Jam'iyyar APC Ta Dauki Zafi, Ta Yi Magana kan Shirin Tsige Gwamma Fubara daga Mulki

Jam'iyyar APC Ta Dauki Zafi, Ta Yi Magana kan Shirin Tsige Gwamma Fubara daga Mulki

  • Jam'iyyar APC ta yi watsi da yunkurin 'yan Majalisar dokokin jihar Ribas na tsige Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa daga mulki
  • APC ta reshen jihar Ribas ta ce ba za ta zuba ido tana kallo a ruguza gwamnatin Fubara saboda son rai na wasu mutane ba
  • Ta yi kira ga mambobin APC na Majalisar dokokin su kauracewa duk wata matsin lamba, kar su bari a sauke Gwamna Fubara daga mulki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Rivers, Nigeria- Jam’iyyar APC reshen Ribas ta yi fatali da yunkurin da ake yi a Majalisar Dokokin Jihar na tsige Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa.

APC ta bayyana lamarin a matsayin abin da ba zai yiwu ba tare da gargaɗin cewa hakan na iya kara rura wutar rikici da tayar da hankalin gwamnati a jihar Ribas.

Kara karanta wannan

Majalisar Rivers ta lissafo zunuban Fubara 11 yayin take shirin tsige shi

Gwamna Fubara.
Gwamnan jihar Ribas, Sir Siminalayi Fubara yama jawabi a fadar gwamnatinsa Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Source: Facebook

Tun da fari, rahotanni sun bayyana cewa Majalisar Dokokin Ribas ta fara shirin tsige gwamnan, kamar yadda jaridar The Cable ta kawo.

An ruwaito cewa Kakakin Majalisar, Rt. Hon. Martins Amaewhule, ya bayyana Fubara a matsayin “kuskure” tare da zarginsa da aikata manyan laifuffuka na rashin da’a a aiki.

APC ta yi fatali da shirin tsige Fubara

A wata sanarwa da kakakin APC ta Ribas, Darlington Nwauju, ya sanyawa hannu, jam’iyyar ta ce ta samu labarin abin da ta kira ci gaba mara daɗi daga Majalisar Dokoki.

“Mun yarda cewa Majalisa ɓangare ne mai cin gashin kansa a tsarin mulki, kuma aikin sa ido da daidaitawa yana daga cikin haƙƙin ta na dimokuraɗiyya.
“Amma matsayar jam’iyyarmu a yau ita ce, ba mu yarda da duk wani yunkuri na tsige gwamnanmu da mataimakiyarsa ba," in ji sanarwar.

Jam’iyyar ta ce ba za ta yi shiru ba yayin da rikice-rikicen da suka samo asali daga PDP ke neman sake barkewa a cikin APC ba, tana mai cewa hakan ba abin amincewa ba ne, in ji Vangaurd.

Kara karanta wannan

Majalisa ta fara shirin tsige gwamna Fubara bayan sabon rikici da Wike

Sakon APC ga 'yan Majalisar dokokin Ribas

APC ta yi kira ga ’yan Majalisar Dokokin Ribas, musamman mambobin APC, da su ƙi amincewa da duk wani matsin lamba daga waje da ke neman dagula gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Siminalayi Fubara.

“Jam’iyyarmu za ta yi duk mai yiwuwa don tabbatar da cewa ba a rusa gwamnatin APC a Ribaa ba sakamakon rikicin cikin gida,” in ji sanarwar.

Jam’iyyar ta kuma buƙaci Majalisar ta dakatar da shirin tsige gwamnan nan take, domin kada hakan ya jawo wa APC tozarta da kuma hana ci gaban da jihar ke samu.

Jam'iyyar APC.
Tutar jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya Hoto: @OfficialAPCNig
Source: Twitter

Wike ya kira Fubara da mara tarbiyya

A wani rahoton, kun ji cewa Ministan Harkokin Abuja, Nyesom Wike, ya soki Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara bisa rashin ci gaba da wasu ayyuka da ya bari.

Wike ya bayyana Gwamna Fubara a matsayin mara tarbiya yayin da yake nuna damuwarsa kan yadda ya soke daukar wasu ma'aikata.

Wannan na zuwa ne a lokacin da rikicin siyasar jihar ke kara kamari bayan janye dokar ta bacin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya sanya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262