar hadaka, ADC nan ba da jimawa ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Jagoran cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Primate Elijah Ayodele, ya yi hasashen cewa wasu gwamnonin APC takwas za su canza alkibla a zaben 2027.
Fitaccen limamin cocin, wanda ya yi kaurin suna wajen hasashen abin da zai faru a gaba, ya ce ya hango yadda Shugaba Bola Ahmed Tinubu da APC za su sha wahala a zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan
Boye boye ya kare, majalisar Kano ta yi magana kan shirin Gwamna Abba na komawa APC

Source: Twitter
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da mataimakin mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Osho Oluwatosin, ya rattaba hannu, kamar yadda Tribune Nigeria ta rahoto.
Ayodele ya hango shirin gwamnonin APC 8
Malamin ya bayyana cewa kimanin gwamnonin APC takwas za su yi aiki a ɓoye domin yin wa Shugaba Tinubu da jam’iyyar APC zagon ƙasa gabanin zaɓen shekarar 2027.
Primate Ayodele ya ce gwamnonin na iya ci gaba da zama a APC ko kuma sauya sheƙa zuwa jam’iyyun adawa, amma duk da haka za su yi aiki ne domin hana Tinubu da jam’iyyarsa samun nasara.
“Ina ganin gwamnonin APC kusan takwas za su yi aiki domin yakar jam’iyyar kafin 2027. Ko dai su zauna a APC suna yakarta, ko kuma su koma jam’iyyar adawa,” in ji shi.
Ana ganin Tinubu zai sha wahala a 2027
Ya kuma yi hasashen cewa Shugaba Tinubu ba zai ci nasara cikin sauki a zaɓe mai zuwa ba, yana mai cewa akwai abubuwa da dama a kusa da shi da suke kama da gaskiya amma duk rufa-rufa ce.

Kara karanta wannan
"Ni zan masu dariya a karshe," Kwankwaso ya kara tabo batun sauya shekar Gwamna Abba
“Zaɓen ba zai yi wa Shugaba Tinubu sauƙi ba. Akwai abubuwa da yawa da suke bayyana a matsayin gaskiya amma ba haka suke ba.
"Ba da jimawa ba za a fara gano su, don haka dole ne ya shirya sosai,” in ji Primate Ayodele.

Source: Twitter
ADC za ta yi babban kamu a Najeriya
Har ila yau, Malamin addinin ya ce wani babban jigo a siyasar Najeriya zai sauya sheƙa zuwa jam’iyyar ADC nan ba da jimawa ba, lamarin da zai girgiza fagen siyasar ƙasar.
“Ina ganin wani babba a siyasar Najeriya zai koma ADC nan kusa. Abin zai ba mutane mamaki kuma zai girgiza siyasar ƙasar. Zai faru nan ba da jimawa ba,” in ji shi.
Yawan gwamnonin APC zai amfani Tinubu?
A wani rahoton, kun ji cewa jam’iyyar APC ta ce yawan gwamnonin da take da shi a cikinta zai kara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu karfin tunkarar zaben 2027.
Shugaban jam’iyyar APC a Jihar Kwara, Sunday Fagbemi, ne ya bayyana hakan, ya ce gwamnonin da kw sauya sheka za su karawa Tinubu damar nasara a zabe na gaba.
A cewarsa, halin da jam’iyyar ke ciki a yanzu ya nuna karara cewa APC na kara fadada karfinta a fadin kasar nan.
Asali: Legit.ng