Majalisar Rivers Ta Lissafo Zunuban Fubara 11 yayin Take Shirin Tsige Shi
- Majalisar Dokokin Jihar Rivers ta fara shirin tsige Gwamna Siminalayi Fubara, inda Kakakin Majalisa ya kira shi matsala ga jihar Rivers.
- ‘Yan majalisa 26 sun zargi Fubara da manyan laifuka, ciki har da ƙin gabatar da kasafin kuɗin 2026 da sauran laifuffuka da ya aikata
- Kakakin Majalisar ya ce ko da gwamnan ya gabatar da kasafi yanzu, hakan ba zai dakatar da shirin tsige shi ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Port Harcourt, Rivers - Majalisar Dokokin Jihar Rivers ta fara shirin tsige Gwamna Siminalayi Fubara a hukumance.
Kakakin Majalisar, Martins Amaewhule, ya bayyana gwamnan a matsayin 'kuskure' ga jihar da al'ummarta baki daya.

Source: Twitter
Zarge-zargen da ake yi wa Fubara
Rahoton Vanguard ta ce hakan ya biyo bayan matakin da Majalisar ta ɗauka na sauya shawarar da ta yanke a baya ta komawa zama a ranar 26 ga Janairun 2026.
A zaman majalisar da Amaewhule ya jagoranta, Shugaban masu rinjaye a majalisa, Major Jack, ya karanta takardar zargin manyan laifuffuka da aka jingina wa gwamnan.
Takardar, wadda ‘yan majalisa 26 suka sanya wa hannu, ta zargi Fubara da aikata abubuwan da suka saɓa wa kundin tsarin mulkin Najeriya.
Daga cikin zarge-zargen, ‘yan majalisar sun ce gwamnan ya mayar da kuɗin jihar zuwa dala, tare da zargin cewa ya biya wasu mutane daga Abuja domin su yi tasiri ga Bola Tinubu don ya hana Majalisar kiran sa domin gabatar da kasafin kuɗin 2026.

Source: Facebook
Gargadin majalisar ga Gwamna Fubara a Rivers
Amaewhule ya kuma gargaɗi cewa duk wani yunƙuri na gabatar da dokar kasafi ko Tsarin Kashe Kuɗi na Matsakaicin Zango (MTEF) yayin da ake binciken zarge-zargen, ba zai hana shirin tsige gwamnan ci gaba ba.
A cewarsa, gwamnan ya daɗe yana ƙin gabatar da kasafi, yana mai cewa da a ce Fubara na da niyyar yin hakan, da ya riga ya gabatar tun da wuri.
Ya ce:
“Yawancin zarge-zargen manyan laifuffuka sun shafi ƙin gabatar da kasafi da kuma kashe kuɗi ba bisa dokar kasafi ba.”
Amaewhule ya ce idan gwamnan ya sake yunƙurin gabatar da kasafi ko MTEF domin ya kauce wa shirin, ‘yan majalisar sun buƙaci a dakatar da hakan har sai an kammala binciken da ake yi masa da mataimakiyarsa.
Ya ce Fubara da mataimakiyarsa, Farfesa Ngozi Odu, su ne kaɗai shugabannin jihohi a Najeriya da har yanzu ba su gabatar da kasafin kuɗin 2026 ba, cewar TheCable.
Ya ce:
“Wannan abin kunya ne ga dimokuraɗiyyarmu. Gwamna Fubara da mataimakiyarsa barazana ne ga dimokuraɗiyya, kuma idan aka bar su a kan mulki, ba a san abin da zai faru ba.”
A ƙarshe, Amaewhule ya ce tushen shirin tsige gwamnan shi ne ƙin gabatar da kasafi, duk da cewa an taɓa yin taruka da dama da Shugaba Tinubu da tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike, domin warware rikicin.
Wike ya kira Fubara mara tarbiyya
An ji cewa ministan Abuja, Nyesom Wike ya ci gaba da sukar Gwamna Siminalayi Fubara a rangadin da yake domin yi wa jama'a godiya a Rivers.
Wike ya bayyana Gwamna Siminalayi Fubara a matsayin dan da bai gaji halin ubangidansa ba.
Ya gode wa shugabannin al'umma da na siyasa a yankin karamar hukumar Asari-Torubisa jajircewa da goyon bayan da suka nuna masa.
Asali: Legit.ng

